Sashe 14
Sirrin Keta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Suka sa dariya salma tace wallahi kuwa wai neman aiki ma take inda zaki san kawai ballagaza ce kin tsufa a gida kinyi kwantai kin rasa miji kin kasa auruwa amma a hakan ma aiki take nema hahahaha kina da aiki jaa,
Haka sukai mata tatas sannan suka haye gado sukai bandam bandam ,
Bayan ta gama cin kukan ta
Share hawayen tayi ta tashi tana neman wajen kwanciya sunyi baje baje a gadon bata da gurin da zata kwanta da taga guri taje zata hau sai su matso haka sukai ta yi batada halin magana tana fad'an d'aya zasu fad'a mata goma qarshe ma su had'a mata sharri a wajen abban su da y'an uwan ta su ci mata mutunci ,
Zanin ta ta d'akko ta shinfid'a a qasa tayi kwanciyar ta lokacin da take buqatar bacci ya d'auke ta sai yaqi zuwa sai faman tunane tunane take wani sabon shauqin son ta samu aiki ne yake qara tunzura ta har ta fara tunanin komawa bata samu bacci ba har sai da ta tabbatar wa kanta zata koma wajen neman aikin koda za a qara wulaqanta ta maganganun awaaz da su salma sune suke tunzura ta har ta yarda da komawar a cewar ta idan rabon ta ne zata samu,,
Washe gari da shirin ta ta tashi tin wuri lokacin da ta isa kamfanin yalla'bai ko isowa beyi ba da alama d'an guntun mutumin nan yayi mamakin qara ganin ta har sai da ya qara tambayar ta wai kece again ?
Tace masa eh,
Yace ban ta'ba ganin wanda yayiwa yalla'bai haka ba ,
Hararar sa tayi tareda turo baki bata kulashi ba tana baya baya take cewa wannan d'an guntun mutumin ya cika masifa ko ina ruwan sa da be ta'ba ganin wanda yayiwa yalla'bai haka ba toh tinda haka ne tayuwu qaddarar mu tana sarqe da juna ne ko kuma taurarin mu abokan juna ne"
karo tayi da mutum ta juyo a firgice ganin yalla'bai yasa tayi baya tana zaro ido ta qame guri d'aya tace ya haquri yalla'bai kuskure ne dan allah k....
Watso mata idanun sa da yayi ne yasa ta had'iye sauran maganar yasa kai ya wuce ciki,
Gyatsine fuska tayi tace mutum sai miskilanci kawai,
Bin bayan sa tayi tana cewa yalla'bai dan allah kayi haquri ka d'auke ni aikin nan zan iya mutuwa idan narasa aikin yalla'bai!!,
Yalla'bai dai ko juyowa beyi ba,
zuwa yanzu d'an guntun mutum dai ya saduda ya sallamawa reetaj dan haka be hana ta bin yalla'bai ba,
Kujerar sa me kama da ta mulki ya ja ya zauna,
a kansa ta tsaya tsegege tana cewa yalla'bai dan allah kayi haquri ka manta da komai bazan kuma kuskure ba ka fad'a min duk abinda baka so sai in dena,
Wannan abun me kama da remote taga ya matsa dandanan d'an guntun mutumin ya shigo kansa a qasa ya tsaya cike da jiran umarni ,
Qurawa reetaj ido yayi sosai
Sai a lokacin yalla'bai ya ta'ba qare mata kallo har haka a ganin ta,
Bayan ya gama qare mata kallo ya janyo biro da takarda ya fara rubutu bayan ya gama ya miqawa d'an guntu,
Reetaj taso ganin abunda ya rubuta sai dai ko (a) bata gane a ciki ba saboda da irin rubutun indian yayi,,
'Dan guntu kuwa fara karan ta takardar yayi sannan ya fassara mata da turanci...
Madam abunda yalla'bai yace shine...
Wannan abun da kike ba me dacewa bane kuma nagaya miki baki da gurbin aiki a wannan kamfani,
A yanzu ma ba aikin kamfani ne ya dace dake ba kije kiyi aure ki zauna kiyi aikin gidan ki shine wanda yafi dacewa dake dan ke y'a mace ce ,
Madam wannan shine saqon isarwa na yalla'bai a gareki ,
Shiru reetaj tayi jikin ta yayi mugun sanyi wasu zafafan hawaye ne suka bayyano kan fuskar ta bata san lokacin da surutai suka fara fitowa daga bakin ta ba..
Baka sani ba baka sani ba baka sani ba yalla'bai baka san abunda ya faru dani ba da bazakai min zancen aure ba kowa burin sa nayi aure bakuyi la"akari da abunda ya faru dani ba kawai shekaru na kuke gani kawai kowa ya d'ebo sharar sa sai ya juye a kaina ni kuwa meysa tawa qaddarar tazo a haka meyesa kowa yake qyamata meyesa kowa ya tsaneni ashe haka rashin aure yake???
Kuka ne ya kufce mata ta durqushe a wajen taci gaba da cewa nima zanyi auren idan lokaci yayi zanyi aure allah yabani miji nagari wanda yake sona da gaskiya badan wani abu ba nima inyi aure ko zan zama mutum ko da za a dena gudu na ,,
Yalla'bai a da ina tunanin kamar rashin gurbi ne yasa kaqi d'auka ta ko kuma laifin da nayi na zuwa gidan ku amma yanzu na gane ba haka bane kaima ka tsane ni ne,
meyesa kowa baya fahimta ta meyesa babu wanda ze iya saurara ta meyesa qaddara ta rabani da komai nawa damuwa ta qulla abota dani yanzu a haka kenan zan kasan ce ??
Badan komai nazo nan neman aiki ba badan son wani abun duniya ba kawai ina neman aiki ne domin rage damuwa naso in shiga cikin mutane koda zan samu salama amma hakan ya gagara babu komai na yarda da Allah na yarda da qaddara ta a haka rayuwa ta zata qare kamar yadda suke cewa haka ne na gazgata maganar ki awaaz'"""
Insha Allah babu ni babu qara zuwa wannan kamfani na haqura zan nesanta da kamfanin ka yalla'bai zan koma in cigaba da rayuwa ta ta daaa tinda bakason gani na zan 'bacewa ganin ka yalla'bai bazan kuma zuwa ba na haqura da wani aiki ko nameye zanje in jira mijin da ze aure ni ya riqeni amana sai in aureshi inyi aikin gidan ,
Tashi tayi tana kuka tayi hanyar fita har taje qofa wata daddad'ar murya ta dakatar da ita..
Ina son jin labarin ki!!!!!!
A firgice ta juyo ta kalli yalla'bai tana cewa dama ka iya magana ???
Ganin ba ita yake kallo ba da alama ma ba shine yayi magana ba yasa ta juya tana share qwallah tace haukan nawa har yayi tsanani haka? Har ya kai in dinga jin magana ni kad'ai ba kowa ??
Har zata fita ta qaraji ance.. kiyi abunda nace in ze yuwu,
Dafe kai tayi tana cewa wayyo Allah na ashe da gaske na haukace??? Dawowa tayi tace yalla'bai dan Allah da gaske ba kaine kayi magana ba ? Kenan da gaske ni mahaukaciya ce ?,
Biro ya miqo mata yace ... Ki rubuta,
Cikin tsananin mamaki tace yalla'bai dama ka iya magana?
Tambayar tata sai da taso bashi dariya ya d'an kauda kai miskilin murmushin sa na gefen baki yayi be kulata ba hakan yasa ta d'auki pen d'in ta fice,
Jinta take kamar ba ita ba kamar a mafarki wai wannan mutumin ne yake yin hausa ? Koda taje gida ta kasa nutsuwa har yanzu ji take kamar ba da gaske bane ga kuma pen d'in da yabata tana ta riqon sa ,
Sai da tasamu tayi wanka sannan taji ta d'an samu nutsuwa kintsawa tayi sannan ta zura hijab ta fito waje abokan nata duk basa nan jikinta yayi sanyi sam batajin dad'i idan ta fito taga basa nan har zata koma taga abdurrahman qanin afiya ta kira shi babu musu yazo tace abdurrahman afiya tana gida?
Eh tana nan,
Yauwa nagode dan Allah jeka kiramin huzaifa a gidan su idan yana nan ,
Abdurrahman yace wane huzaifan? Ohh jaa gayya?,
Gyad'a masa kai tayi tace eh jeka dan Allah,
Tafiya yayi ita kuma ta shiga gidan su afiya da sallama ta shiga maman su ta amsa da fara a tace yau kece a gidan namu reetaj?
Murmushi tayi tace eh umma nice ina wuni, lafiya lau ya mutan gidan??
Lafiya kawai tace lokacin afiya ta fito tana dariya tace yaya yau kuma? Kullum sai nace ko shigo gidan mu sai ki qi sai yau lamarin Allah,
Umman su tace wallahi kuwa reetaj ai bama afiya bace kawai take so ki shigo ni nace mata tace miki ki dinga shigowa nan munayin hira mu rage miki kewa kinga ita kuma afiya bata da y'ar uwa mace duk maza ne shiyasa bata jin dad'i amma idan ta ganki sai taji kamar yayar ta sai dai ke kuma a tsarinki baki yarda da shiga maqota ba koh?? Kin yarda dai da zaman hira da su huzaifa a qofar gida ita ma afiyan bata iya zama Ai sai kiga ta d'auki gyale ta fita ku zauna a waje kuyi ta hirar ku abun ku ai nan tamkar gidan ku ne reetaj karki wani damu dan Allah,
Ita dai reetaj murmushi kawai take afiya kuwa dariya take,
Kafin umma ta farga ta ja reetaj d'aki zama sukayi afiya tace yaya ya batun aikin kin samu kuwa??
Huci reetaj ta furzar ta dafe goshi ta girgiza kai ,,,,
Afiya tace.. a"a yaya baki samu bane? me yafaru ? Naga kamar bakya jin dad'i ,
Reetaj tace afiya nan gaba ma sai dai kuji na had'iyi zuciya na mutu kawai,
a razane afiya tace yaya kinji abunda kika fad'a kuwa me yayi zafi haka????
Wayyo afiya kowa dai ya samin ido a rayuwar nan kinji shi kuma yalla'bai d'in kawai dagaji ina surutai na na banza yace wai in rubuto masa labarina nufin sa dai abunda yafaru dani wayyoh Allah kuma duk nice na jawa kaina meyesa bana iya sarrafa baki na akan mutumin nan meyesa nake irin maganar nan? Gaskiya ni afiya na haqura da aikin kawai zan mayar masa da biron sa ince bana so bazan rubuta d'in ba,, wai meyesa ma ban ta'ba tunanin yanajin hausa ba???
Ido afiya ta zaro tareda furta hausaaaa????????
Eh afiya hausa ce a bakin sa rad'au har wani gadara yake ya iya yaren mu,
Afiya tace yau naga takaina yaya hausa fah??
Wai kina mamaki kenan ni da naji ma nazata haukacewa nayi..
Ni zance masa kawai na haqura da aikin ma,