← Book details Rayuwar Mace Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 66

Sashe 56

Rayuwar Mace Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Lallai, kalli cikin ki fa very flat kaman baa taba saka masa abinci a ciki ba. "

" Let me feed you, bud'e bakin."

Budewa tayi bayan tayi bismillah ya bata abincin, a nutse har ta soma jin ta koshi, ta girgiza masa Kai da ya sake nufo bakin nata alamar ta koshi, be yi musu da ita ba, ya ajiye yana siyaya mata ruwa a glass cup tasha kad'an ya ajiye sannan ya tashi zai tattare kayan tayi saurin tashi,

"Zan kwashe!"

"Yau dai ba ranar aikinki bace, zauna ina zuwa." Yace mata yana tattare kayan ya fita dasu, mayafin ta dauka ta sake rufawa ta koma ta zauna a kasan tana nannade kafarta. Wajen mintuna biyar ta zata zai dawo taji shiru, sai ta fad'a toilet din tayi fitsari sannan ta wanko bakin ta, ta fito ta hange shi a saman gadon ya rufe iya kasan kafarsa yana kokarin saita AC din dakin dan shi zafi yake ji. Gaba daya dakin ya dau sanyi har ya soma shiga cikin jikinta amma shi ko a jikin sa, hakan shine daidai yayi mugun sabawa, da hannu ya yafito ta ganin tayi tsaye, ta karaso kusa dashi ya jawota zuwa kan gadon ta saman jikinsa zuwa dayan sashen gadon,

"Wannan kayan ba zai dame ki ba?"

"Zan chanja."

"Ok, chanja kizo kiji." Yace yana sakinta, ta yunkura ta sauka ta dayan side din zuwa gaban wardrobe din ta bud'e tana kallon kayan ciki da ake jera su gwanin sha'awa, da k'yar ta hango wata doguwar riga mara nauyi kuma da dan tsawon ta dan ta wuce guiwa sosai ta kusan kai idon sahu, dauka tayi ta nufi toilet ta saka ta sake yafo mayafin ajikinta ta dawo dakin, dan kallon ta yayi, ya maida hankalin sa kan wayar sa da yake duba sakonnin mutane, gadon tazo ta hau ta kwanta akan dayan pillow din ta kalli dayan barin ta juya masa baya. Ajiye wayar yayi bayan ya saka ta a flight mood ya saka hannu ya juyo da ita suna fuskantar juna.

"Kina jin bacci?"

"A ah." Ta girgiza kanta

"Ok bari na baki labarin mijinki." Ya sake jawota sosai ta shiga jikinsa kanta na saman kirjinsa

"Sunana ABDALLAH IBRAHIM K'AREFA, d'a ga Alhaji Ibrahim, mu biyar ne a wajen iyayen mu, nine babba sai MD (Mudan) sai Ibrahim (Aby baya nan yana karatu a Sudan) Aysha (Amira) sai Khadija (Ihsan). Baba Alhaji shine mahaifin mu da matan sa biyu Mom da Mami, tun da na taso ban san wani abu wai rabuwar kai ba, mun taso dukkan mu cikin so da kaunar juna, ni da Ihsan ne kadai yayan Mom, amma kuma mun fi shakuwa da Mami fiye da mahaifiyar da ta haife mu. Hakan ya kara mana kaunar junan mu kamar yadda zaki gani a tsakani na da MD, bani da aboki kamar sa haka shima bashi da tamka ta, mune koman juna babu wata baraka a tsakanin mu tun tasowar mu kawo yanzu. Mahaifin mu dan kasuwa ne tun da muka taso muka bud'e ido, hakan ya saka mana so da kaunar kasuwanci duk da be barmu mun tsunduma a harkar kasuwancin ba har sai da muka kammala first degree dinmu daga nan muka fad'a harkar, ina kokarin kamalla degree na na biyu Allah ya dafa min har na bud'e company nawa na kaina da nake yin order motoci ina saidawa wanda na fara kamar wasa. Tun daga nan MD ya karbi ragamar kula da harkokin Baba na waje ni kuma nake kula da duk wani abu da ya shafi cikin gida. Wannan shine tarihi na da gidanmu a takaice, bayan boko nayi karatun addini me zurfi har ta kai na sauke al'qur'an me girma kuma na kammala littafai da dama."

" Masha Allah." Tace tana jinjina kai,

" You will get to know me better in sha Allah,

"In Sha Allah."

A gajiye yake ranar, dan haka kawai rumfa yayi mata da hannun sa, yace mata goodnight bayan yayi kissing forehead dinta. Nan da nan bacci ya dauke shi, ta dinga kallon sa ta dan hasken da ya shigo cikin dakin, tana admiring din sa.

Da safe ta riga shi tashi bayan yayi sallar asubah ya koma sai ta sulale wajen bakwai da rabi ta bar dakin zuwa na kusa dashi, sai a lokacin taga dakin, ta cire kayanta ta zuba su a laundry basket din da ta gani a tsakanin toilet da dakin, ta bud'e akwatin da tazo da ita jiya me dauke da tsofaffin kayanta ta dauki wata bakar abaya ta saka ta fito zuwa falon, babu datti babu komai sai kawai ta wuce kitchen ta tsaya tana tunanin abinda ya kamata tayi, ita ba yarinya bace karama bare ta zauna ta shanya baki bata yi musu komai ba, doya ta dauka ta feraye ta wanke ta tas sannan tayi mata yankan da zata soya ta haka ba tare da ta yanka ba, ta ajiye a gefe ta dubo kayan miya da veggies wasu fresh an jera su akan wani abu shima me kyau wanda duk aikin MD ne da Anty Faty, sai dangin su garlic da fresh ginger suma a gefe daya, sauce zatayi da fried yam din sai ta yayyanka tomatoes tayi grating bell peppers da scotch bonnet, ta yanka albasa me yawa, da hada da half green pepper tayi sauce din me dan karen dadi da kamshi, sannan ta soya doyar bayan ta gama miyar. Sai ta dafa ruwan tea me kayan kamshi ta saka a sabon tea flask ta hada komai akan babban tray ta kaisu falon ta jera a tsakiya. Turare ta kunna a cikin bunner sannan ta koma dakin ta shiga wanka, ta shirya cikin wani hadadden lace mint green da touches din golden, cikin kayan lefen ta ne yayi kyau sosai kuma kana gani kasan me tsada ne. A hankali ta tura kofar dakin taga ya sake dunkulewa waje daya, sai ta dauki wayarta a saman mirror ta fito ta sake jawo masa kofar a nutse. Karatun al'qur'an me girma ta kunna a wayar ta ajiye a saman kujera ta koma kitchen din ta dan sake gyara shi ta jawo kofar sai taji ana knocking a kofar shigowa part din, wajen kofar taje tace

"Waye?"

"Mune." Amira tace suna rik'e da warmers din abinci da tea flask,bud'e musu tayi tana fad'ad'a fara'ar fuskar ta, suka gaishe ta a tare suna satar kallon ta dan ba karamin kyau tayi ba, kayan sun zauna das a jikinta sannan daurin yayi mata kyau sosai.

"Sannun ku, Amira da Ihsan ko?"

Dadi ne ya kamasu jin ta fadi sunan su, suka amsa mata da eh, tace su zauna,

"Mami tace karmu zauna wai yayi safiya, zamu dawo anjima breakfast tace a kawo muku. "

" Toh shikenan,mun gode ku gaishe su "

" Sai anjima. " Suka juya ta rufe kofar tazo ta bud'e warmers din taga farfesu ne da chips sai kunun gyada, plate ta dauko ta zuba ta ajiye sauran a wajen da ta jera kayan abinci ya zauna taci sosai, ta gama tasha tea dan bata fiya son kunun gyada ba ita, ta wanke kwanukan ta dawo ta zauna kenan sai gashi ya fito. Idansa fes akanta ya sakar mata murmushi yana nufo ta, tashi tayi tsaye ya karaso ya bud'e hannun sa ya rungume ta.

"Good morning Baby!"

"Ina kwana!?"

"Lafiya lou, kin tashi lafiya?"

"Lafiya lou."

" Masha Allah, shine kika gudu kika bar ni ko?"

" Bana jin bacci ne."

" Sai kika zo kina bawa kanki wahala maimakon ki huta ko?"

" Ba wata wahala fa."

" Ba wani."

Yace yana zama a wajen kayan abincin

" Wanne ne yaran chan suka kawo wane ne kika girka da hannun ki?"

" Dama kaji zuwan su?"

" Ina jin su, na ganki ma kina zuba loma baki jira ni ba."

" Laaaa..." Tayi saurin rufe fuska da tafin hannun ta, yayi dariya ya bud'e flasks din yace ta zauna, ta zauna ta zuba masa doyar da sauce din kamar yasan shine wanda tayi, yaci sosai da ruwan bunu hakan yayi mata dadi sosai, ya gama ta tattare wajen ta gyara shi kuma ya shiga wanka, sai da ya tsokane ta akan tazo ta tayashi ta gudu kitchen ya dinga dariya shi kadai yana wankan har ya kammala ya fito ya shirya irin shirin da yake weekends yace tazo su shiga cikin gidan. Mayafi ta yafa madaidaci ya fito suka nufi chan part din iyayen tana karewa ko ina kallo.
Tarba ta musamman ta samu a wajensu, musamman Mami da take ta nan nan da ita, duk sai taji tsoron da take ji ya kau, taji wani gwarin guiwa na zuwar mata, har falon Baba Alhajin Mami ta kaita ta gaishe shi, ya dinga saka mata albarka, sai da MD suka shigo tare da Abuyan sannan suka koma cikin gidan ta zauna dasu Amira a falon suna kallon wani film me kyau.
Sai wajen twelve sannan yayi mata text yace ta dawo, ta tashi tace ma Mami din zata tafi, sai tace mata ta shiga wajen mom ta sameta a daki, ta shiga ta gaishe ta again sannan tace zata tafi ne dama, dadi taji sosai ta saka Ihsan tace ta rakata. Sosai Asma'un ta kwanta mata ta gamsu da ita a matsayin matar Abdallan nata.
Chapter 56 · 0% Book details