← Book details Sirrin Keta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 47

Sashe 3

Sirrin Keta Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Awaaz ce kwance da laptop a gabanta tana kallon wani indian film reetaj ta shigo da sallama kallon ta tayi tai tsaki tace kina nan kina sana ar kenan
Ba tareda ta kalleta ba tace eh ko zaki siyane dariya tayi tace haba dai se kace wani alawa gaskiya kinma raina ni sosai
Dariya Awaaz tayi tace ni yaya kina bani mamaki wallahi tabe baki tayi tace toh da nabaki wayece ki karba
Dafe kai Awaaz tayi tace wallahi kin rama shikenan ai
Yanzu dai zoki fadamin wanne irin miji zaki aura??
Hararar ta tayi tace ke zaki bani idan na fada miki??
Tace aa kika sani ko inyi addu'a Allah ya karba murmushi tayi tace gaskiya ne amma nidai banida wani buri Awaaz kawai
Kullum adduA ta itace Allah yabani miji nagari me so da kaunata da gaskiya badan wani abuba
Wanda ze iya kare mutunci na kuma ya jajirce akaina ban damu da kyau ko rashinsa ba ko dogo ko gajere nidai na mika zabina ga Allah nasan shine kawai zemin zabi mafi Alkhairi a rayuwa ta
Shewa ta zuba tace lallai yaya gaskiya na yarda wallahi da ake cewa ke ba irin yan matan zamani bane
Wallahi yanda kisan budurwar daa- haka kike har gwara ma budurwar kauye wasu sun dan fara kilewa
Amma ke gabaki dayanki sai a hankali ai dole zakiso namiji wanda idan akace maza toh yana daka cikinsu kinsan akoi namijin da ya amsa sunan sa namiji akoi wanda kawai sunan ya tara
Bakin gado reetaj ta samu ta zauna tace ban gane miki ba fah Awaaz gyara zama Awaaz tayi tace ina nufin dirarren namiji kyakkyawa me jiii da kansa dan gayu ba me irin shigar kolawa ba wanda da kin gansa kinga kudi kinsan kudi sun zauna
Wanda zakije ki huta ba wai kin fita daka gidan a wahale kina saran kinje gidan yanci ya zama kuma harkar kara kara ce kawai ya kasan ce ehh. Kawai ki hau nera ki murza nera shine alaji.. Amma yau an kullo miki dan tsire a bakar leda gobe dan lemon fata habaaa wa yake irin wannan batun
Ai wallahu yaya ina a gidan mijina na kasan ce tamkar wata sarauniya irin ta indian nan ko kasar larabawa yanda ba kowane ma ze iya ganeni ba inzama nakere sa"ah kawai ai idan kika samu dama ki dama yaya shine batu maa' malam ki fito tareda tsulelen mijinki wanda da
An ganku tare ansan kedin eee.. Kawai baraini kamar balarabe ku haifi ya'ya yan duma duma masu zubin larabawa ke goyon cikin ma kawai a kasar waje yaya taaa kuma dan soyayya kamar sharu'khan ya dinga lallabaki yana tarairayar ki yayah... Ganin labarin dokin ranon nata baze kare ba yasa reetaj tace kehh ware da allah rufemin baki nifa kowane irin da Allah yabani inason kayana ba wai se wani me kyauba uban dan ma ko yafi me muni kawai indai yanada kyawawan halaye an wuce gurin wani iya sosai wannan ma damuwar ki ce bahamagiya ki zauna kita lissafin dokin rano da fadan abunda baze yuwu ba yanzu dan Allah a duniyar nan ina zaki samu irin wannan namijin da kike fade kuma a wannan kasar tamu
Muda muke bakar fata amma ke na lura a naki haukan kamar dai irin yan indian da kike gani a film koh toh ai kuwa bazaki taba ganin irinsu a zahiri ba ma sai dai a laptop din nan takarasa maganar
Tana dariya hararar sama da kasa tayi mata kafin tace kefa dadi na dake ana nuna miki gabas kina ke yamma wannan zancen nawa ne yayi miki kama sa dokin rano ?? Rausayar da kai tayi tace toh Awaaz idan ba dokin rano ba ya kike so ince ???
Toh ai kuwa da gaske nake nidai bazan auri mummuna talaka ba gaskiya
Reetaj dai murmushi tayi tace toh Awaaz Allah yabaki wanda kikeso cikin murguda baki tace amin ya rabbi
Reetaj tace alamu suna nuna yau autanci da kuruciya suna damunki koma dai meye ki zubamin ido ke kuma kiji da takabar ki matar liman

Yau dai sun tashi da son ziyara koda suka tambayi amma bata hanasu ba suka shirya suka fita taso su fita a motar gida amma reetaj taqi dan Awaaz bata iya tuki ba reetaj din ce dai aka koyawa ita kuwa tsorone yake hanata hawa gashi kuma basuda tsayayyen Driver
Hakan yasa suke fita a ta haya
Yamma ce likis har an fara kiran sallah suna titi abun hawa yayi wahala hankalin reetaj duk yayi gida Awaaz kuwa aikinta take na ganin mutum ta tanka wannan hancin sa yacika girma wannan tsawon ta yayi yawa wannan yafiye baki ko kuma kiba taiwa wancan yawa
Wata blue mota ce ta gifta ta gabansu tayi can gaba tayi parking cikin takaici reetaj tace wannan
Kuma ko wane yake shirin hawa kaina da mota?? Ta fada tana raka motar da harara dariya Awaaz tayi tace kijifa muna manne da juna amma a hakan kanki kawai ze hau ??
Dariyar ita tayi tace naga ai ni yafi kawowa hari sukayi dariya Awaaz ta maida hankali kan motar kyakkyawan saurayin da yafito daka cikin motar ba karamin
Tafiya da imanin Awaaz yayi ba ware ido ta karayi tana kallon sa ta kara kallan falleliyar motar da yake ciki
Woww ta furta hakan ya jawo hankalin reetaj tace lafiya dai Awaaz lafiya mana kalli gayen can dan Allah
Wanda ya kusa buge mu wallahi kyakkyawa ne ajin karshe ga iya salo ga takunsa ma kawai abun kallo ne gashi dai da alama babban ne tsaki reetaj tayi tace Allah yabaki lafiya Awaaz ita kuwa kamar tunzurata take sai ma kara cewa tayi ki kalla yaya wajen mu yake tahowa fah reetaj tace nidai Allah yay min tsari da mugu ko muguwa ni wallahi masu kudin ma tsoron su nakeji kamar yadda Awaaz ta tsammata wajen nasu yazo sannun ku yace
Awaaz tace yauwa yace daka ina haka ?? Karaf reetaj tayi tace inda muka baro ya saki wani yalwataccen murmushi yace toh sai ina?? Ta kara cewa inda zamu shikenan koh ?? A kaji amsa maza ka ware fece maza ta fada tana masa nunin hanya da duk yatsunta guda hudu murmushi yayi yace haba kanwata naga kamar na kusa buge ku ne shiyasa nace bari na baku hakuri reetaj zatayi magana Awaaz tai saurin dafeta tace ahh babu komai ai yace toh shikenan zan iya rage muku hanya naga magrib tayi kuma abun hawa yana wahala koh?? Cikin fara 'a tace eh hakane
Tsaki reetaj tayi tace haka ne ana wahalar mota amma bama bukatar temakon ka wuce kawai a dan hasale Awaaz tace haba yaya meyesa kike hakane dan Allah kidena irin haka maida kallon ta tayi kan gayen tace babu damuwa dama mun gaji da yawa yayi murmushi yace toh kanwata muje koh ??
Reetaj zatayi magana yace dan Allah ko dan kanwar ki kizo ki shiga mota ta ko kinga nayi kama da barayin mutane ne cikin raha yayi maganar yake reetaj tayi tace a'a amma.... Katse ta yayi da cewa idan har kinga nayi kama da barayin toh kar ki hau kawai shikenan amma idan kin tabbata banyi kama da irinsu ba ?? Ga hanya tasan dai idan tace yayi kama da mutanen banza ma karya take bare kuma taji yayi kama da barayi hakan yasa ta shiga baya ita kuwa Awaaz tana gaba abunta ( ni kuwa nace hajiya hauwa da kokari... Hattara dai ...ehem...ehehem ........nayi shiru kawai🤪)
Chapter 3 · 0% Book details