← Book details Rayuwar Mace Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 66

Sashe 66

Rayuwar Mace Complete Hausa Novel · about 4 min read

Dariya suka saka dukka, ta mika ma Abdallan ya karba yana kura ma yaron ido, da yake kama dashi sak tamkar an tsaga kara. Fita Mami sukayi da Anty Faty, ya hadasu ya rungumosu zuwa jikinsa, farin ciki na lullube shi.
Zuwa akayi aka saka mata drip saboda ta dan samu karfi dan ta galabaita sosai, Allah ma ya taimake ta babu dinki, tea aka hada mata tasha me kauri, shi kuwa bakon duniyar sai baccin da yake tsakanin sa da Allah. Huduba Abdallah yayi masa sannan ya fita dan yin sallar asubah a masallacin kusa da asibitin.
Da sassafe labarin haihuwar ya karade yan uwa da dangi, nan fa aka soma tururuwar zywa asibitin, kafin kace me an cika musu asibiti taf, gashi babu damar sallamar ta sai babban likita yazo ya duba su da babyn, haka akayi ta tururuwar zuwa har aka sallame su, a tunanin ta zai ce a kaita gida dan sun taba maganar dashi yace ta bari dai tukunna, sai gani tayi an dau hanyar gidanta, tun daga nan ta gane ba zai yarda taje gidan ba, shiyasa ma yaki yarda su shigo mota daya, sai kawai ya sakata a motar MD yace zai tsaya ya siyo abubuwan da ake bukata.
Umma ce ta kira bayan sun koma tayi mata sannu, ta kuma yi mata bayanin abubuwan da ya kamata ayi kafin a turo me zauna mata, su Ya Hadiza zasu kula da ità kafin a dauko matar. Abba ma ya kira bayan nan shima yayi mata sannun, suna tare da Hajiya Mama a lokacin ya bata wayar, sukayi magana, sannan ya kashe. Rauda na zaune a kusa da ita bayan ta gama wayar, tace kinsan me? "

" Me? "

" Ya Adam fa ya bar kasar gaba daya, idan kika ganshi wallahi ba zaki gane shi ba, he's a change person, ya chanja sosai wallahi, har gida yaje ya bawa su umma hakuri da Abba, ya kuma ce a baki hakuri kema, daga baya naje gida umma take cewa ai ya tafi karatu. "

" Allah sarki, haka ake so ai, ka gane gaskiya ka tuba, ni na riga na dade da yafe masa, ban rik'e kowa ba dan nasan hakan da nayi ne ya sa Allah ya duba ni, ya musanya min da mafi alkhairi. "

" Gaskiya dai, ai wallahi halin ki yayi ne Ya Asma'u, dole ya Abdallah ya soki, kina da kirki da sanin yakamata. "

" Banda fasa kai, kema ai Rauda baki da matsala. "

" Ban kaiki ba wallahi, ai kaf gidanmu babu kamar ki, baki ga yanzu ma umma da Abba sun fi son ki ba, ai halin ne ya jawo. "

" Ba wani sona, kawai dai kawai dai. "

" Ki yarda Allah. "

" Asma'u taso ruwa yayi. "

" Tam tam! Wallahi akwai dabi, ruwan zafin nan ko masifa. "

" Karki kashe mata guiwa malama. " Ya Hadiza tace, a sanyaye Asma'un ta tashi, ta bi ya Hadizan suka shiga toilet din, ta gaggasa mata jikinta da ruwa me zafi sosai da towel, tace sai yamma za'a fara na darbejiya, dakin su da Abdallan ta shiga, ta zauna tana shafa mai sai gashi ya shigo da ledoji niki-niki, ya ajiye su a gefe ya zauna daf da ita yana karbar man ya tayata shafawa. Kaya ta hau sakawa shi kuma ya fita ya dauko babyn, ya dawo dakin bayan ta gama, ya bud'e camera dinsa ya dauke su a hoto ita da shi da dan jinjirin, yayi mata kiss a goshi yace

"I love you so much matata, nagode da wannan kyautar da kika bani, Allah ya raya mana Ahmad."

"Ahmad sunan sa?" Tace da sauri

"Sunan da kika ce min kina so kin tuna?"

"Nagode nagode mijina, Allah ya barmu tare cikin amince da kaunar juna, Allah ya kara buda maka kofifin arzikin ka, ya raba ka da iyayenmu lafiya."

"Amin Ma'u ta, Amin ya Allah."

***Alhamdulillah ya Allah. End!!!!!

***Assalamu alaikum masoya zafafa biyar, ina muku fatan alkairi a duk abinda kuka saka a rayuwar ku, mun gode da zabin zafafa biyar a ko da yaushe. Ina neman afuwar wadanda na batawa awannan littafin nawa, dan Allah kuyi hakuri ku yafe min, hakan ajizanci ne na dan Adam, nima na yafewa kowa, Allah ya bamu sa'a a rayuwar mu, ya bawa yan matan cikin mu mazaje na gari, ya kara zaman lafiya da fuskantar juna masu auren, wanda suke cikin matsala a gidajen auren su Allah ya kawo musu dauki, ya yaye musu alfarmar annabi Muhammad SAW.
Mun gode mun gode mun gode da jimirin bibiyar zafafa biyar
Allah ya sake hada mu da alkhairin sa
Chapter 66 · 0% Book details