← Book details Rayuwar Mace Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 66

Sashe 31

Rayuwar Mace Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Owk tam." Tace ta juya ita kuma ta tashi, ta sakko daga gadon ta shiga bayi ta kuskure bakin ta, ta wanko fuskarta, ta fito dama tayi sallah tun asuba, sai kawai ta zura hijab ta fito, biyo ta Abeedan tayi, suka je tace waye.? Jin muryarta, ya saka shi jin wani sanyi a ransa, ya tabbata idan yace shine toh ba zata bud'e ba, sake maimaita waye tayi, yayi kokari sosai wajen saita muryar sa, yace Abbati ne. Ji tayi kamar muryar abbatin kamar kuma ba tashi ba, kai tsaye ta zare lock din ba tare da tunanin komai ba, cike da hanzari ya tamki hannun ta, ta turje idon ta na fitowa waje

" Menene haka?"

Da sauri Abeeda ta juya ciki tana kwala kiran Mummy, ya sa karfi ya jata zuwa motar tana kwacewa, sai dai karfin su ba daya ba, tura ta yayi ciki ya rufe da key sannan ya zagaya ya bud'e bangaren sa ya shiga ya bar layin.  Daidai lokacin Ya Hadiza da Abban su Abeed suka fito da mugun gudu ya Hadiza ko dankwali babu akanta, amma kafin suzo har ya bar layin, rik'e Abeeda tayi tana fashewa da kuka

"Waye ya tafi da ita? Waye?"

"Uncle Adam ne."

"Na shiga uku, me zan cewa Abba, Adam dama bashi da hankalin ban sani ba?"

"Calm down, tunda ma shine ai da sauki, muje ciki ki shirya bari na kira Abba, dole ya dawo da ita tunda mu ai ba mahaukata bane kamar sa, idan yaki sai a saka shari'ah a ciki, tunda be san addini ba."

  Hankali a tashe ta koma ciki ta chanja shigarta dan ba ma zata iya wanka ba, tana jin shi suna magana da Abban, a nutse suke maganar da dukkan alamu ba kamar ita da ta rude ba. Wayar Asma'un ta dauko a daki da handbag dinta suka tafi gidan su, suna zuwa suka tarar da Umma hankalin ta  a tashe, ranta yayi masifar baci, shi kansa Abban dan dai namiji ne amma kana kallon fuskar sa zaka ga yanayin sa ya chanja, be kira Hajiya Mama ba, tunda ya fuskanci kamar har yanzu tana goye da bayan dan ta, kuma ma dai baya bukatar wata magana kawai Adam ya dawo masa da yar sa. Dama mijin Ya Hadizan yake jira yana zuwa suka fita a mota tare, sai police station dan shine kawai mafita yanzu a garesu, sai da suka je kofar shigar kuma sai Abban ya kasa sauka daga motar, ya dinga jin kamar hakan tona asirin family din su ne, kamar kuma be kyautawa Yayar sa ba, tunda duk tsiya dai Adam din ma nasa ne, cewa yayi su juya zuwa gidan Hajiya Maman kawai, Abban su Abeed ya jinjina zumunci irin na Abban wanda baa samun sa a wannan zamanin sai an tona. Shi kadai ya fita ya shiga gidan yace mijn ya Hadizan ya jirashi, ya shiga kansa tsaye ya same ta a zaune a falo ta rafka tagumi

"Sannu da zuwa." Tace masa tana mikewa, maimakon ya zauna sai ya tsaya daga kofar shigowar

"Adam yaje har gidan Ali ya dauki Asma'u, bansan me yake nufi ba, ban kuma san ina zai kaita ba, amma inaso ya dawo min da 'yata kafin nan da awa daya, idan ba haka ba zan nemi hukuma ta shigo ciki."

"Na shiga uku, Adam din? Chan ya tafi dama? Wannan wanne irin abu ne dan Allah, na shiga uku."

Ta hau tafa hannu tana salallami, sallama Abba yayi mata ya fita yana jin duk babu dadi yadda abubuwan suka kasance. Wayar ta, ta jawo da sauri ta shiga kiran layin Adam din amma be daga ba, ta dinga jera masa kiran ba kakkautawa.

***Gudu ya dinga shararawa har sai da ya kusa kure titin, be san ina zashi ba,be shiryawa hakan ba, a lokacin da ya ganta kawai tunanin yazo masa. Duk magiya da rokon da take masa yayi kamar be ji ba, shi dai tunda yanzu suna tare burin sa kawai ya samu in da zasu, ya samu wanda zai tabbatar masa akwai aure har yanzu a tsakanin su, sannan ya umarce shi akan ya daura musu aure a take a wajen! Jin kiran da ake masa babu kakkautawa ya saka shi daukar wayar ya kashe ta ma baki daya, ya juya akalar motar zuwa hanyar barin garin baki daya.

***Hankalin Fido yaki kwanciya akan kiran da Hajiyar tayi mata kuma ta kira bata daga ba kuma bata biyo kiran ba, a daren da zata tafi gidan Faiza ta hanata tace ta bari dai da safe, aikuwa wajen goma na safe taga shiryawa, Faizan ko tashi batayi ba, ta dauki hanyar gidan bayan ta tsaya tayi wa Hajiyan siyayyar kayan fruits.
  Yanayin Hajiya Mama ya chanja lokacin da ta ganta ta shigo, ta kalli hannun ta kafin ta aro jarumtar yi mata maraba, zama tayi tana gaida hajiyan

"Dama naga kira ne jiya, shine nazo naji ko lafiya?"

"Eh wallahi, lafiya lou bansan na kira ba ma wallahi, jiyan nan ina neman wata number ashe ke nake kira."

"Ayya."

Tace tana karewa falon kallo, ta jima bata ga Adam din ba, bata kuma da bukatar ganin sa har sai ranar da ta shigo gidan sa, a yanzu tasan zai iya cewa zai nada mata duka, shiyasa take mugun takatsantsan dashi.

"Na tura wa chan kannen Baban Adam din address din da kika bani, nasan yanzu sun je ko zasu je ma, ban dai ji daga gare su ba, yau nake shirin ji."

"Allah sarki." Tace tana sinne kai, dadi na cikata saura kiris burin ta ya cika, dan jim ta zauna ganin kamar Hajiyar bata cikin nutsuwar ta, ya sakata mikewa

"Zan koma Maama,dama zuwa nayi na duba ko lafiya."

"Lafiya lou, nagode sosai ki gaida gida."

"Yauwa."

Tana fita ta zauna dabas, zafi goma da ishirin, kira ne ya shigo wayarta, tayi saurin wawurar wayar a tunanin ta Adam ne, sai taga wani kawun su Adam din ne, kawu murtala. Dagawa tayi

"Barka da safiya Asabe."

"Barka dai kawu, ya mutanen gida."

"Lafiya lou, dama batun Adamu ne, akan yarinyar da aka ce muje mu nema masa aure, toh Alhamdulillah, an je kuma mun samu iyayenta da maganar sun yi murna da farin ciki, sun kuma amince sun bashi ita dan a take ma akayi komai muka bada sadaki aka daura aure..."

"Na'am?"

"An daura aure, sai bayan an daura ne ma wani baffanta yake shaida mana ai rabon su da ita yau shekara guda kenan tun wani zuwa da tayi ta gaishe su, tunda har ta turo a nemi auren ta toh su dama haka suke so, shiyasa ma baa bata lokaci ba."

"Tirkashi!" Ta furta

"Sauran bayanin zanzo gidan anjima, wannan dai na fad'a miki ne saboda girman maganar ba zan iya jira sai nazo din ba, jiya muka je kuma dare yayi mana a hanya ga rashin network me kyau da tun a jiyan ma zan kira."

" Shikenan Kawu, sai kazo."

" Yawwa,Allah ya sanya alkhair ya basu zaman lafiya."

Kasa amsawa tayi da Amin, taji kamar  kalmar bata chanchanci a fadeta a irin wannan auren na Adam ba, jin tayi shiru sai kawai ya kashe, su yanzu sun zama yan kallo a sha'anin Hajiya Maman da yaranta, duk abinda tace dasu suyi shi kawai sukeyi basa wani duba ya dace ko be dace ba.

***Dukkan su sun hadu a gidan suna zazzaune, Rauda har da kuka da aka gaya mata ta taho a lokacin, Hidaya ma da sauran yan gidan duk sun zo, wayar Asma'un da Ya Hadiza ta dauko aka kira, umma ta kalle ta ita ma ta kalle ta sannan ta kalli wayar, ABDALLAH ta ga anyi saving, ta gane waye amma kuma bata san me zata ce masa ba idan an daga. Katsewa tayi aka kuma sake kira

"Ki daga kice bata kusa."

"Toh." Tace tana dagawa

"Hello, ina kwana."

"Lafiya lou." Ya amsa cike da tantamar wadda ta daga

"Yayarta ce, Asma'un bata kusa."

"Oh... Ina kwana?" Ya gaishe ta

"Lafiya lou, zaa fad'a mata idan ta zo."

" Owk nagode Aunty."

Ya katse yana cike da jin kunya. Tashi yayi daga gadon dan yau ya more baccin sa sosai, yana tashi ita ta fara fado masa a rai, shine ya kirata yaji lafiyar ta, toilet ya nufa yana rage kayan dake jikin sa, ya bud'e drawer a dan corridor din da zai kaika wajen da akayi a farkon toilet din me dauke da wardrobe din kayan sa, laundry basket, mirror , shoe rag da sink a gefe, towel ya ciro ya daura a kugunsa ya tsaya a gaban mirror din yana taba sajen fuskar sa, yana bukatar aski dan ya dan tara gashin sosai, maimakon ya shiga toilet din sai ya jona clipper ya tsaya a gaban mirror din yayi gyaran fuska, ya gama ya mayar da komai wajen sa sannan ya fad'a cikin toilet din in da toilet din da wajen wankan yake. A tsanake yayi wankan ya fito ya gyara jikinsa ya saka kananan kaya riga da wandon, ya zura slippers ya fito falon su, MD ya tarar a saman table yana duba abu a system gefen sa black tea ne, zama yayi a kujerar gefen sa.

"Good morning Sir." Ya dan sauke kansa kasa alamun girmamawa

Dariya MD ya saka yana ture system din

"Waye Sir din? Ai wallahi ban isa ba.".

" Sir Mudan mana, MD K'AREFA GROUP OF COMPANIES."

" Toh ai kai kuma kai ne kankat din Oga, kai na a k'asa."

" Munafuki motar nan na zuwa zaka koma raina ni." Ya buge masa kafada

" Ai ban isa ba wallahi, Oga a kawo maka tea din ne?"

"Eh a kawo, a hado da wani abun me dan nauyi."
Chapter 31 · 0% Book details