← Book details Rayuwar Mace Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 66

Sashe 32

Rayuwar Mace Complete Hausa Novel · about 8 min read

" An gama ranka ya dade." Ya mike yayi hanyar barin part din, murmushi kawai Abdallah yayi, yana kara jin kaunar dan uwan nasa, hadin kansu shi yafi masa komai, hakan kuma ya samo asali ne tun a farkon zamantakewar iyayen su, in da har baka iya banbance dan waye wannan a cikin su, shi kansa yasan yafi sabawa da Mami fiye da Mum da ta kasance mahaifiyar sa, haka ma MD yafi sabawa da Mum, tsiran haihuwar sa da ta Mudan shekara daya ce shiyasa suka taso tamkar tagwaye. Koman su daya ne tunda suka tashi har kawo yanzu da suka girma hakan bata chanja ba, banbancin su kawai shine shi Abdallah bashi da hayaniya da magana kamar Mudan din.

_ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_

_ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_ 2

_BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_

_KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._

_WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU  IN SHA ALLAH

_KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_

_SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_🥰

_BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍

_MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_🥰

_HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️

_NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍

***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_*

_BIYAR : DUBU DAYA (1k)_
_HUDU: 700_
_UKU: 500_
_BIYU: 400_
_DAYA: 300_

_AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE  MU TA: _

*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*

*KATIN MTN*👇👇

09166221261

______________________

ZAFAFA BIYAR

VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA)

VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA.

TWO PAGES DAILY
INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE.

*_TEAM ZAFAFABIYAR_*

*RM*

     *25*

***Dawowa yayi dauke da tray ya ajiye masa a tsakiyar falon, mikewa yayi bayan ya gama karanta bayanin dake kan screen din system din yazo ya zauna ya tankwashe kafarsa, gefen sa MD ya zauna shima bayan ya dauko system din ya dawo da ita kasan, suka cigaba da hira yana breakfast shi kuma yana shigar da wasu informations.

"Kunyi waya da Baba kuwa?" Abdallah yace bayan ya gama ya ture tray din gefe, a ka'idar sa baya taba magana idan yana cin abinci, sai ya kammala. "

"Eh munyi."

"Owk ya maganar dawowar sa? Ko zaka je ka same shi a chan?"

"Anya? Kamar sun ma gama zuwa jibi yace zai dawo."

"Owk,. Allah ya dawo dashi lafiya, akwai aikin da ya bani nima, kafin ya tafi duk da dai naci karfin sa, sauran rarrabawa kawai."

"Aikin zakkar ne?"

"Eh wallahi, shi yake sani kwanciya late kwana biyu,amma an gama fitar da komai kawai yanzu rabawar ne.."

"Ah masha ALLAH, gaskiya Baba yana kokarin sauke hakkin Allah, kasan fa yanzu yan kasuwa da masu kudi basu cika fitar da zakka ba, ko a fitar a bada ita ta yadda ba zata taba wani amfanar wanda aka bawa ba."

" Sosai, Allah ya bamu ikon sauke nauyin dake wuyan mu."

" Amin na Ma'u."

" Ka fara kenan ko?"

" Daga magana?"

" Tashi mu shiga wajen ciki, Allah yasa bakayi barin zance ka fadi maganar nan ba."

"Wacce, ta I love you din nan?"

"Kana da katuwar matsala, kaga ka sameni a ciki kawai."

"Allah ban fad'a ba, na dai ji inason na fad'a da na shiga dazu, na daure dai saboda abinda kayi min alkawari."

"Kaji dashi, idan ma ka fada kanka kayi ma ai."

"Ba zan ma fad'a ba." Yace yana zura takalmi a kafarsa, tuni har Abdallan ya kai kofa , yayi sauri suka jera har ciki, Ihsan da Amira na zaune kowacce da waya suna dannawa, suna ganin su kowacce ta nutsu, suka gaishe da Abdallah tunda dama shine be shigo ba, ya amsa yana hararar hannun Ihsan da yake ita ke facing dinta,

"Baku da aiki sai danne dannen waya ko?"

Girgiza kai tayi, ya wuce be sake cewa komai ba, dariya ce ta so kwacewa Ihsan din tuno abinda taji jiya, ta kalli Amira tayi mata signal da ido,dan dama tun a jiyan ta fesa mata labarin, kama bakin ta tayi da hannu tayi mata alamar wallahi babu ruwan ta,

"Gulmar me kuke? Munafuki."MD yace yana duban kowaccen su

"Wallahi Allah Ya Mudan babu ruwa na."

"Nima babu ruwana."

"Sai kun fad'a min, kallon me.kike mata? Ke kuma me kike cewa ba ruwanki?"

"Dama ihsan ce..."

"Amana fa nace miki."

"Toh ni ai ba ruwana, ni bance ki fad'a min ba kika fada min,."

" Wai me? Me ta fad'a miki."

Rage muryarta tayi sosai kasa k'asa tace

" Jiya ne kuna magana da Ya Abuya a balcony ashe isy taji shine tazo ta fadawa Mami da Mum nima ta fad'a min."

" Shikenan kun ja min, yanzu zai dauka ni na fad'a.". Da sauri yayi hanyar dakin Mami da Abdallan ya shiga, ya tarar da shi a zaune kusa da mamin tana masa magana, wani kallo da yayi masa tun kafin ya karaso ciki ya bashi tabbacin maganar Mami take masa, Ashe neman shi da take tayi tun dazu kenan, ji yayi tana cewa

" Naji dadi sosai wallahi, Allah ya tabbatar mana da alkhairi ya sa ayi damu."

Kasa amsawa yayi da Amin saboda kunyar da ta lullube shi, ya dinga jerawa MD aiken harara, da sauri ya karaso ciki yana kama bakin sa

"Wallahi Allah bani na fad'a ba, Mami dan Allah ni na fad'a miki?"

"Toh idan kaine sai me? Dama ai dole a fad'a mana tunda abin farin ciki ne."

"Eh amma.dai ai ba wajena kika ji ba? Waccan me bakin akun ce ta fad'a miki ko?"

"Wa?" Tace tana nuna kamar bata san wa yake nufi ba, dan tasan zasu iya takurawa Ihsan akan haka, shiyasa ba ma zata ce ita bace ta fad'a, tsakanin su chan su karata da boye boyen su

"Kai ka fada min dazu da ka shigo ko ka manta, anan su ma yaran sukaji."

"Mami..." Ya fad'a saman gadon ta yana hade hannayen sa waje guda

"Dan Allah ki taimaka min kice bani na fad'a ba."

"Waye ya fad'a toh?"

Ganin da gaske ba zata fad'a ba, ya saka shi bin bayan Abdallan suka shiga dakin Mum suka sake fitowa a tare, su Ihsan basa falon sun tashi, daga gani Mami ce tace su tashi kafin su fito. Zai kama su ne ko zuwa anjima ne, ya ayyana a ransa.
Wayar sa ya dauko kawai daga shashen nasu ya bar gidan ba tare da ya saurari MD din ba, dan so yake ya fara aikin da Baban ya saka shi yau yaga abinda zai iya yi kafin yammacin ranar.

***Wayar sa ya kunna sanda suka isa zariya, ya dubo number wani friend dinsa da sukayi school tare ya yi dialing, yana dagawa yace masa gashi a zariya yana neman masauki shi da madam ne, baya kuma son sauka a hotel, kasancewar yasan yayi aure ya saka be kawo komai ba, ya fad'a masa in da zasu hadu, ya katse wayar yana sauka daga kan main road din,

"Ina zaka kai ni?"

"Auren mu zan nemi wanda zai gyara mana shi, I can't do without you, nasan kuma kema haka ne, so ki kwantar da hankalin ki, duk abubuwan da nayi miki a baya marasa kyau, zan gyara komai,."

"Bana son ka, bana kaunar me son ka, idan kaga dama ka tafi dani daga nan har karshen duniya ba zan taba auren ka ba."

"Ai ba ke dama xaki aure ni ba, ni ne zan aure ki, za kuma ki gani, my baby love." Ya kai hannun sa ya shafi gefen fuskarta, ta matsa da sauri tana hararar sa, ji take kamar ta samu wani abu ta daba masa, ta daina ganin shi kwata-kwata saboda tsanar da take masa.
In da zasu hadu da abokin nasa suka je, ya zo suka gaisa ya shigo motar, suka tafi, bata ce musu uffan ba, tana jin abokin yana tsokanar ta da amarya, tayi masa banza sai Adam din ne yace ai bata jin dadi ne, abokin yace Allah ya kara sauki.
Wani dan madaidaicin gida ya kaisu, ya fito yana basu umarnin su fito

"Ina fatan dai ba zaku takura anan ba, part biyu ne,madam dita ce a daya, dayan kuma na brother dina ne da zai yi aure, an gama komai."

" Ya isa, just kwana biyu zamuyi, wani aike ne ya kawo ni da na gama zamu wuce."

" Owk, muje toh."

" Muje." Ya bud'e mata kofar, ta fito tana masa mugun kallo amma ko a jikinsa, ya sakata a gaba har ciki, dan idan ma tace zatayi masa gardama bata kuma san in da zai kai ta ba.

_ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_

_ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_ 2

_BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_

_KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._

_WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU  IN SHA ALLAH

_KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_

_SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_🥰

_BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍

_MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_🥰

_HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️

_NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍

***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_*
Chapter 32 · 0% Book details