← Book details Sirrin Keta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 47

Sashe 30

Sirrin Keta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mami tace a"a dakata kaji nima gaskiya abun yana damu na ya kamata ace nayi jikoki ku biyu ne fah kawai dani kaga kuwa in akwai jikoki ai zuriya ta qara ha'baka kuma ko tayi auren ta haihu shikenan kai bazan ga naka d'an ba?? Ai jikan wajen d'aa namiji daban na mace daban
Wai meye ma dalilin rashin haihuwar tata muhsin ko bakwa zaman lafiya ne??

Muhsin yace a"a mami lafiya lau muke zaune ku kwantar da hankalin ku mami insha allah kwanan nan ma kuwa zaki ga jikokin ki,

Mami tace ato ni duniyar nan abun mamaki babu wuya ni tsoro na d'aya kar muje yarinyar nan juya ce kaga batun ganin jikoki babu shi,

Ahh mami insha allah babu abunda ze faru zaki ga jikokin ki ,

Tayi murmushi tace shikenan Allah i yarda Allah ya muku albarka dukan ku,

Suka amsa da amin,

awaaz kuwa tana can tana mulki a gida bata damu da haihuwa ko rashin ta ba hasalima ta manta da ita saboda ba ita ce a gaban ta ba shi kuwa muhsin be ta'ba nuna mata yana son haihuwa ba ko kuma ya damu akan bata haihu ba ,

Kullum shaquwa da sabo da aminta qara shiga rayuwar su take koda yaushe yanzu reetaj ta gama fahimtar waye ayaaan duk wani abunda baya so da wanda yake so duk ta sani kuma babu wannan miskilancin a tsakanin su shiyasa rayuwa take musu dad'i idan suka fara fira harda ameed ake zama dan shima ba dama ne sai yanzu ayaan ya gane sam be mori zama da ameed ba a da dan kuwa ameed idan baka da comedy a waya shi kad'ai ma ya ishe ka idan kuwa aka had'a da reetaj maqura ne ,

Zeeeny ganin duk wani abunda zatayi bata nasara akan ayaan gashi kuma koda yaushe qara son shi take batajin zata iya haqura dashi alina ta bata shawarar su fara zuwa wajen boka ai kuwa haka sukai boka kuwa yace ba buqatar sai an zuba masa wani abu a abinci ko anyi wani abun kawai zasuyi masa kiranye kuma zasuyi ta jifansa da asirai da sihiri da kansa ze kai kansa wajen zeeeny sun ji dad'in labarin sosai suka biyashi kud'i suka tashi kamar yadda yace haka ya fara aiki tuquru akan ayaan,,,

Shigowar sa kenan ya tarar suna fira sai zolayar mhamah suke suna cewa lokacin bikin bhaiyan su sai tafi sarauniyar india kyau ita kuwa tace sai dai sarauniyar garin su suna ta dariya qarasawa yayi aka farayi dashi Abie yace bhaiya wai wacece antyn nan tamu ne ??

Murmushi kawai ayaan yayi dan kuwa a duniya bayajin akwai macen da zata iya fuskantar sa har ya iya zama da ita dan shi kanshi yasan wani irin mutum ne wanda ba kowa ne yake iya fahimtar sa ba,,,

Ayaat ma tace bhaiya kayi shiru?? Muna ji,

Mhamah tace ai kuwa ko wacece sirika ta dole ta kasance ta musamman ko kuwa ???
Annaa tace qwarai ma kuwa ko ya kace bhaiya??

Dariya ayaan yayi yana sunkuyar da kai dan kuwa shi kunya ma yake ji tashi yayi zebar wajen mhamah tace bhetaa?? nayi magana da papu yace kaje india,

Tana fad'a reetaj kawai ya fara tunawa tayaya zata iya jurewa rashin sa har na wani lokaci???
Da kyar yace mhamah akwai wata matsala ne??

Tashi tayi ta taka sau uku sannan tace kenan?? Idan babu matsala ba zakaje ba???

Sunkuyar da kai yayi yace yaushe zan tafi??

Murmushi tayi tace ka shirya cikin kwana ki biyu nima zan zo bayan lokacin insha allah ,

Gyad'a kai yayi jiki babu qwari ya wuce sashin su kamar ya fara kuka,,,

Shagwa'ba'b'be kawai🙄🙄🙄🤭🤭

Comment and share dan allah🙏🙏

Karku manta da sharhi🥰🥰🥰
https://facebook.com/groups/575599953675542/

*💫💫ANNURI WRITER'S ASS.*💫💫
(Annuri is the best)

*(A.W.A)*

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FEViiYLkmiwKIUEZc2PcLD

*SIRRIN QETA*

*Page* *43~44*

*by yar gatan annuri writers*

🎉🎉 *Indo ce..*🎉🎉

*بسم الله الر حمن الحيم*

Bhabhai na zaune a falon sa yana duba wasu takardu ayaan ya shigo ko sallama babu kusa da bhabhai ya zauna yayi shiru..
Ganin haka yasa bhabhai yace.. yaro me ya faru ne?
Mhamah ce ko??

A shagwa'be yace bhabhai mhamah bata damu da uzurin wani ba bana son zuwa ko ina a yanzu amma tace in tafi india kuma bata fad'a min me zanyi ba,,

Murmushi bhabhai yayi yace mhamah sai haquri amma tana da dalilin hakan ba hakanan bane, bata fad'a maka ba kawai amma nasan zata fad'a,,

Kuka ya farayi yana cewa bhabhai nifa ban damu da fad'ar ta ba kawai bana son tafiyar ne kace ta barni kawai taje ita kad'ai,

Hannun sa bhabhai ya kama yana murmushi yace yaro kana da saurin kuka kai fa namiji ne kuma babba ka tuna fa qannen ka suna da yawa kuma sannan duk suna qarqashin kulawar ka ne idan kana yin kuka da sauri haka taya ya zaka iya jure musu har ka tare musu fad'a ??
Ina so ka kasance me dakakkiyar zuciya kuma jajirtacce bana so kake yawan zubda qwalla domin suna da muhimmanci a lokacin da akafi buqatar su lokacin da ba"a ra'ayin su kuwa ba"a so ayi 'barnar su ka gane ko???
Yanzu ka share hawayen ka kaji?? Ai bazaka dad'e ba zaka dawo,
Yaro. bansan meye wani abu me tasiri da ya shigo rayuwar ka ba a yanzu domin kuwa kai da india ko ba'a ce kaje ba kana zuwa a duk lokacin da kaga dama meyesa yanzu baka son zuwa yaro???

Lafewa yayi a jikin bhabhai ya kwantar da kai tunanin tambayar da yayi masa yake amsar kuwa d'aya ce wato reeetaj itace kawai zata sa yaji baya son zuwa ko ina bama iya india ba,,,

Bhabhai yace shikenan kayi shiru to amma dai ka shirya kaje allah ya tsare kaji ko?? Bazan iya ja da maganar mhamah ba dan nima tamkar uwa take a gareni kaji yaro?? Ka girmama maganar ta dan kuwa nasan bata abu wanda be zama yana da dalilin aikata shi ba ,

Turo baki yayi yace amma bhabhai zanyi kewa da yawa yanzu shikenan babu me kula dani gashi bana kusa da mhamah??

Bhabhai ya jinjina kai yace yaro bansan wane irin sauyi ne ya riske ka ba tabbas ba haka kake ba..
Amma ko meye Wannan ya kasance shi me sa"a ne kuma me nasara sannan kuma abune me matuqar nagarta da da ya iya tasiri a kanka kaje kawai yaro na kiyayewar Allah tana tare da kai babu wata damuwa tinda kasan babban gandu zaka shiga cikin iyaye da kakan ni har sun fimu yawa kuma duk cikin su babu me iya kulawa da kai?????

Qara lafewa yayi yace mhamah ce kawai bayan ita kuma sai guda d'aya bayan haka kuma bhabhai babu wanda ze iya dan Allah to kace mhamah ta tawo da wuri ,

Shafa kansa yayi yace insha Allah da wuri zata zo karka damu,

Haka bhabhai yayi ta janshi da labari had'i da nuni da fahimtarwa sun dad'e sosai suna hira ,,

Washe gari

Suna zaune suna hira Reeetaj tace yalla'bai amma dai kana tsoron mhamah ka sosai ko??

Kallon ta yayi yace me kika gani ??

Yalla'bai kawai alama na gani naga ranar da na buge qanwar ka d'in nan kamar ka tsora ta sosai,

Murmushi yayi yace ba ita nake tsoro ba 'bacin ranta shi nake tsoro kuma nake guje masa ,,

Reetaj tace kaiiii? Yalla'bai baka tsoron ta amma kana tsoron 'bacin ranta? To meyesa nifa ban gane ba ma ,,

Kur'bar shayin sa yayi kafin yace eh haka ne kika ce meyesa saboda ba"a 'bata mata rai
Duk wanda kuwa yayi gangancin 'bata mata rai to shima nasa ran ze 'baci idan akai wasa ma ran kowa ze 'baci,

Da mamaki reetaj tace kenan daga 'bacin ran mutum d'aya sai da yawa su kamu?? ba"a 'bata mata rai ?? to wai saboda me ????

Saboda ita d'in y'ar amana ce kuma a matsayin mutum biyu ake d'aukar ta shiya bhabhai baya son a ta'ba ta kuma duk abunda taso kowa shi yake so babu wanda yake ja da duk wani hukuncin ta farin cikin ta shine farin cikin gidan mu idan babu wannan farin cikin nata kuwa babu sauran farin ciki a wannan ahalin...

Shiru ya d'anyi yace mhamah ta akwai ta da wuyar sha"a ni mutum ce ita me zarra da izza bata son raini koda kad'an bata son musu bare jayayya mutum ce me matuqar son abi ra"ayin ta bata damu da naka ra"ayin ba bata damu da uzurin ka ba tafi so duk abunda ta fad'a ya zama shine daidai ko tsinke ta aje bata so a qetara shi to kawai ka barshi inda ka ganshi sai dai wani abu d'aya ita d'in bata abu da ka sai tayi nazari tayi tunani a kai sannan take zartar wa tana son farin ciki kuma tana son wasanni bata da wani aboki kuma sai mu dukan mu mune abokan wasan ta ko wane wasa za"ayi tana cikin mu kuma har gobe munayi bamu fasa ba,
Indai aka bi ta mhamah za"a rayu cikin farin ciki dan kuwa tana son nishad'i da farin ciki sai dai tanada tsanani bata son qarya sannan bata son munafurci bata son rashin jin magana idan kayi hakan ko waye bazata raga maka ba tana da son y'ay'a amma bata yarda suyi abunda ba daidai ba zata nuna maka zallar 'bacin ranta shiyasa kwata kwata bana so nayi abunda ze 'bata mata rai ,

Ajiyar zuciya reetaj ta sauke sannan tace yalla'bai hakan fa yayi amma naga tana son ka sosai naga duk motsi sai ta kira ka taji kana lafiya?? Kuma kace min a matsayin mutum biyu take to taya hakan ta kasan ce??
Chapter 30 · 0% Book details