← Book details Sirrin Keta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 47

Sashe 5

Sirrin Keta Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Haka ake shan fama tsakanin awaaz da reetaj taki yarda da cewar sonta yake ita kuwa awaaz ta lura da yanayin sa ta tabbatar son yayar ta yake amma reetaj tak'i yarda
Kuma bata fasa kin daga wayar sa ba
Yau yazo da yamma ya tura salma ta fad'a mata amma sai cewa tayi ace bata nan
Haka salma ta juya awaaz tabi bayan ta bayan salma ta isar da sako awaaz ta karasa gurin,
Fad'ad'a murmushi yayi yace kanwa ta gaishe shi tayi tace dan Allah idan ba damu zanyi maka wasu yan tambaya yace Allah yasa na sani ''
Ki shigo motar mana gaba ta shiga ta zauna sannan tace dama kawai tambaya
Ce akan tsakanin kai da yaya ta
Murmushi yayi yace gaskiya ne toh nidai gaskiya suna na muhsin Ahmad usman ni da kanwa ta ne kawai a gurin iyayen mu ina aiki a wani babban company wanda ya kasan ce ni babba ne a cikinsa gaba daya company din a karkashi na ma yake nine me alhakin kula da duk wani al'amra nasu bayan haka ina harkar kasuwanci na daban baba na kuma dan kasuwa ne har kar kasuwanci yake mami ta
Kuma macen gida ce amma koda yaushe fatan ta kawai na samu mata sirika tagari yar mutunci yar manyan mutane
Shine mafarkin mahaifiya ta kullum addu'ar ta in samu gwana ta ana cikin haka kuwa ido na ya kai kanta lokaci daya kawai naji ta matukar tafi da imani na
Naga kamala da dattaku irin nata abin yabani sha"wa sosai nasan mami zatayi farin ciki da samun sirika kamar reetaj gefe guda ma ban ankara ba zuciya ta ta kamu da son reetaj awaaz gaskiya dayace ina matukar son yayar ki reetaj ina sonta sosai sai dai kuma na lura karatun ta tasa gaba kawai ina fargabar taqi amincewa da soyayya ta zan cutu idan narasa soyayyar reetaj nakasa gaya mata asalin gaskiya ta bansan ta ina zan fara ba reetaj duk da yarinya ce amma tanada kwarjini kawai sai inji ta cika min ido bazan iya gaya mata ba awaaz dan Allah zaki temaka min??
Awaaz ta sauke faffad'ar ajiyar zuciya farin ciki kamar tayi hauka da kyar ta iya dannewa dan kar ya gane yanayin da take ciki tace eh zan temaka maka yaya muhsin soyayyar ka ba irin ta yasarwa bace kai mutumin kirki ne yaya muhsin babu budurwar da zaka sota tace batasonka
Amma nasan halin yaya ta idan nice na fada mata zatace karya nake idan kaine ka fada mata bazata amince ba zatace meyesa daa, baka fada mata ba?
Toh kawai abunyi anan shine ka samu magabatan ka da maganar auren ta kawai sai suzo wajen su abban mu ayi maganar aure kawai ayi komai cikin sauki ba tareda an sanar da ita ba idan a bakin abba taji toh nasan zata yarda kuma zata soka musamman idan taji cewa da zancen aure kazo dan ita yaya batason shiririta kawai ita gaskiya da gaskiya shine tsarinta ,
Ajiyar zuciya ya sauke gami da lumshe ido yace gaskiya naji dadi sosai kuma nagode da wannan kyakkyawar shawarar nasan ta bangare na iyaye na basu da matsala indai har abba ze amince kinga ai soyayya ta tana gab da nasara gaskiya nayi godiya mara adadi kanwa ta kin ceci rayuwa ta ' awaaz tayi murmushi tace babu komai yaya muhsin ai babu batun godiya Allah ya temaka , ya amsa da amin, kafin yace wane irin tukuici zan baki kanwa ta??
Zaro ido tayi tace tukuici kuma yaya muhsin haba dai gaskiya ba abunda zaka bani kokarin bude kofa ta fara amma kofar taki buduwa kudi masu yawa ya cira ya bata kauda kai tayi tace a"a dan Allah kabarshi mene na wani tukuici yaya??? Murmushi muhsin yayi yace shikenan babu tukuici ki karba kyauta ce dan farin cikin soyayya ta dan Allah kar kice a"a idan baki karba ba bazanji dadi ba, kamar bata so ta karba tareda yi masa godiya sukai sallama ta shiga gida reetaj tana daki a kwance ta shigo hada kudin tai cikin hijab ta boye, reetaj tace ina kikaje ne awaaz??
Amm.oh.kawai naje gidan su kawata ne afiya' reetaj tayi tsaki tace a qawaye dai zaki qare , eh naji wani ma yayi kawayen mana . ni bana ra"ayin su kwata kwata banda haka ai da nayi tsaki awaaz tayi tace shiyasa kike takurawa mutane dan bakisan abota ba ,
Murmushi tayi tace abota indai ta wuce wadda take tsakanin nidake toh bansan wata ba,
Kauda kai awaaz tayi tace ai kuwa zaki santa kwanan nan keda yaya muhsin idan kuka fara tsinkar fure... Magana kikai ?? Ta jefeta da tambaya saurin girgiza kai tayi tace a ah.. Ba magana nai ba waya ma nake ni , kyaji dashi dai reetaj ta fada gami da gyara kwanciyar ta
Chapter 5 · 0% Book details