← Book details Rayuwar Mace Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 66

Sashe 34

Rayuwar Mace Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Toh. " Ta saka mata number ta, tace ta kira idan ta koma zata gani sai tayi saving, ta kira kuwa a take, sannan ta shiga daki ta hado mata abubuwa a leda ta kawo mata. Shiru su Adam din basu dawo ba, Umar ya sake kiranta yace ta fito kawai, tayi wa Ayshan sallama ta rakota har waje, ta gaida su Abban, motar Asma'u ta shiga, ta sake mata sallama tana tsaye suka bar layin, ta girgiza kanta tana juyawa dan ta koma ciki, ta hango motar su tana shigowa layin amma ba ta in da su Asma'un suka bi ba, ciki ta koma suka shigo, ta fito tana musu sannu da zuwa, wara ido Adam yake ko zai ganta amma ko motsin ta be ji ba, kasa hakuri yayi yace

"Please Madam kice ta fito na ganta, tunda muka zo ake punishing dina."

"Owk." Tace sannan tace

"Dear dan zo kaji." Bin ta yayi ciki, ta fad'a masa komai da komai da Asma'u ta fad'a mata, dama yayi tunanin haka ganin a yadda suka zo garin da kuma yadda Adam din ya damu sosai, gwara da akayi haka ma, komawa yayi wajen Adam din ya tarar dashi yana kaiwa da komowa irin ta wanda yake cikin damuwa sosai,

"Ba zata zo ba?" Yace da sauri

"A ah, she's gone. "

" How? Ta yaya? " Ya fad'a a kidime

" Kayi hakuri kawai, kasan dai babu aure bayan saki uku, ina ganin be kamata kayi kokarin halatta abinda yake haramun ba. "

" Ba wannan nake son ji ba, ka fada min tana ina, ina taje? "

Yayi maganar cikin daga murya da karaji

" Tare da kai muka fita, bayan mun fita aka zo aka tafi da ita, she told my wife everything. "

" Damn it! " Ya daki bangon falon

" Da na sani ban yi trusting naku ba, amma zan dawo..." Ya juya cikin sassarfa ya bar falon, ya rasa ina zai kama, ta ina zai fara, ya samu dama me kyau amma yayi wasa da ita, me yasa ma ya tafi ya barta, bayan yasan tana da damar da zatayi waya ta kira gida. Rasa ina tsoma ransa yaji dadi yayi, ya kasa tuka motar ma, baya tunanin zai iya hawa titin nan balle ya kai kansa kano a daren, dole zai jira gari ya waye saboda lafiyar sa, sai da ya bari kafa ta fara daukewa a garin ya samu wani gidan mai da baya amfani, direbobin mota ne yawanci suke kwana a ciki parking yayi a ciki, ya sauke glass din motar ya kwanta a baya, sauro kuwa yace da wa Allah ya hada mu, ya dinga gasa masa cizo babu tausayawa, abinka da farar fata kafin safiya ya fice daga hayyacin sa, babu wanka babu komai ya dauko hanya.

Hafsat Rano -RM
           27

***Lokacin da suka dauko hanya Umma ta kira Abba, ya daga ya sanar mata da gasu nan tare da Asma'un, Alhamdulillah, ta furta sannan ta kashe tana sanar musu da abinda Abban yace, har lokacin Hajiya Mama na gidan, tana jin an ce sun taho ta tashi, tayi musu sallama ta tafi,dan dama zaman jiran da take kenan, Nadeeya ta kirata ta fad'a mata zuwan kawayen Fido gidan, shiyasa take so taje taga me yake faruwa duk da dai an ce sun tafi. Duk suma sai umma tace su tafi gidajen su sun dawo gobe, Ya Hadiza ce kawai ta rage suka zauna da Umman suna dakon zuwan su Abban, sai dare sosai suka dawo, Asma'u ta rungume umman tana fashewa da kuka, ita ma umman kukan ta saka, amma ba kamar Asma'un da duk dauriyar da take jin tana da ita a gaban Adam din ta neme ta a yanzu ta rasa, ta gaji sosai da komai dama rayuwar baki daya, hakuri duk sukayi ta bata, Abba yayi mata nasiha me ratsa jiki, hakan ya sanyaya mata jiki ya sakata yin shiru sai jan ajiyar zuciya take, su kansu sun san tabbas a yanzu ta kai karshe. Da safe ta tashi da missed calls din sa, da text message bayan kiran da yayi mata da ya Hadiza ta fad'a mata da zata bata wayar, ji take kamar bata bukatar sake shigar da kanta wata matsalar a yanzu, amma kuma ba zata iya yi masa wulakanci ba. Wanka ta fara yi, tana shiryawa umma ta shigo dauke da abincin ta, ta ajiye tana kallon ta, shigowar ta uku kenan tana tarar da Asma'un na bacci, tausayin yar tasu suke ji dan sai da Abba yaga da gaske ba a lokacin zata tashi ba ya hskura ya fita, dan da so yayi ya dan kara bata baki kafin ya fitan.

"Umma..."

"Naam Asma'u, kin tashi kenan."

"Eh na tashi, ina kwana!?"

"Lafiya lou, Abban yana ta jiranki, yaki fita da yaga baki tashi ba sai ya hakura suka fita da Abbati."

" Allah sarki Abba, bacci nayi tayi wallahi."

" Ai gwara ki huta sosai, ga abinci nan kici, saura ki tsaya janjani kici sosai."

",Toh umma." Tace tana sauke abincin kasa, ta zauna kenan wayar ta, tayi kara, ta kalli umma kafin ta kalli wayar, shine yake sake kira.

" Shine ko? Ki daga kar yayi tunanin wani abu, jiya ya kira ma."

"Toh." Tace tana dagawa, sai umman ta fita ta ja mata kofar a ranta tana addu'ar dacewar Asma'un

Daga nan tana iya jiyo ajiyar zuciyar da ya sauke, dan shi kadai ya san yanayin da ya shiga na rashin samun ta a waya jiya gaba daya, badan aikin da ya fita ya tsaida shi ba da komai dare sai yazo, shiyasa yau yana tashi ko shiryawa be ba, ya hau kiran ta, be sameta ba yayi mata text message shima shiru shine yanzu har ya zauna a office dinsa yaji sai ya kuma gwada kiran ko zata dauka,

"Ina kwana?" Tayi breaking shirun da yayi ta hanyar gaishe shi, shi kansa be san shirun me yayi ba bayan abinda yayi ta fata kenan yaji ta daga, amma kuma ya lura kamar so yake ta sake magana yaji muryarta tar ya sake tabbatr da ita din ce ta daga a yanzu

"Me bawan Allah yayi aka wahalar da zuciya da ruhin sa jiya? Umm?"

"Babu komai, wayar ce bata wajena."

"Baki san yadda na damu ba wallahi, anyways, hope komai lafiya?"

"Alhamdulillah."

"Ok masha Allah, nazo na ganki?"

"Na'am?"

"Eh? Are you free nazo yanzu, inason ganinki. "

" Owk sai kazo. " Ta samu kanta da hana shi, murmushi yayi wanda har sai da ta jiyo sautin sa, ya ajiye wayar bayan yace mata gashi nan, mikewa yayi ya cire rigar suit dinsa dake rataye a saman kujerar da yake zaune, ya saka yana balle botir din jiki MD ya turo kofar ya shigo rik'e da wasu manyan files, wani kallo yayi masa ganin yana tattare wayoyin sa daga kan table yace

" Don't tell me fita zakayi."

" Fita zan, akwai wani abu ne? "

" Sosai, sai ka duba kayan nan, akwai wajen da zakayi signing kafin su saki kayan. "

" Gaskiya sauri nake, ba zan iya ba, ajiye kawai sai na dawo. "

Dora files din MD yayi a saman table din yana bin Abdallah da kalllo, hanyar fita yayi ya bishi da sauri yana jerawa dashi

"Meeting zaka?"

"A ah."

"Ina toh?"

"Ina ruwan ka? Dole sai kaji duk in da zani?"

"Ahhhh! Yau kuma?"

"Eh." Ya kauda kansa barin kallon MD din dan zai iya ranfoshi nan da nan, cikin lift suka shiga MD nata kokarin sai ya ji in da zaije amma yaki fad'a masa, ya bishi har parking space yana masa magiya, ganin da gaske ba zai fda masa ba, sai kawai ya bud'e motar ya shiga, ya zauna a gefen sa

"Aikuwa sai dai muje tare, nima dama inaso naga Aunt din tamu, taga dan kanin ta itama."

"Mudan wai me yasa kake takura min ne?"

"Toh ai kaine, sai kayi ta boye-boye, yanzu dai muje kawai ko ina zaka sai naji."

" Oya." Ya jefa masa car key din yana balle murfin motar ya fito, sannan ya zuro kansa yana hararar sa

" Kasan ni ba driver ka bane ko? Fito toh."

Ba musu ya fito, ya zagayo wajen driver ya shiga, shi kuma Abdallah ya koma wajen me zaman banza, yaja motar.

Fita tayi ta samu umma a daki, ta dan yi jim kafin ta fad'a ma umma wai zaizo, tashi umman tayi da kanta ta sake tabbatar da falon Abba a gyara yake, sannan tace

" Kin fada masa kina gida? Kar ya tafi chan."

Girgiza kai tayi,

" Kira shi toh, ba dadi sai yaje chan sannan ya taho nan."

Wayar ta dauko, ba zata iya kiran sa ba, dan haka ta tura masa text message na address din gidan, lokacin sun dauke hanyar gidan Ya Hadizan yaga text din, ya saka MD juyawa suka dawo baya, yana bashi direction din gidan har suka karasa, a waje MD ya faka yana kallon unguwar, yana kuma son ya tsokani Abdallah amma kuma sai sun fito, wayar ya ciro ya kirata, gabanta ya fadi ganin kiran sa ,ta mike tana daidaita nutsuwar ta sannan ta daga, toh tace kawai ta ajiye wayar ta fito, umma na ganin ta tasan sun zo, tace taje ta shigar dashi ta kofar gaban gidan. Fitowa tayi ta bud'e kofar gidan ta dan leko, yana zaune cikin mota yaga sanda ta leko, be cewa MD komai ba kawai ya fito, ganin haka ya saka shima fitowa yana ware ido yayi gulma, gaba kawai Abdallan yayi ya bishi a baya, tana tsaye jikin gate din kamshin turaren su me dadi ya riga su isowa, ta yi saurin kallon wajen dan ta tunanin ta basu ganta ba, shiyasa ma daga leko ta koma tana tunanin wanda zata saka yayi musu magana sai gasu, a kunyace ta gaishe su, tayi ciki tace su shigo,

"Nan ma ya isa, kinji?"

Tsayawa tayi, ta dawo duk kunya ta cikata, ta tsaya daga jikin gate din, ya shigo ciki MD na take masa baya

"Auntyn mu." MD uban azarbabi yace yana wuce Abdallan ya shigo ciki sosai
Chapter 34 · 0% Book details