← Book details Rayuwar Mace Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 66

Sashe 37

Rayuwar Mace Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ba komai." Ya sake maimaitawa sannan suka fita daga gidan, MD be ce komai ba, har ya bud'e masa motar ya shiga shi kuma ya zagaya ya zauna a wajen MD din zai kunna motar, rik'e hannun sa MD yayi, yana duban sa

"Are you ready to marry  da?" Ya tambaye shi yana tsire shi da ido

"I'm more than ready ma, anything?"

"Ina wayata?" Ya lalubi aljihun sa, sai ya dauke ta a saman kafarsa

"Bani two mint ina zuwa."

Ya balle murfin motar ya fita

"Karka koma ciki pls."

"Waya zan yi." Yace masa yana matsawa gefe, Baba Alhaji ya kira lokacin sun fito compound din gidan shi da Alhaji Muktar da kanin sa Alhaji Tukur, dama duk yammaci indai Baba Alhajin na gida anan suke zama har sai bayan sallar isha'i sannan suke tafiya shi kuma ya shiga ciki, kiran MD ya katse musu hirar da suka akan kasuwancin su,

"Ya akayi Mudan?" Yace bayan ya daga

"Dama akan maganar yarinyar da Abuya yake neman aure ce,idan kayi mana izini a daura auren a yau?"

"Saurin me ake Mudan? Akwai matsala ne? Kuma shi mahaifin nata zai yarda ya baku auren ta daga zuwan ku?"

"In Sha Allah babu matsala, dama Baban nata yace a turo ayi magana."

"Yanzu me kake so ayi kenan Mudan? Ina shi Abuyan? "

"Yana mota, amincewar ka muke nema, idan ka amince sai muga abinda ya kamata ayi."

"Na amince, ka tura min address din gidan yanzu zamu zo mu samu mahaifin nata, ka jiramu kafin muzo."

" Allah ya kara girma, mun gode Allah ya saka da alkhairi."

" Amin. Ina jiran ka."

" Zama me kama ku ba, danku ya dauko aure, yanzu haka so suke wai nayi musu izini su nemi auren, shine nace zamu zo sai ayi magana da mahaifin ta muje matsayar sa, su kuma muji dalilin gaggawar, bamu san me Allah ya boye ba, harkar aure tana bani mamaki sosai kar ka sauwala rabo ya kashe ka."

" Haka ne, idan har yaron ka ko yarinyar ka ya nuna maka aure yake so , toh kayi masa shine mafi aala, balantana Abdallah ba yaro bane, shi da kansa ya isa ya kai ya nema wa kansa aure kuma a bashi, musamman saboda nagartar sa."

" Haka ne." Duk suka hada baki wajen fad'a, suka tashi driver Alhaji Muktar ya dauke su suka nufi unguwar su Asma'un.

Lekowa MD yayi maimakon ya shigo matar, fuskar sa tar kamar an masa bushara da gidan aljanna, kamar bashi ne cikin bacin rai a dazun ba, hannu Abdallah ya daga masa alamar ya akayi? Ya kwashe da dariya yana jingina da jikin motar, horn ya danna masa da karfi, ya sake lekowa yana mika hannu ya zare key din motar

"Mene haka wai? Na tafiya zamuyi ba?"

"Eh akwai sakon da zan karba."

"Bani key din ka taho toh, ko so kake ya fito ya kara kama ka da rigima shi da baya gudun abin kunya?"

"Wuce nan wallahi, dan a cikin gida ne na kyale shi Amma wallahi anan sai na daka shi kuma na sa an rufe min shi wallahi, yanzu ma ai ban hakura ba, zamu gauraya dashi bayan na nuna masa karfin iko na."

Tabe baki Abdallah yayi, cike da kosawa da maganar MD din,

" Sai kayi tayi ai."

" Zan kuwa yi amma sai na fara aurar da kai tukunna."

" Silly boy." Ya zaro wayar sa ya hau dannawa yana share MD din da shirmen sa, Waka yaji yana rarewa, ya girgiza kai yana ayyana abinda ya saka shi farin ciki haka nan da nan, yana zaune cikin motar rabin kafarsa na waje ya zuro su yana rik'e da wayarsa kansa a kasa yana dannawa yaji shigowar mota layi, be dago ba ya cigaba da abinda yake sai yaji an faka a daidai saitin sa, hakan ya saka shi dagowa , mamakin ganin wadanda be yi tunanin gani ba ya cika shi, ya kalli MD da yayi wajen su ya dawo da ganin sa kofar gidan su Asma'un, kansa ne ya kulle ya ma kasa tunanin me yake shirin faruwa ko me yake faruwa, har lokacin yana zaune a motar yana bin su da kallo, Abba ne ya fito daga gidan yana saba babbar rigar sa, cike da girmamawa da mutuntawa suka gaisa sannan ya jasu zuwa cikin gidan, wani kallo yayi ma MD da yake kada kai kamar kadangare yana fatan komai ya kasance kamar yadda ya shirya. Motar Adam na nan kuma be fito daga gidan ba, ya tabbata yana ciki kuma hakan ya sake masa dadi, ya dinga zayaye a tsakanin wajen, fitowa Abdallah yayi ya damko shi yana bata fuskarsa

"What have you done? Me ka aikata?"

"Wait and see, aure zan maka."

"Aure? Ban gane ba."

"Nima ban gane ba."

"Allah sa ka fada min, kai ka kirasu ko? Me kace musu?"

"Eh ni na kira, kana tunanin idan ni ne zan iya barin abinda nake so tare da wanchan mahaukacin? Wallahi ko me za'a yi sai na aure ta na nuna masa iyakar sa, tunda shi jaki ne mahaukaci, kuma ko kusa da ita naga yazo walalhi sai na saka an tsinke min kafarsa daya wallahi."

" Oh innalillah, yanzu da wanne idon zan kalle su? Kamar fa yadda ka nuna I'm in desperate kenan ko? Na shiga uku. "

"Toh gauro irinka dama ai dole a same shi da matsuwa man,. "

" Baka da hankali wallahi. " Yace yana juya masa baya, be san ina zai dauki abinda yake ji ya ajiye ba, farin ciki, tarin fargaba da wani abu kamar tsoro tsoro, a zahiri a nutsen sa yake kamar babu wani abu amma kuma a badini shi kadai ya san luguden da ake a girkinsa, kiran sallar magriba ne ya fito dasu, kasancewar akwai masallaci a daidai saitin gidan, nan suka nufa suna hira cike da raha kamar sun jima da sanin junan su, hakan ya dan kwantar masa da hankali har ya samu kwarin guiwar daura alwala suka bi bayan su.
Ana idar da sallah Abba dama yayi wa limamin magana tun kafin a tayar, dan haka ana idarwa ya bada sanarwar daurin auren Asma'un, kallon kallon Abdallah ya dinga yi yana bin mutanen cikin masallaci da kallo, fit ya tashi ya fice MD ya bi bayan sa da sauri, akan kunnen su akayi siga da komai, Alhaji Muktar ya bada sadaki naira dubu dari biyu, anan take aka daura auren Abdallah da Asma'u. Rungume shi MD yayi yana furta Alhamdulillah, shi kuwa gogan sai ya rasa in da zai saka kansa, ya dinga jujjuayashi yana mamakin yadda al'amarin ya kasance. Wajen su, su Baba Alhaji suka nufo, ya mika ma Abdallah hannu alamun su gaisa, a kunyace ya mika masa ya rik'e shi cikin nasa yana murmushi

"Congratulations my son. In sha Allah kayi sa'ar mata."

"Baba..." Ya fad'a yana shiga jikinsa ya rungume shi, bayan sa ya bubbuga cike da zolaya yace

"Abuyan MD ya girma."

Dariya suka saka a tare su Alhaji Muktar suka karaso, suka bashi hannu suma dukka sannan suka yi masa Allah sanya alkhair, wani iri yake jin sa kamar wanda iska zata dauke tayi sama dashi

"Mahaifin ta ya roki a basu sati biyu kafin ta tare, ganin yanayin yadda auren ya kasance."

"Ba komai, mutum na gari me cike da karamci, naji dadin yabon da ya samu dashi da yarinyar, shiyasa ma ban yi k'asa a guiwa ba, wajen ganin Abdallah na ya mallake ta, ina fatan ta zamar masa sanyin idaniya kamar yadda mahaifiyar sa ta zamar min."

"In sha Allah."

Suka amsa a tare, MD sai rawar jiki yake kamar mazari, shine nan shine chan kamar ya taka rawa, har mota suka rasa su Baba Alhajjn Abba yazo suka sake sallama da yiwa juna murna da fatan alkairi, suna tafiya Hajiya Mama na zuwa ita da Nadeeya a gigice, Nadeeya ce take tukin, Hajiyan ta kasa nutsuwa tunda Abban ya kirata yace zai daura ma Asma'u aure, bata san nan Adam din ya taho ba, yake dai gida ya samu Fido ya nada mata mugun duka sannan yayi ficewar sa, Ashe nan ya taho tana ta kiransa a waya sai Nadeeya ce tazo ta duba Fido din ta bata magani, yanzu haka sun baro ta tare da kawarta Faiza dan har targade yayi mata.
Duk abinda ake da maganar auren har da daura auren Adam be sani ba sani ba dan bacci yake sosai a dakin Abbati saboda cewa yayi ba zai tafi ba, kuma duk alamu sun nuna baya hayyacin sa shiyasa Abba yace su kaishi dakin Abbatin kafin ya dawo hayyacin nasa, ita kanta uwar gayyar Asma'u bata san wainar da ake toyawa ba, tana kan abun sallah tana tilawar alkur'ani me girma, umma ma Umar ne ya shigo bayan sun zo yace mata manyan baki ne suka zo wajen Abban sai kuma sanarwar da taji daga masallaci duk da loudspeaker din bata da kara sosai kwana biyu matsala take basu dan haka ba kowa ne zai ji ba.
A gigice Adam din ya farka kasancewar ba kwanciya bace ta dadi abinda yasha ne yaci karfin sa ya saka shi baccin dole, Hajiya Mama ya gani a kansa tana sharar hawaye tausayin sa sosai takeji musamman da taji cewa an daura auren Asma'un, tasan zai yi hauka sosai, gaba daya ya zama wani iri,

"Mah... Zasu barni naga Asma'u? Dan Allah kice tayi hakuri wallahi ba zan sake bata mata rai ba."

"Adam me kake so ka maida kanka? Kana da hankali kuwa?"

"Baki kawai zaki saka wallahi zasuyi hakuri, kar su bata wannan da yazo, ni nafi shi chanchanta."

"Ka tashi mu tafi gida, wannan ba ita ce rayuwar ka ba?"

"Idan na tafi zaki kawo ta? Zaki basu hakuri su sake bani aurenta?"

Gida mishi kai tayi tana kauda kanta gefe, ya mike da k'yar yana tangadi kamar zai fadi, ta rik'e shi Amma sai ya zame hannun sa yayi gaba ta bishi da sauri, duk su Abba suna tsaye a tsakar gidan suka fito, ya isa gaban Abban ya durkusa

"Abba kayi hakuri."

"Ba komai Adam, tashi."
Chapter 37 · 0% Book details