Sashe 45
Sirrin Keta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Komai dawo mata yake kamar a mafarki duk ta kasa nutsuwa ko abinci ta kasa ci har wani zazza'bi zazza'bi ne yake naman kama ta,
Ayaana..
Kukan ta take yi iya qarfin ta babu yadda mhamah batayi ba akan tayi shiru amma abun yaci tira kowa yayi rarrashin duniya taqi gashi dare yayi kowa hankalin sa yaqi kwanciya dan kuwa juyin duniya taqi fad'ar abunda yake damun ta..
Mhamah tasan makarin ta dan haka tace ayaana maza jeki kice bhaiya yazo ina neman sa,
Bata son yiwa mhamah gardama dan kuwa gardama yana d'aya daga cikin abunda ta tsana dan haka ta tashi tana kuka ta nufi sashin sa,
Lokacin yana zaune yana danne danne sai gata ta shigo a tsaye ta tsaya masa tsege taqi magana sai aikin kuka,,
Sun 'bata lokaci a haka kafin yayi wasu y'an tofe tofe a hanun sa na dama sannan ya tashi finciko ta yayi ta fad'a jikin sa ya d'ora hannun akan goshin ta cikin lokaci kad'an tayi qasa ta zube a wajen rajaf kamar macijin da aka zarewa dafi bacci me nauyi yayi sama da ita..
Tsalleke ta yayi ya wuce ya kalli armaan da ya shigo yanzu yace bhai d'auki yarinyar nan ka maida ita wajen ammuu ko mhamah ,
Armaan beyi musu ba ya d'auke ta ya kaiwa mhamah ita sannan ya dawo,
Washe gari..
Reeetaj bata je aiki ba dan kuwa har yanzu bata dawo dai dai ba.
Ayaan ma sam beji dad'i ba shiyasa ya tashi da wuri,
Ayaana kuwa da safe sai da kyar ta iya tashi saboda mugun ciwon jiki da takeyi sai da temakon ayaat ta samu ta d'an miqe tini ciwon kai ya kama ta saboda tunane tunane gashi ayaan ya kuma kulle mata kai ta rasa meye abunda yayi mata har baccin nan me nauyi ya sure ta,
Roooh da aslam suna zaune suna d'an ta'ba hira aslam yace roooh nifa ina jin tsoron abunda ze afko a gidan nan dan kuwa akwai matsala fa ban ta'ba tunani koda da sunan wasa zanga irin abunda na gani jiya ashe dai bhaiya da gaske yana da wata abokiya??
Murmushi roooh yayi yace eh mana ni tin ranar da ze tafi india na santa kuma da alama ya shaqu da ita sosai kuma babu shakka ma soyayya ce kuma me tsanani banajin bhaiya ze iya rabuwa da ita shiyasa kaga ina ta damuwa tabbas zeyi baqin ciki sosai a rayuwa bhai aslam baka ga har na fara ramewa ta kai ba?? Nasan akwai baqar badaqala kuma gaskiya rayuwar ta abun tausayawa ce shine kad'ai wanda ya kamata ya zame mata bango dama dai mhamah baza ta raba su ba amma nasan dole hakan zata faru...
Jiki a sanyaye aslam yace kaiih shiyasa fa wallahi jiyan nan duk na tsorata gani nake kamar shikenan an gama nasan wallahi idan taga wata tare dashi ba shi kad'ai ba mu kan mu tamu tagama qarewa wai ni a ina ma ya same ta dan Allah,
Roooh yace na bibiye ta na kuma gane wacece ita ita ba y'ar kowa bace y'ar mutane ce kamar dai kai kuma babban qalu bale ne a gaban ta dangin ta duk sun qita saboda wata muguwa ta rusa
Mata farin cikin ta..
Hmm a yanzu babu inda take ra'ba taji sanyi sai wajen d'an uwan mu dan haka koda yanzu yazo yace min ze aure ta zan kasance ina bayan sa,
Aslam yace gaskiya nima haka ko babu komai farin cikin bhaiyan mu ai namu ne,
Sithara da ta dad'e a wajen tana jin abunda suke fad'a da sauri ta bar wajen tana fashewa da kuka shikenan wata qaddarar ta afku ita ta kamu da soyayyar mutumin da bata ta'ba sanin asalin sa ba tasan a ina yake ba kawai daga ganin sa soyayyar sa ta sarqe ta kuma tasan koda ace tasan inda yake ta samu soyayyar sa to fa a gidan su baza'a ta'ba bari ta aure shi ba gashi ita kuma tana jin idan ba shi ba to gaskiya zata kasance ba aure har ta mutu yanzu gashi shima bhaiya ya kamu da son wata bare wadda ko ana ruwan wuta da qanqara baza"a bari ya aure ta ba idan ma suka san da cewa yana soyayya da wata shi kad'ai ma babban tashi hankali ne ita kanta idan ta bari aka gane ta kamu da son wani babu shakka aure zasuyi mata ko bata shirya ba
ko da kuwa kashe kanta zatayi bayan auren kuka take yi sosai abun yayi matuqar damunta,
Da sannu sannu..
Roooh aslam islam sun jero za suyi cikin gida ayaan ya kira sunan roooh duka suka zo a ladabce dan kuwa daga yanayin kiran ma zaka gane na manyance ne...
Fuska a had'e ya tsura masa ido qasa yayi da kai dan shi besan laifin da ya aika ta ba,
Sama taka yaji wani wawan shigaggen mari a kumatun sa ..
Dafewa yayi ko d'agowa beyi ba,
Rai 'bace ayaaan yace bance kar na qara ganin ka da sarqa a wuya ba??? Ko kai kafiri ne???
Girgiza kai kawai yayi.
Ayaan yace bani ita nan,
Ciro ta yayi ya miqa masa ya kar'ba sannan yace na kuma gani ka saka ta kai da ba arne ba kazo kana wani sawa mutane sarqa kamar wani d'an daudu ware daga nan ko na shola ka yanzu,
Wucewa yayi kamar ze hantsila sauri sauri yakeyi jikin sa sai kakkarwa yakeyi idanun sa kuwa sunyi murtuk kai tsaye sashin su ya nufa su aslam suna bin bayan shi ko kallon su beyi ba islam ne ya fara qoqarin bashi haquri ai kuwa yayi kanshi da fad'a sama sama sai da ya gama zazzaga masa masifa sannan yayi shiru sai kai kawo yake yi a falon ya kasa zama zuciyar sa sai tuquqi take ya rasa ina ze sa kansa,
Misalin qarfe 10:00pm
Suna zaune shida armaan suna hira aslam da islam suka shigo kansu a qasa,,
Kallon su armaan yayi yace lafiya kuke kuwa???
Aslam ne yayi qoqarin cewa bhaiya rooooh ,
'Dagowa ayaan yayi ya kalle su yace hmmm???
Aslam yace bhaiya roooh yaqi nutsuwa ko Abinci yaqi ci ,
'Dan tsaki yayi yace kuje kawai ,
To suka ce sannan suka juya,
Armaan yace yau ka ta'bo wutar baya kenan sai rigima yana can zuciya ta hana shi zama hamagon d'an uwa na ,
Ayaan yace ai tara ce take dukan goma kaima ai haka kake ba wani banbanci ku dinga sawa ran ku salama dan Allah kamar ba maza ba??
Armaan yace eh ba mazan bane mata maza ne ,
Murmushi kawai ayaan yayi ya tafi sashin mhamah,
Tana zaune a falo tare da shukreey tana koya mata karatun alqur"an ya shigo kusa da ita ya zauna kamar baze magana ba sai kuma yace mhamah roooh fa,
Tace uhmm ka mare shi ba???
Qasa yayi da kai yace eh mhamah baya jin magana ne nace ya dena saka sarqa amma yaqi kawai shine na mare shi ya 'bata min rai ne,
Murmushi tayi tace yayi daidai kayi abunda ya dace nima nace ya dena yaqi sai yace wai shi kwalliya ce amma dai yanzu da ka nuna masa 'bacin rai ta yuwu ze dena...
To amma mhamah yaqi cin abinci fa kuma nasan ko bacci baze iya yi ba,
Shiru tayi kafin tace baka son 'bacin ran d'an uwan ka gashi baka iya rarraahin sa ba ya kamata ace ka koyi sarrafa shi amma sai dai kazo kace min mhamah wata rana idan ya kasance bana nan fa???? Sai ka zuba masa ido kenan kai fa d'an uwan sa ne ya kamata ka iya rarrashin sa..
Karka damu kawai kaje ka ci gaba da abunda kake yi zan shawo kansa kaji ko???
To mhamah,
Tashi yayi ya koma ita kuma ta nufi sashin su,,
Meyesa kake ta fushi har haka ne roooh ??
A zuciye yace mari na fa yayi ya za"ayi ya mare ni haka kawai ni kawai mhamah ki barni kawai ni dai,
Abu me sauqi ruwa me d'an banzan sanyi ta d'akko ta tsiyaya masa ta bashi da yaqi kar'ba sai da tayi masa da gaske sannan ya sha,,
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya fara kuka..
Shikenan ta wucu...
Bayan ta d'auki tsawon kwana uku bata je ba sai a na hud'un ta koma kamar babu abunda ya faru tini ta watsar da komai gigi da rawar kai kuwa babu abunda ya ragu...
Tsura masa ido tayi shi kuwa sai aikin sa yake d'an murgud'a baki tayi kafin tace yalla'bai ina da magana,
Murmushi yayi yace ina ji ai,
Wai da gaske kai ba musulmi bane??
Sororo yayi yana kalllon ta kafin yace na zata kinfi kowa sani na ashe ba haka bane ??
Meyesa zakiyi min wannan tambayar??
A tunani na koda wani ne ya fad'a bazaki yarda ba bare kuma ke ki fad'a da bakin ki,,,
Kodan kinji na fad'a haka ranar nan??
Tace to eh mana yalla'bai ai ni na d'auka da gaske
Haba ke kam da wasa nake miki saboda kin kirani da haka ne yasa nima nace miki haka kuma gatse nayi miki ba da gaske ba duk dangin mu gaba da baya duk musulmi ne..
Kina d'auka a india babu musulmi ko ??
Gyad'a masa kai tayi,,
Yace akwai su kuma akwai addinai kala kala suna da yawa ne shiyasa ba"a gane adadin su kuma a yanayin shigar su bazaki banbance su ba shiyasa, kuma ba'a fiye nuno su a film ba shiyasa bazaki sani ba duk da ke bama kallon indian film kike ba amma nasan awaaz d'in ki tana kalla kuma itace take baki labari ko???
Eh mana kuma tace min babu musulmi sai y'an kad'an shiyasa ma na yarda kai ba musulmi bane,
Murmushi yayi yace to yanzu ai kinji dil ko??
Tace eh.. Yauwa to yalla'bai wai wannan zanen meye yake a dokin wuyan ka???
Murmushi yayi yace wannan hatimi ne na tambarin dangin mu ,
Tace kenan yalla'bai d'an gidan ku kawai ake yiwa ???
To wai kuma da zafi??
Kuma ana yiwa mata ma kuwa???