← Book details Sirrin Keta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 47

Sashe 25

Sirrin Keta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tin da mhamah ta nuna wa ayaana 'bacin ranta an samu sauqin fitina amma bayan kwani biyu da zafin ta ta dawo,

Yalla'bai kuwa har ya fara sabawa da 'baran'batamar reeetaj,
Yauma ta gama har ta gaji be kula ta ba bacci yayi awon gaba da ita tana zaune kan kujera take ta faman zabga gyangyad'i gashi kujerar babu makarai kamar zata wuntsilo qasa hankalin ayaan ya gaza kwanciya kallon ta kawai yake dan kuwa gani yake da ya juya zata fad'o shi kanshi be san dalilin da yasa ya damu da ita sosai ba haka kawai yake jin baze iya jurar ganin wani abu ya same ta ba gani yayi ta kusa shan qasa be san lokacin da ya matsa kusa da ita ba rungumo ta yayi a hankali yayi mata masauki a kan kafad'ar sa ya kwantar da ita yadda zataji dad'in baccin ita kuwa bata san anayi ba sai ma qara jan numfashi da take shi kuwa danne dannen sa yake ba tareda damuwa ko tunanin gajiya ba har wani lokaci,
Ameeed ne ya shigo da sallama cakkk ya tsaya yana zarowa yalla'bai ido cike da mamaki yace yalla'bai meye hakan abunda ban ta'ba gani ba.

Tsakin da ayaaan ya zabga ne yasa yayi saurin kama bakin sa yace yalla'bai ana neman iso ne zeeeny ce wannan me nacin tsiyar nan kusan kullum sai tazo na hanata shigowa yanzu yalla'bai me zance mata??

Kace ta shigo.
To yalla'bai..

Zeeeny cikin farin ciki ta shigo tana taku qaras qaras sai wani fi'ili take a ranta kuwa tasa aniyar gogewa wannan bagidajiyar y'ar aikin tasa hadda sai ta nuna mata ita qaramar y'ar bariki ce sai wani juya idanu take tana fari dasu ta shigo tareda sallama cikin wata maqalalliyar murya,
Suman fad'uwa qasa ne kawai batayi ba ganin reetaj kwance sha'be sha'be kan kafad'ar ayaaan a tsaye ta daskare tana jin wata wujujuwa a cikin kanta da yake qwararriya ce ta ta fannin bariki dan da nan ta sauya salo tayi kamar bata damu ba ta danne zuciyar ta,,
Cikin harshen turanci tace barka da wannan lokaci ayaan kana lafiya?

Remote d'in kira ya danna ameeed ya shigo da sauri,
da hausa ayaan yace kayi magana da ita dan naga kamar bata jin hausa,
Maida hankalin sa yayi kan reeetaj yana gyara mata d'an kwalin ta da ya rufe mata fuska jin ta motsa yasa yayi saurin hura mata iska a hankali sauke ajiyar zuciya tayi gami da shaqar daddad'an numfashi ta sauke a hankali shi kuwa ya zuba mata ido kamar wani wanda ake ce yana kauda idon sa za a d'auke ta.

Qullutun Baqin ciki ne ya toshewa zeeny maqoshi ji take kamar ta kurma ihu da kyar ta iya daurewa tace kayi haquri da kai nake son nayi magana,,,

Duba agogon sa yayi sannan ya kalli ameeed da harshen hindi yayi magana,
Ameeed ya maimaita mata cewar yalla'bai namu yace babu lokacin ki a yanzu kya iya dawowa wani lokaci..
Ki fita yanzu yanzu yalla'bai baya buqatar ganin ki,

Babu abunda be ziyar ci zeeeny ba indai na 'bacin rai ne kamar ta tashi sama ta fita kai tsaye parking sface ta nufa ta d'auki motar ta ta wuce gidan da suke tantirancin su ta nufa ta samu alina tana shaye shayen ta saida ta kora itama sannan taji dama dama tace alina ?? Ni ze ciwa mutunci ayaaan be san wacece ni ba ko??

Alina tace eh da alama dai meye faru kuma yanzu??

Zeeny tace wannan munafukar sai da nace miki zanyi maganin ta kikace ba matsalar ta bace yanzu gashi nan ta mallake min zuciyar sa zuwa fa nayi na tarar da ita sai bacci take a kan qirjin sa alina meyesa ze min haka?? ya wulaqanta ni a gaban wannan me gadin nasa yaci zarafi na kawai dan yaga ina son shi?? Alina meyesa hakan take faruwa meyesa alina yaqi fahimta ta be saurare ni ba bare ma ya fahimce ni alina yanzu ya zanyi? meyesa ayaan ze gagare ni ???
Ki fad'a min alina meye zanyi yanzu ??
baya son gani na kwata kwata ni kuma sai na same shi ko ta tsiya ko ta arziqi,

Alina tace qwarai ma idan baki samu ayaan ba ai bamu cika ba wallahi zeeeny sai munyi maganin sa ke dai yanzu ki nutsu kawai naga ba a hayyacin ki kike ba idan muka nutsu zamu tattauna a kai yanzu dai ki tashi ki shirya dan kuwa *babban yaro* ze zo gurin ki ki masa tanadi me kyau gaskiya karki bamu kunya ki cire duk wannan damuwar dalla ki raqashe tareda shi har tsawon kwana yana tare dake yarinya ai ke baki da matsala ayaan d'in banza tinda ga wanda ze d'ebe miki kewa ki manta dashi kawai in kin gama kya fara tunanin sa yanzu dai ga wannan ki fara sha tukunna miqa mata kofin hannun ta tayi.
Ta kar'ba ta shanye qyatt,

Bayan tayi baccin me isar ta a hankali ta farka jinta a jikin mutum yasa ta firgita zaro ido tayi tana kallon sa shima kallon ta yake fuskar sa d'auke da murmushi yace kin tashi??

Janye jikin ta tayi tana murtsike ido tace ba gashi ka gani ba ?? Ko mene ya kawo ka kusa dani ma??'

Shafar sumar sa yayi yace kin fiye bacci da yawa kuma kina bacci a kan kujera sai kin je kin fad'o kodai a kawo miki gado???

Zaro idon ta da sukai wuri wuri tayi kafin ta langa'bar da kai tace nifa.. haba yalla'bai ni dai.. Ka dena ... Nidai .. Ka dena yi min magana...

Ya d'an yi dariya yace hmmm??,
To shikenan Zan dena maganar ko kin min magana ni kuma zanyi shiru,

a"a yalla'bai ba haka nake nufi ba nidai ka dena tsokana ta,

Tayi magana cikin sigar shagwa'ba,

Ohhh ka dena tsoka na ta shikenan tashi ki tafi gida maza,

Ai dama zan tafi in ba haka ba nan gaba ma goya ni zakai qila dama ai ku haka kuke goben ma ko aikin bazan zo ba,

Shikenan hakan ma yayi zan turo mhamah ta ta d'auko min ke"

saurin dawowa tayi tana cewa yalla'bai yi haquri insha allahu da wuri zanzo wallahi tsoron mhaman ka d'in nan nake dan Allah karka had'a ni da ita karma ka bari tasan ina aiki a kamfanin ku dan Allah wallahi duk dangin ku ma tsoron ku nake ji yalla'bai sai da safe bazan ma kuma yin baccin ba na dena,

Daga haka ta fice da saurin ta

Dariya yayi yace yarinya kenan
Ai kuwa zaki dena tsoron su dan nasan ni dama na dad'e da zama kakan ki, ta raina ni da yawa komai yazo bakin ta kawai kwa'ba min shi take wani lokacin kamar yarinya y'ar shekara biyar take komawa,
Tana son farin ciki tana son wasa tana son nishad'i, hmm amma a hakan aka samu wanda ze cuce ta,
bata damu da duniya ba yarinyar da babu ruwan ta,
amma dai koma waye kanshi ya zalumta kuma bi'izini'rabbana zata zama kamar yadda take
cikin farin ciki koda yaushe, zata zama fiye da yadda ba a so a ganta wata rana komai ze zama labari dama haka duniyar take.
.Ohh ya Allah.
Meyesa na shaqu da ita har haka??

Yana shiga babban falon su yaji ihun qannen sa dukkan gidan duk yawan su sun taru a wajen suna ta surutu da dariya sithara tana ganin sa tace yauwa gashi nan ya dawo.

Shukreey tace bhaiya yau mhamah tasa atamfa zo ka gani kayi sauri !!!

Armaan ne ya tashi ya riqo hannun sa yana cewa bhaiya zo ka gani dan Allah mhamah ba tafi kyau a cikin kayan hausawa ba??

Murmushi yayi yana kallon mhamah islam yace bhaiya dan Allah ka duba fa ka gani amma mhamah tace irin kayan hausawa baza suyi mata kyau ba,

Aslam yace bhaiya ai yau dole mu raqashe mhamah tasa atamfa yau dole muyi rawa irin ta Ado gwanja ahahahayye....

Ayaan ya d'an harare shi yace kaifa mugun garafuni ne wani lokacin,,

Suka kaure da Ihuuu roooh yace Antashi!!!!!!!!!!
Wallahi bhaiya ya gama wasan gaskiya yau ana cizo a gidan nan......,

Islam yace wooo!!! Gaskiya ne shikenan bhaiya ya kwarfe ka in ba ya gama da kai baa inqi.... Gaskiya in nine kai na dena fita,,

Khairee yace kai la"ilaha'illallahu wallahi mhamah daga kanki an gama wanda,,

Aslam yace kai dalla mazgo mana sauti ke ayaaat bamu wuta kinji""

Ayaaat kuwa ta saki kid'a nan fa suka fara cashewa kowa nishad'i yake wai mhamah tasa atamfa,

Roooh ya canja salon kid'an yasa waqar Naziru m Ahmad me taken Ataka..
Wadda akaiwa launi da Happy birthday laila...

Suka fara bin waqar masu rawa nayi masu juyi nayi ..

Anna ce ta kama hannun ayaan tace tashi mana yaro na kai ma fah sai kayi rawa yau,

Annaa?,
Nifa in zanyi rawa ba irin waqar nan nake so ba kuma sai dai nayi tareda d'an uwa na,

Annaa tace abu me sauqi Kamar shan ruwa kai bhai Armaan kaima yau cashewa zakayi ga kai ga d'an uwan ka,

Armaan yace ni zanyi rawa a gaban yaran nan annaa ??

Annaa tace aaaa?? Tab!!!! Ai kuwa tinda bhaiyan ka yace kayi zakayi,

Kallon roooh tayi tace kai bawa bhaiya remote ya kunna waqar da yake so sannan kowa ya shirya rawa duk wanda baze iya ba yaja baya,

Roooh ya bawa ayaaan remote ya kar'ba yana za'bowa hannun sa kuwa ya sauka kan wata waqar india me take Hippop'' Hippop'"'

Waqar akwai disko da yawa duk daurewar mutum idan yajita ko beyi rawa ba sai jikin sa yayi ko ta kafad'a ko ta qafa ko kuma kawai kaji jikin ka na kakkarwa(...hihihi...)

Nan fa naga inda ake murza rawa a wajen ayaaan da Armaan cikin salo da qwarewa suke yinta kamar ba sune ba kowa sai da ya basu fagen dan babu wanda ze iya sai sud'in cikinsu kowa sai da yayi bajin tar iya tasa qwarewar dan bazaka ce ga wanda yafi iyawa ba,
Chapter 25 · 0% Book details