← Book details Rayuwar Mace Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 66

Sashe 52

Rayuwar Mace Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya juya ya shige ciki, tsaye tayi a wajen cike da tunanin abinda ya kamata tayi, shiru be fito tayi tunanin da gaske yake kawai sai ta bishi, ta same shi a kwance a gadon be kuma saka rigar ba.

"Please dan Allah."

"Um um, bacci nake ji, zo mu kwanta, inaso naji heartbeat din matata. "

" Dan Allah. "

Lumshe idon sa yayi yana tariyo abinda ya faru yan mintunan da suka wuce, murmushi ne ya subuce masa, ta kalli yadda yake murmushin sai ta samu kanta da murmusawa itama, tana tsaye sai da ya gama yangar sa sannan ya tashi yana mika mata rigar

"Samun kafin na chanja shawara."

Da sauri ta karba ta shiga saka masa, duk da ya kere ta nesa ba kusa ba a tsayi, amma babu yadda ta iya dan ba zata zo ta kwana ba saboda kunyar da zataji. Tana gama saka masa ya rungume ta yana jujjjuya su a dakin.
Da k'yar ta samu ya dauki car key dinsa suka fito, suka tafi. Ya tsaya ya siya mata dinner da wasu tarkacen kayan sannan ya wuce da ita gida. A kofar gidan ma sai da tayi da gaske sannan ya kyale ta, ya fito ya raka ta har cikin harabar gidan nasu, ya kama hannun ta ya saka mata kudi masu yawa

"Kudin kunshi da kitso, MD zai kawo drinks da safe, da sauran abubuwan da za'a bukata, da daddare zanzo mu wuce. "

" Allah ya kaimu, thank you so much, jazakallah bhi khair Allah ya kara budi "

Murmushi yayi mata yana me jin dadin addu'ar, ya amsa da Amin k'asa k'asa. Har ta juya ta soma tafiya ya tsayar da ita, ta tsaya tana juyowa, ya taho suka hadu, ya rankwafo zuwa daidai saitin kunnenta

"You are very sweet." Ya furta in a romantic voice and way, da sauri tayi ciki kamar wadda aka tunkuda, ya kyalkyale da dariya ya juya ya bar gidan yana shafa kansa, yana jin sa kamar wanda yake yawo a saman gajimare!

RM
   41

***Duk suna tsakar gidan wannan karon ma, dan duk a gida zasu kwana saboda shirye shiryen ranar goben, kamar wadda aka sarawa kafa haka taji, amma sai taga kamar basu fuskanci komai ba, sannu da dawowa suke mata dukka sai Ya Hadiza da ta dan harareta cikin sigar wasa tace

"Kika barni ina ta jira."

Bud'e baki tayi zatayi magana ta katse ta Kuma

"Jeki ajiye kayan kizo dan Allah, gwara a kitse kan kafin gobe dan ba lallai na samu damar yi miki ba."

"Wai kitso zakuyi Ya Hadiza!!?" Rauda tace tana waro ido

"Ba gwara a kitse shi ba, da ta barshi haka." Umma ta sako baki tana daga gefe tana duba sauran kayayyakin da aka siyo

"Allah gwara a bar mata, ai yafi yasha mai tayi parking din sa wallahi."

"Kufa kun fiya shiririta, kitson be fi umma?"

"Allah Umma gwara dai ta barshi haka daga baya sai tayi kitson."

" Ke Asma'u me kike so?"

" Zanyi daga baya umma." Tace da sauri dan tabbas a yadda kan nata ya koma sai duk sun harbo jirginta, shiyasa da Rauda tayi maganar taji kamar taje ta rungume ta saboda tsabar dadi.

" Ai shikenan, sai a barshi a hakan ai."

Daki ta mike ta shige da sauri, ta sauke ajiyar zuciya tana sakin murmushi, da ba dan Rauda ba da ta sha kunya yau, dan har lokacin a jike gashin yake da ruwa gashi kuma duk sun san da maganar gyaran kan zasu ce Ina ta samo ruwa akanta, toilet ta shiga da sauri bayan ta dauko hand-dryer dinta a cikin kayanta da Hidaya ta hade mata su waje daya, ta shiga da ita ciki dama rechargeable ce ta shiga busar da kan. Sai da ta gama sannan Hidaya ta shigo dakin ta ajiye abu ta fita, sauya kayan jikin tayi ta fito wajen su, ta samu sun koma cikin falon saboda wutar da aka kawo, tana zama wayarta tayi kara, Abdallah ne yake kiranta, da sauri ta kashe hasken wayar tana kallon su, sake kira yayi bayan wanchan din ya katse,

"Ki daga mana, ba kiranki ake bane!?

" Wata number ce take ta kirana, idan na daga sai ayi shiru shi yasa bana dagawa kawai."

"Ki sakata black list kawai."

Ya Hadiza tace tana cigaba da hirar da ta dauko

Text message ya turo mata jin bata daga ba

"Baby.. How are you feeling? Hope babu wata matsala ko? Take care of yourself.. xoxo"

Murmushi tayi kawai ta sake kifa wayar aka cigaaba da hirar da suka kusan kai dayan dare sunayi bayan sun gama kallon lefen Asma'un a karo na kusan uku, sai an gama sai a sake tuno kaza sai a sake budewa cike da yabawa, Rauda tuni ta sulale tayi bacci sai ita da Ya Hadiza, Ya Amina, Batul da Hidaya. Ita ta fara tashi dan gaba daya kawai daurewa take amma gabobin ta ciwo suke mata sosai, wanka ma take so ta fara yi kafin ta kwanta amma kuma bata jin zata iya, so kawai take ta ajiye hakarkarin ta a k'asa ko zata ji saukin jikin nata. Tana kwanciya bacci me nauyi ya kwashe ta, cike da mafarkin Abdallah. Babu wanda yayi mata maganar motar ta, yadda suke shirya dama sai da safe idan an tashi, bayan an yi breakfast sai kuma ayi breaking mata news din, Abbati ne gaba a tsara hakan umma dai bata ce komai ba a lokacin sai murmushi kawai da take cike da jin dadin yadda rayuwar Asma'un take sauyawa zuwa wani bigire na daban.
Da safe ta tashi da karfin jiki dana zuciya, ranta fes kamar an mata bushara da gidan aljanna, har yan uwan umman sun iso saboda tayin aikin abincin da za'a yi tun duku-duku sai karin ma'aikata uku da aka karo, tana nade akan gado tana kallon duk abinda yake wakana Hidaya ta kawo musu fanke da Lipton suka ci, sannan ta dauki waya ta masa reply din text din da yayi mata jiya da daddare.

"I'm fine, how about you?" Ta rubuta masa ta ajiye ta mike ta fita.
Yana tsaye kusa da Baba Alhaji da yake nuna masa wata takarda a harabar gidan text dinta ya shigo, cigaba da abinda suke yayi har sai da Baban ya sallame shi bayan ya saka hannu a takardun sannan ya wuce zuwa chan gate ya samu bencin da gateman dinsu yake zama ya zauna ya zaro wayar ya shiga message yayi mata reply yana daga kansa sama, sanyayyiyar iskar safiyar na busawa cike da wani yanayi da be taba riskar irin sa ba

"Alhamdulillah, thank for yesterday, kin biya ni har da kari ma, Allah yayi miki albarka ya barmu tare har abadah."

Sosai yayi relaxing a wajen har rana ta soma isowa in da yake, ya cigaba da shan ta kafin ta soma dukan fuskar sa, sannan ya tashi ya koma ciki ya hau shiryawa, dan so yake ya gama komai yau da wuri ya dawo gida, ana magriba zai je ya dauko matar sa ba zai jira ba, ba kuma wani zai wakilta dauko masa ita ba, shi kadai ya isa.

Dawowa dakin tayi da zumudin ganin reply dinsa, ta dauka tana karantawa tana murmushi, sai kuma ta lunshe idon ta, ta zauna tana sake maimaita text din tana tuno tsadaddun kalaman sa na jiya da duk in da ta motsa sune suke mata amsa kuwwa a kanta, bata san haka soyayya take da dadi ba sai a wannan lokacin da ta hadu da gwarzo tamkar Abdallan, wanda ita kadai ta san wannan bangaren nasa, idan ka ganshi a haka zaka rantse ko hannu aka saka masa a baki ba zai ciza ba.

***Sosai hidima ta kankama kan kace menene gidan ya kacame sai kaya kaya kawai ke tashi, tayi wanka ta saka wani lace me kyau golden da yellow, wanda ya haska ta sosai ta fito amayar ta sosai ba kamar bikin Adam ba, tun da ta fito tsakar gida mutane sukayi mata cha, kinyi kyau kinyi kyau. Murmushi kawai take har ta isa wajen da kanwar Umma Anty sadiya take a zaune, ta durkusa a gabanta tana mata magana sai ga Hajiya mama sun shigo da ahalin ta, wani irin sak tayi ganin Asma'un kamar wadda aka sauya ta da wata ta daban, bata jin dadin jikinta tunda Adam ya dawo gida dan ko lekowa be yi ba tun bayan dawowar sa bare yazo ya gaishe ta, sau biyu tana shiga gidan bata ma ganin sa sai Fido tace mata yana sama baya son hayaniya, abun yana damun ta har ciwo tayi amma haka ta hakura, kamar ba zata fito yau din ba ma amma ta daure sai kuma tazo taga Asma'un sai duk taji damuwar ta, ta karu da tunanin damar da ta kwace musu ita da Adam din, Allah yayi musu gamdagatar amma suka wofintar da ita har ta kubce musu. Kowa sai da ya lura a wajen da yadda take kallon Asma'un kamar ranar ta soma ganin ta, ita kanta Asma'un sai data tsargu da kallon ta shige dakin umma da saurin ta sai a sannan Hajiya Maman ta dawo hayyacin ta, ta hau wayancewa cike da borin kunya. Daki umma tabi Asma'un tace mata ta dinga addu'a saboda baki, ta amsa da toh umman ta fita ita kuma ta zauna a wajen da sauran sisters din umma suka cigaba da zaman su a dakin har aka zo lokacin walimar, dakin ta, ta koma ta sauya kaya zuwa wasu daban suka fita zuwa compound din inda aka gabatar da walimar, aka ci abinci aka sha abun sha sannan Anty Hauwa ta sake tunatar da mutane akan rayuwar aure da kuma hukunce hukuncen da suke kan mace wanda ya zama wajibi ta sauke nauyin domin samun rahmar ubangiji, daga nan ne kuma Abbati ya shigo mata da motar wanda ta shiga tsananin mamaki, Itace motar da ta nuna a ranar, duk da ya nuna mata da gaske yake amma bata ji a ranta cewa ta chanchanci mallakar hadaddiyar motar ba, har kukan dadi sai da tayi dan farin.
Chapter 52 · 0% Book details