← Book details Rayuwar Mace Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 66

Sashe 65

Rayuwar Mace Complete Hausa Novel · about 8 min read

****Kwana biyu tsakanin zuwan su aka shigar da Adam kotu, bayan an tuntubi su Abba dan shine akan komai, sai a ranar ne mama taga Adam din nata da ya fige ya fita hayyacin sa, be san wahala ba be saba da ita ba kwata kwata, sai gashi ya fad'a cikin kaddara, rayuwa ta juya masa baya, kuka ta toshe bakin ta, ta dinga yi tana daga zaune a baya kusa da Nadeeya.
   Baa sha wata wahalar shari'a ba, tunda dama ya amsa laifin sa, kuma duk wani bincike DSS sun gama shi tas, hukuncin shekara uku aka yanke masa a gidan kaso, ku kuma ya biya tarar kudi. Dora kansa yayi a kan katakon wajen yana jin duk duniyar ma ta fitar masa akai. Abdallah da yake zaune a wajen ya dubi Hajiya Mama da Abban su Asma'u dashi yake ta fadi tashi akan case din, ya nemi lauyan da ya gabatar da karar akan maganar tarar, sukayi exchanging number yace suyi waya, cell aka maida Adam daga nan mama ta shiga tunanin yadda za'a biya tarar dan ba zata iya jure Adam a gidan yari ba, suna da manyan kadarori dan haka dasu za'a yi amfani a biya tarar ko da zasu talauci su tsiyace, gefe ta kira Abban ta fad'a masa yadda za'a yi, yace mata yana zuwa dan Abdallah ya same shi shima da wani zance na daban. Daga nan suka tattara suka yi gida, washegari Mama na ta jiran Abba yazo aje ayi abinda za'a yi wajen siyarda abubuwan da za'a siyar sai ga abban yazo da Adam din, da gudu ya rungume Maman yana rushewa da kuka, itama kukan ta shiga yi da k'yar aka basu baki sukayi shiru kafin Abba ya fad'a mata yadda akayi, Abdallah ne ya biya masa tarar ta hannun Abban. Farin ciki hade da kunya suka sake kama Maman, ta dinga jera masa addu'a Abban an amsawa.

***Rayuwa gaba daya ta sauya wa Asma'u, kuncin da ta sha na baya duk ya wuce, bata san komai ba a yanzu sai soyayyar Abdallan me tsayawa a rai, be taba daga mata murya ba, bare yace zai ci mutuncin ta, kullum cikin hidimarta yake da ta gidan su, babu abinda zata ce masa face ta gode wa Allah da yayi mata sauyin alkhair. Bangaren su mom bata da matsalar komai dasu, yadda suke son ta ba kad'an bane,ba kuma su taba nuna mata bakin cikinsu akan yadda Abdallan yake kula da ita ba, baya iya boye soyayyyarta a gaban kowa, duk da bashi da hayaniya amma duk abinda ya kasance nata ne, sai in da karfin sa ya kare.
   A lokacin da ta fara laulayi daina zuwa ko ina yayi, ya tare a gidan shi yake mata komai, har sai da cikin yayi kwari sannan ya barta, a lokacin ne kuma aka shiga maganar bikin MD da Amaryar sa Khadija, yar sister din Mom ce wani zuwa hutu da sukayi suka hadu shikenan kuma sai labari ya sha banban, a falon Asma'un suke zama susha soyayyar su har kuma magana tayi karfi manya suka shiga. Lefe Abdallah ya fara hada masa, dan dama yace shine zai yi komai na bikin, baya son hannun MD din ko kad'an, shi da ita suke fita su siyo kayan idan sun ga na babies ma sai su kwaso, suka hada kaya masu yawan gaske na gani na fad'a, ranar kai lefe akai kai daga nan aka saka bikin wata biyu, lokacin cikin Asma'u na da wata takwas da sati biyu
   Tun da satin bikin ya kama Abdallah ya hanata komai, yace kuma kar a sakata komai saboda cikin, taso tayi masa magana dan ita kalau take jinta amma yaki barin ta ma tayi magana, dole ta hakura sai dai ta zauna tana kallon su suna aikin, dan ko da tayi attempt din tayasu fad'a Mami tayi mata, cikin shigar wasa tace mata

"Ban shirya korafin Abdallah ba, yanzu zaizo yayi ta mita wa ya saka masa mata aiki."

Dariya aka saka a wajen ita kuma duk kunya ta kamata, haka ta hakura ta zauna din har aka shiga bikin gadan gadan. Ta gayyaci yan gidan su ranar mothers day da za'a yi a cikin gidan, Ya Hadiza da Umma sai Rauda da Abbati ne suka zo, ya zauna shi ya jirasu a mota suka dan dade sannan suka tafi. Washegari akayi daurin aure, umma ta saka akayi mata snacks masu yawa ta aiko abbati ya kawo da wuri , su kayi ta godiya kuwa. Wajen azahar umman tazo akayi yinin da ita da la’asar abbati ya zo ya dauke ta suka tafi.

   Duk da babu abinda tayi na aiki amma a gajiye take tikis, ga kafarta da ta kumburo sosai da Da wuri ta koma shashen ta dan bata jira ma an kawo amarya ba, itama anan cikin gidan aka gyara mata waje, bata jin dadin jikinta tun wajen laasar, kawai ta dinga daurewa ne. Ruwa ta saka me zafi tayi wanka dashi, ta dauko doguwar shimi ta saka ta kwanta akan gado ta saka pillow a tsakanin kafafunta ko zata ji dadi. Shigowa yayi da dan saurin sa ganin be ganta a falo ba, ya zauna a gefenta yana tambayar ta menene?

“Ba komai fa, kawai hutawa nake.”

“are you sure?”

“Ba komai fa, karka tashi hankalin ka.”

“Still dai, idan kinji wani changes ki fada min.”

"In Sha Allah."

"Allah ya raba lafiya, I'm very nervous wallahi, tunda month din nan yazo."

"Nima, khair in sha Allah."

"In sha Allah."

"Bari na miki massage, naga kamar kafarki ta kumbura."

"Aiko da naji dadi, ji nake kaman dutse kafar wallahi."

"Ayya sannu." Ya daga kafar ya dora akan cinyar sa ya dinga matsa mata a hankali, hakan ya dan sakata jin saukin kafar, sai dai kuma sanda ta yunkura zata mike wani abu ya cikareta daga cikin ta, ta dafe cikin tana dukawa

"Wash Allah na." Ta sauri ya jefar da towel din hannun sa ya riko ta

"Menene?"

"Cikina!"

Sai ta sake durkusawa, tana jin wani abu na dunkulewa a mararta, kafin ya tattare ya chure a waje daya, da gudu ya fita ya ma manta da ga shi sai wando 3-quarter da yar singlet, sai da yaje sannan ya tuna kayan da ke jikinsa dan yayi shirin wanka ne a lokacin, gashi ana biki sai ya sake juyowa da sauri, yazo ya sameta har ta kai kasa, wayar sa ya dauka ya riketa da hannu daya, ya kira wayar Mami da hannu daya, tana dagawa yace

"Mami Asma'u!*

" Gani nan,. " Ta amsa masa itama a rude, da sauri ta karasa part din nasu ita da Anty Faty, zuwa lokacin har Asma'un ta soma galabaita, suka taimaka mata Anty Faty ta dauki jakar kayan haihuwar suka ce ya kunna mota, manta mukullin yayi har ya fita ya sake dawowa, tsaida shi Anty Faty tayi ta karbi keys din tace ya taimaka a fito da Asma'un dan taga alamar ba lallai ma ya iya driving din ba, haka akayi kuwa ita ta tuka su, suna zuwa aka karbe su aka shiga da ita dakin haihuwa, lokacin har ta kai 5cm cikin ikon Allah.
Zagaye ya dinga yi a wajen ya kasa zaune ya kasa tsaye, sai addu'a yake, su kansu su Mami a cikin tararradi suke, dan haihuwa siradi ce, Allah dai ya sauketa lafiya. Baba Alhaji ne ya kira Mamin ta fad'a masa halin da ake ciki, yayi addu'ar sauka lafiya, Mom ce kawai da sauran family suka karbi amarya sanda aka kawo ta, ita kanta hankalin ta na asibitin dan da ba zata taba iya zuwa bane, tasan Mami zatayi komai fiye da yadda ma zata iya, bata so a sanar da mahaifiyar Asma'un dan ba zata iya bacci ba, duk da tasan dama ba lallai su yi tunanin fad'a mata a halin da ake ciki ba.

Haka kawai Umma sai ta kasa bacci cikin dare, tunanin Asma'un kawai ya fado mata, tashi tayi tsam ta dauro alwala tazo tayi sallah raka'a biyu ta roki Allah ya raba su lafiya da cikin ta, dan tun ganin da tayi mata dazu duk tausayin ta ya kamata , cikin yayi kasa sosai alamun haihuwa tazo. Da k'yar ta koma bacci wajen uku da rabi.
Asma'u ta sha wahala sosai dan daga 5cm din nan sai ya tsaya chak, sai uban ciwo amma baya karuwa, haka sukayi ta inducing dinta sai daga karshe wajen ukun na dare haihuwar ta taso gadan-gadan, da Kuma Allah ya kawo ta da sauki sai nan da nan ta haihu, sai kukan jariri suka ji, Abdallah ne yayi hanyar dakin a gigice

"Mami kamar kuka ko?"

"Eh kukan jariri ne Abuya, ta sauka"

Cigaba da zagaye yayi a wajen dan sai ya fara jin halin da Asma'un take ciki, wata nurse ce ta fito suka wajenta da sauri

"Ta haihu, kin yi sabon ango."

Tace ma mami.

"Maman fa?" Ya tambaya

"Lafiyar ta kalou, suna gyara su ne."

"Alhamdulillah!" Yace sai kuma ya saki fuskar sa, ya hau farin ciki. Sai da aka gama gyaran babyn da Asma'un sannan aka maida su dakin Hutu, suka samu damar shiga wajensu, yana zuwa ya rungumeta tana daga kwancen,

"Sannu kinji? Allah yayi miki albarka."

"Sannu Asma'u, sannu kinji, Allah ya raya ya baki lafiyar shayarwa."

"Sannu matar Abuya, Masha Allah, kaga baby tabarkallah Masha Allah." Anty Faty tace tana daukan babyn, lekowa Mami tayi ta lakace masa hanci

"Sabon me gida, ni dai nafi son tsohon mijina gaskiya yafi wannan hanci "
Chapter 65 · 0% Book details