Sashe 25
Rayuwar Mace Complete Hausa Novel · about 6 min read
Daga haka ta tisa yar ta a gaba suka tafi, dan ko tasha giyar wake ba zata bar ta ba, akan me? Sai yanzu za'a nuna ana son ta bayan abu ya kwabe musu, hakan ma da suka zo ya wadatar ba sai kuma an nemi wani abun ba. Ita kanta Asma'un ba son zaman take ba, dan dai kawai ba zata saka baki a maganar su Umman ba, shiyasa umman na cewa su tafi tayi saurin bin ta.
Suna kokarin barin cikin asibitin Adam na sako kansa, su suna kasa shi yana mota basu ko lura dashi ba, shi dai ya gansu dan har wani burki ya taka da ya kusan janyowa na bayan shi ya taba shi, allah dai ya kiyaye, gefe ya ja ya matsa masa yazo ya wuce shi kuma ya juya motar yabi bayan su, be san dalilin bin nasu ba, kawai ya samu kansa da zuciyar sa da bukatar hakan, har sun tare napep zasu shiga ya karaso wajen, Asma'u ce ta fara ganin sa gaban ta yayi mummunar faduwa, tayi saurin fadawa napep din kafin ma umma ta gama yi masa kwantancen in da zai kaisu.
"Ai kin tsaya a gama daidaitawa ko Asma'u!?" Umma tace tana shigowa itama, sai a lokacin ta ga Adam din, yana tsaye a gefen su zaune cikin motar sa, be fito ba kuma be tafi ba, dauke kai Umman tayi tamkar bata san shi ba, tacewa me napep din
"Muje."
Bari wajen su kayi ba tare da sun nuna sun ganshi ba, ya daki sitiyarin motar yana jan tsaki, me ya hau kansa ne da har ya aikata haka? Juya motar yayi zuwa cikin asibitin yana me jin haushin kansa. Duk yadda yaso ya yakice tunanin ta ya gaza, duk in da ya juya ita yake gani sanda ta kalle shi da zata shiga napep din, hirar ta yaji su Mama nayi da Nadeeya, ya kasa kunne yana saurara har da murmushin sa, sai bayan yayi ya kuma hade rai yana me jin haushin kansa, tashi yayi ya bar dakin ya fito waje ko zai daina jin abinda yake ji a ransa.
Yana fita Fido na zuwa ita da kawarta, reception ta tsaya sai da ta gano dakin da Maman take tazo dubuta, ita kanta Maman da ta ganta sai da ta ji gaban ta ya fadi, wani irin kwarjini da tsoron yarinyar take ji wanda ta rasa na menene, kamar mutuniyar arziki take gaida Hajiyan, shiru ne ya biyo bayan gaisuwar, har sai da Faiza ta dan zungure ta sannan tace
"Mama dama batun ciki ne."
"Naam?" Mama tace a kideme
Nadeeya da ranta ya baci tace
"Wai baku ga halin da take ciki bane, haba mana."
"Abun da zai sakata warkewa ne ai, dan nasan shine dalilin kwanciyar tata, ciki dai na zubar dashi..."
"Kin zubar?"
"Eh, an ma da sharadi, dole Adam ya aure ni, magana tuni tana hannun hukuma idan ya amince sai na janye idan be amince ba shikenan."
"Ya ma amince, ya amince ma."
Murmushi tayi, suka kalli juna ita da Faiza, sai suka mike a tare suka ajiye ledar hannun su
"Ga kayan dubiya, Allah ya kara sauki."
"Angode, ku gaida gida."
Suna fita Nadeeya ta dubi Maman
"Mama tsoron ta kike?"
"Sosai nadeeya, wallahi ko kallon fuskar ta bana son yi, idan Adam be aure ta ba zan taba samun nutsuwa ba. "
" Innalillah wa inna ilaihi rajiun, Anya mama haka yarinyar nan ta barki? Karuwa ce fa, kalli zubin ta amma a haka zaki sa Adam ya aureta? "
" Shi din menene Nadiya? Sanda yake kula ta duk be san hakan zata faru ba, ko kina ganin shi tunda namiji ne yaci banza, abinda ake nuna musu kenan, baka san da wadda zaka hadu ba, ba kuma kasan sharrin ta ba, tunda har ya kasa zama da mutuniyar kirki irin Asma'u bani da zabi, sai ya auri daidai dashi su karata, dama ai mazinaci sai mazinaciya irin sa. "
Shiru Nadeeya tayi cike da tausayin Maman da Adam din, dan tasan Maman na fadar haka ne dan bata da hanyar da zata hana yarinyar, amma babu wanda zai so auren irin Fido duk lalacewar nasa dan!
***Duk yadda yaso abun ya bar kansa,ya kasa tsawon sati biyu kenan tunda ya ganta ya gaza sukuni,duk abinda yake yi ita yake gani. Gaba daya ya fita hayyacin sa, shiyasa ma ki maganar Fido baya tunawa, tun bayan dawowar mama daga asibiti da tayi masa maganar auren Fido din yaki amincewa, ta nuna bacin ranta sosai akai kawai yace suyi duk abinda suke ganin daidai, be sake sanin abinda ake ciki ba, dan ko yar fitar nan ya daina, yana gida a ko da yaushe tamkar bashi ba. Ba zai iya jurewa ba, duk yadda yaso ya yakice tunanin ya gaza har ya soma fita hayyacin sa, shiryawa yayi ya nufi gidan Abban kawai duk ma abinda zai faru ya faru.
Umma na tsakar gida da yake yamma ce su Abeed sun zo sai dare Baban su zai zo ya dauke su, fitowa Asma'u tayi ta zauna a gefen Umman tana jawo Abeed din jikin ta
"Abba zai barni naje gidan su Abeed umma?"
"Zai iya barin ki, kinsan yanzu lallaba ki yake, ki kirashi dan yace yau zai yi dare, ko ki bari idan ya dawo gobe sai ki shirya kije."
"Ai ban ma hada kayan ba, idan ya dawo din sai na tambaye shi."
"Hakan ma yayi, kwana nawa zaki?"
"Sati daya."
"Kai Asma'u har sati?"
Dariya ta saka
"Umma ai ba yawa satin fa, dan ma Abba ba zai bari ba da nayi ko sati biyu ma."
"Lallai, satin ma ki yi addu'a ya barki, kinsan baya son ki matsa nan da chan, da ya shigo yake fara neman ki."
"Tausayi na yake ji ai, ni kuma fa komai ya wuce na manta ma ni wallahi."
"Shi ai yaki mantawa."
Zatayi magana akayi sallama a dan corridor din da yake kafin ka shigo gidan, gaban ta ne yayi mummunar faduwa, ko a mafarki taji muryar shi sai ta firgita bare har taji shi a tsakiyar cikin gidan su, duk da tsoratar da tayi amma bata nuna ba, tana zaune kyem tana cigaba da wasa da hannun Abeed, umma ce ta amsa tana dan leka kanta, dan bata dau muryar sa, jin an amsa ya saka shi shigowa kai tsaye, ta mike ta kama hannun Abeed din suka shige ciki.
"Adamu ne, shigo mana."
Umma tace ba tare da ta nuna masa komai ba, babu kunya ya zo ya zauna a gefen tabarmar da Asma'un ta tashi, ya gaida Umman ta amsa ba yabo babu fallasa. Shiru ya biyo baya har sai da Umman tace
"Hajiya ce ta aiko ka?"
"A ah, wajen Asma'u nazo."
Kallon ashe baka da hankali Umma tayi masa tace
" Wajen Asma'u kuma!? Ko dai kayi batan kai ne? "
" A'ah, tambayar ta nazo yi ne. "
" Lallai Adam, yanzu kai dan Allah har kana da bakin yiwa Asma'u magana? Toh wai ba ma wannan ba, baka ji kunyar zuwa kace wajen ta kazo ba? Ban ce kwata kwata ba zaka zo gidan nan ba, amma ba wai wajen Asma'u ba, ko dan kaga mun kyale ka bamu kaika wajen hukuma ba. "
Ransa ne ya baci, sai a lokacin yaga wautar sa ta zuwa, umma kuwa ta wanke shi tas dan dama rashin samun dama ne, yana ranta dan da wani ne bare wallahi sai sun yi shari'a dashi, kasa mikewa yayi har sai da ta gama yi masa tatas, tace kuma kar ya sake zuwa da sunan wajen Asma'u dan aure ma zatayi ta samu miji, wannan maganar ta karshe ita tafi firgita shi, har ya dauki hanyar gida baya gane abinda yake masa dadi.
_RM_
*19/20*
_Hafsat Rano_