← Book details Rayuwar Mace Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 66

Sashe 59

Rayuwar Mace Complete Hausa Novel · about 8 min read

"In sha Allah." Yace har lokacin be cikata ba, sai da ya dau mintuna yana jinta a jikin sa sossi sannan ya cikata ya dauki wayarsa da ta soma burarin kira ya shigo, yana dauka ta katse yabi bayan kiran sukayi magana sannan ya zauna gaban system din ya shiga duba clips din daya bayan daya.
   Falo ta koma da tunanin abinda zata bashi dan da dukkan alamu be saka komai a cikin sa ba, tasan yana son bakin shayi sai tayi masa toasting bread slice hudu ta hado masa da tea din ta turo kofar hannun ta dauke da tray din bakin ta da sallama.
  Ajiye su tayi a gefen da system din take tayi, ta zuba masa ta matso ta dan duka ta mika masa yana fidda tururi, be yi musu ba ya mika hànnun sa ya dora akan nata hannun dake rik'e da handle din cup din ya kai bakin sa yana sha, dan yana bukatar samun energy din da zai yi amfani dashi gobe. Sai da ya shanye sannan ya cika mata hannu ta bashi bread din yaci guda daya yace mata ya koshi dan shi ba gwanin bread bane.
   Bayan ta maida kayan kitchen tazo ta shirya shirin kwanciya bacci dan har kusan sha biyu da rabi, cigaba yayi da abinda yake dan ko zai kwanan zaune yau sai yayi kokarin ganin komai, gashi da yawa amma haka ya daure kansa na cigaba da sara masa kamar zai balle daga gangar jikinsa haka yake ji.
   Wajen biyu na dare ya gama komai amma be samu wani clue ba, sai ma sake zama clueless da yayi kansa ya sake daurewa tamau, alwala ya shiga toilet ya dauro yazo ya shinfida sallaya zai tada sallah yaga ta mike, tace ya jirata, zama yayi taje tayo alwalar taxo sukeyi nafila suka roki Allah SWA sannan suka kwanta wajejen uku da rabi, asubah nayi ya mike ya fice zuwa masallaci dan yana son sanin yadda Baba Alhaji ya kwana akan batun da kuma abinda ya kamata ayi a yau din da wuri. Shi ya fara zuwa masallacin kawai sai yayi raka'atanil fajr kafin lokacin ya karasa shiga.

Manage

_ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_

_ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

_BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_

_KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._

_WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU  IN SHA ALLAH

_KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_

_SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_🥰

_BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍

_MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_🥰

_HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️

_NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍

***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_*

_BIYAR : DUBU DAYA (1k)_
_HUDU: 700_
_UKU: 500_
_BIYU: 400_
_DAYA: 300_

_AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE  MU TA: _

*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*

*KATIN MTN*👇👇

09166221261

______________________

ZAFAFA BIYAR

VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA)

VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA.

TWO PAGES DAILY
INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE.

*_TEAM ZAFAFABIYAR_*

RM
   51

***Tare suka fita da Baba Alhaji ya motar MD din, suka tsaya suka dauki wani abokin Baban wanda ya sakance babba ne a yan sanda, Abuyan ne yake tuka motar su kuma suna baya suna maida magana akan abinda ya faru

"Mu basu dama suyi binciken su, na tabbata tunda bashi da hannu kwana biyu yayi yawa sun gane komai."

"Kowa haka yake cewa, na kira Babagana tanko ma jiya a daren yace zai tuntunbi case din yaji yana hannun wa, daga baya ya kirani yace wani yaro Mansul shine yake leading investigation din, tun daga jos suka yi tracking number din har Kano, suna ta rasa signal idan ya kashe wayar sai a jiyan ne suka samu signal din a daidai lokacin da shi Mudan din ya dauki hanyar kt din."

"Kuma duk abinda suke neman sun sameshi a motar?"

"Eh kwarai, jaka ce wai cike da bullet a cewar wadanda suka dan riski abun dan tsaida hanyar sukayi suka hana kowa wucewa sai da yazo sukayi ram dashi, anan dai mutane suka ga abunda yake faruwa. '

"Kuma dama kasan akwai case na ana shigar da makamai batsari, ina kyautata zaton tunanin da zasuyi kenan."

"Duk zai iya yiwuwa, shiyasa ni duk jikina yayi sanyi wallahi, bana son case irin wannan musamman a wannan lokacin da kidnappers da yan bindiga sukayi yawa, case ne babba kawai sai dai muyi fatan Allah ya kubutar dashi."

" Fatan kenan, muje muga CP muji yadda za'a yi, kafin kuma muji daga garesu su chan DSS office din. "

"Allah ya jishshemu alkhairi. "

" Amin ya Allah. "

Abuya na jin su be ce komai a maganar ba, yayi wa kansa alkawarin sai ya riga su samun duk wani information da ya kamata ya samu akai. A gidan CP ya ajiye su, yace zai je ya dawo, ya wuce office in da yake son sake duba komai, ya kalli duk clip din da security agents dinsa suka tura masa na CCTV cameras din wajen, amma kuma dole wani abun is missing, achan ya har motar tasa tun safe bayan ya dauki abu a ciki be sake bi ta kanta ba, kuma da suka tashi tafiya gida ma a motar MD din suka tafi, dole a wannan tsakanin duk abinda zai faru ma ya faru. Da sauri maigadi ya taso ya bud'e masa kofa, ya tsaya a daidai kan gate din bayan ya dan shigar da ita kad'an, da hannu ya yafito shi alamun yaxo, ya rugo yazo ya russuna ya sake gaishe shi sannan yace

"Tambayar ka zanyi, kayi tunani sosai a jiya waye da waye suke shigo gidan nan?"

"Ranka ya dade masu shigowa suna da yawa gaskiya."

"Babu wani da ya nuna maka yana nema na kai tsaye ko ni ko MD?"

"Eh toh!" Yace yana son tunawa

"Tabbas akwai wani matashi, tabbas yazo a jiya ya kuma ce kai yake nema dan yafi sati yana zaryar zuwa baka nan, sai jiyan da yazo nace ya samu sakatariyar ka sai ya samu ganin ka, be kuma jima a ciki ba ya fito ya tafi har ma yake ce min ai zai sake dawowa, yayi min dan hasafi nayi godiya ya tafi."

" Zaka gane shi idan ka ganshi!?"

" Eh kwarai, ai mun yi doguwar magana dashi, tabbas kuwa zai gane shi."

" Ok!." Ya tura kan motar sa zuwa ciki, ya bar maigaidn da tunani da tararradin abinda yake faruwa, tun safe yake ganin yan sanda na kaiwa da komowa a cikin company nasu, yanzu haka akwai wasu ma a ciki suna ta sintiri da alama ma baa bud'e ofisoshin ba kwata kwata. Dole akwai matsala kenan farin yaron jiyan nan yana da alaka da abinda yake faruwa, lallai akwai matsala dan baya so ya rasa aikinsa,akwai mutuntawa tsakanin sa da yaran shiyasa baya tunanin idan ya bar wajen zai iya samun kamar sa, tsurewa yayi jikinsa ya hau rawa, hankalin sa ya tashi ya rasa ina zai saka kansa.
Yana shiga suna isowa su uku yan sanda ne na farin kaya, suka nuna masa I'd card sannan suka ce suna neman sa zasuyi masa wasu tambayoyi, babu musu ya bud'e musu office dinsa suka shiga suka zauna, suka fara jefa masa tambayoyi wanda duk akan motar da ta kasance mallakin sa ce, iyakar abinda ya sani ya sanar musu, suka dau bayanan nasa cikin kwarewa, sannan suke ce zasu tafi, ya bukaci sanin halin da MD yake ciki amma suka ce duk wannan zai biyo bayan bincike ne, ba dan sun yi saurin samun labarin abinda ma yake faruwa ba, da ba lallai su san halin da ake ciki zuwa yanzu ba, amma sun masa alkawarin a yau duk wani binciken su dangane da shi MD din zai gama, kuma duk yadda ake ciki zasu neme su, suna monitoring wayarsa ne dan samu wasu informations din.
Bayan sun tashi zasu tafi ne babban cikin su ya kalle shi ya mika masa hannu sukayi musabiha kafin yace

"Kasan akwai hidden camera a cikin motar nan?"

"Akwai?" Yace yana kallon sa da sauri

"Tabbas akwai, kuma mun samu abinda muke nema, dan haka don't worry, in sha Allah zaku ji komai. "

" Ok in sha Allah, sai mun jiku. "

Fita sukayi sai ya zauna da sauri ya kunna computer ya shiga google yayi searching motar da available features dinta, sabuwar order ce be kuma wani bincike ta sosai ba, mamakin sa ne ya karu ganin akwai hidden camera a ciki daga baya kasan wajen driver, sai wata daga saman bot ta cikin motar.

" Allah Ameen! "

Yace cike da kwarin guiwar komai zai zo da sauki kenan in sha Allah.

***Tun safe Adam yake kasa kunne yaji labarin accident din Abuya amma kuma shiru, har duba Facebook yayi ko zai gani amma babu komai, ya cigaba da bibiyar abun ganin har wajen sha biyu be samu wani labari ba sai ya gwada kiran G-boy yaji yadda ake ciki amma sai ya samu wayarsa a kashe, abinda ya dan daure masa kai kenan, jiya ya tabbatar masa yayi abinda ya saka shi kuma indai har Abdallah ya hau motar to tabbas sunan sa sorry. Tashi yayi yana fama zagaye a falon, Fido ce ta fito daga kitchen ta kalle shi ganin kamar hankalin sa a tashe yake yasa ta magantuwa dan bata son ta bada kafar da Adam din zai subuce mata ko kuma ya dawo hayyacin sa ya nemi uwarsa.

"Lafiya Man?" Tace tana shafa jikinsa,
Chapter 59 · 0% Book details