← Book details Rayuwar Mace Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 66

Sashe 30

Rayuwar Mace Complete Hausa Novel · about 8 min read

***Hannun sa rik'e a cikin na Baba Alhaji suka karaso wajen motar, ya bud'e masa ya shiga yana jaddada masa abinda suka tattauna, murmushi ne kwance a fuskar sa har zuwa lokacin da motar ta fita daga cikin gidan, juyowa yayi yana kallon agogon dake daure a tsintsiyar hannun sa, ya burza shi yana taba airdrop din dake sakale da kunnen sa,  kiran ta yake so yayi tun dazu, yaji zazzakar muryar ta me sanyi da taushi, sai dai Baba Alhaji be bashi damar hakan ba, dan be bar shi ba tun bayan da ya dawo sai da ya tabbatar da ya sake jaddada masa abubuwan da yake so a aiwatar kafin dawowar sa. Tafiya yake a nutse irin ta jaruman maza masu cike da nutsuwa da haiba, ta daga kiran nasa hade da sallama, bata san shi bane dan be karbi number a wajen ta ba, sai bayan ya tafi ne ya tuna ya kira Abban su Abeed ya tura masa, a time din yaso ya kirata amma kuma shi mutum ne me bin komai a kaida da tsari, baya so ya takura ta musamman da rabuwar su kenan be san ko ta shiga wani uzurin ba, sai kuma yazo ya samu Baba Alhaji ya rike shi gam be barshi ba sai da ya tafi, zai je Abuja yayi kwana biyu akan wasu estates din sa guda biyu da yake son saidawa.
  Sallamar ya amsa cikin bawa kowanne harafi hakkin sa, murmushin tayi me sauti, ta gaida shi ya amsa yana karasawa wata yar kujera ta zauna, sannan ya tambaye ta gida da kowa da kowa, ta amsa masa muryar ta tar babu nuku nuku, kwarin guiwar yaji ya samu sosai, ya gyara zaman sa ya shiga yi mata yan tambayoyi a game da abubuwan da yake son sani a tattare da ita, yadda take bashi amsar yafi masa komai, dan a cikin amsar ya fuskanci nutsuwar ta, wadda ya hanga tun jiya a supermarket din, shagala sosai yayi da hirar, dan sosai yake jin dadin hirar har be san an dau lokaci haka ba. MD ne ya dawo yake ta neman sa ya rasa shi, yaje part dinsa yaje masallaci amma duk baya nan, kuma a gate baa ce masa ya fita ba, motocin sa duk suna nan har wadda ya hau yaje zancen dazu, ya matsu su hadu ya tsokane shi, tunawa da yayi da hanyar garden din dake bayan gidan yayi, ya nufi chan da dan saurin sa yana ayyana samun sa a wajen. Ta baya ya hango shi, shi kadai amma da dukkan alamu waya yake, da sanda ya karaso wajen ya labe daga baya yana jin wayar da yake muryar sa tar kamar bashi ba, sai yaji kamar ma har wani makale muryar yayi, ya ji yana cewa pleaseeee, hadda marairace murya, rik'e bakin sa yayi da yake neman tona masa asiri yayi, ya zaro wayar sa ya danna record, ya kara matsawa kad'an daidai lokacin da yayi mata sallama, bayan ta kashe ya furta

"I love you my asmy, love at first sight!"

Sai ya jingina da kujerar yana lumshe ido, ihun dariyar MD din ta sakashi juyowa da sauri, ya dinga tafa hannu yana zuwa wajen nasa, mur yasha sosai yana mikewa

"Dan sa ido, menene na biyo ni nan din?"

"Ai kai ma kasan wallahi dole na saka maka ido, Abuya ne yau yake waya da mace, who's this lucky girl, gaskiya yau za'a yi ruwa da soyayyen kifi, wai."

"Allah MD bana son abinda kake min, me ka maida ni ne!?

" Agogo mana, ko nace dutse dan ni wallahi Allah na dauka ma baka da lafiya ne, ashe ashe kana ankare. "

"Mtss, kana da matsala wallahi. "

Ya juya zai barshi a wajen

"I love you my Asmy... "

MD ya kwaikwaye shi yana buga kafa, juyowa yayi a kunyace zai kai masa duka ya goce

" Haba ango Ma'u, wuce nan na tsaya, kuma wallahi yau zan fasa maganar nan a babban falo, kowa sai yaji musamman ma Mum, bari kaga."

" Tsaya Dan Allah, kar muyi haka da kai, dan Allah karka min haka. "

Kin tsayawa yayi, ya biyo shi da sauri yana kwala masa kira, sai da suka zo Balcony din da zai shigar dasu main part din sannan ya tsaya, ya karaso da sassarfa

" Zan fasa fad'a amma under one condition. "

" Menene? "

" Sabuwar motar da kayi order inason daya, I ll pay half ka cika min ragowar. "

" Kai! "

" Shikenan bari naje na siyar da jaridar, bari kaga. "

" Na yarda."

" Yes! Thank you big bro, Allah ya kara arziki me albarka, ya raba ka da iyayenmu lafiya ya baka My Asmy dinka. "

Duka ya kai masa ya same shi kuwa, dariya suka saka a tare, ya rike masa kunne ya ja

" Baka ji sam, ka raina ni. "

" Abuya! " Ya fad'a da sigar tsokana

"Ka bata min suna tun daga yarintar, gashi nan hatta Baba ma haka yake fad'a."

"Amma kasan me? Ina son sunan sosai, ina jin dadin duk sanda ka kirani da sunan, yana tuna min old memories din mu na yarinta."

"Abdallah-Abuya."

Suka sake yin dariya, ya rik'e masa hannu suka fasa shiga ciki suka juya zuwa nasu bangaren suna cigaba da tattaunawa kamar kowanne lokaci.

Da gudu Ihsan ta koma ciki tana kwalawa Mami kira, tare suka fito da Mum ta sakasu a tsakiya ta ratayo kafadar su

"Albishirin ku?"

"Goro." Suka ce a tare

"Ya Abuya yayi budurwa."

"Da gaske?"

"Wallahi, yanzu naji suna maganar da Ya Mudan, yana tsokanar sa."

"Wannan maganar danki ce babu ni a ciki."

Mum tace tana zama, Mami kuma ta cigaba da tambayar Ihsan din abinda taji, ta kwashe komai ta fad'a, murna ta hau yi, tace ta dauko mata Jakarta a daki, ta kawo ta ciro ATM din ta,

"Goron albishir, ki je ki siya abayar da kika ce min kina so."

Ihu ta saka ta dane ta,

"Thank you thank Mami na, you are the best, nagode Allah ya kara girma."

"Amin Mamana."

"Kinji abun farin cikin da ya sameni ko?" Tace wa Mum bayan Ihsan din ta fita

"Dan naki ne sha'anin sa sai shi, Allah sa da gaske ne."

"In Sha Allah ma gaske ne, bari nazo na fara shirin shan biki, grand biki da baa taba irin sa ba."

"Allah yasa kar ya baki kunya."

"Bama zai bayar ba."

" Shikenan zamu gani."

Tace cikin nuna halin ko in kula amma a kasan ranta wani dadi ne ya lullube ta, Abdallan ta ya samu matar aure.

_ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_

_ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

_BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_

_KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._

_WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU  IN SHA ALLAH

_KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_

_SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_🥰

_BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍

_MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_🥰

_HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️

_NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍

***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_*

_BIYAR : DUBU DAYA (1k)_
_HUDU: 700_
_UKU: 500_
_BIYU: 400_
_DAYA: 300_

_AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE  MU TA: _

*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*

*KATIN MTN*👇👇

09166221261

______________________

ZAFAFA BIYAR

VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA)

VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA.

TWO PAGES DAILY
INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE.

*_TEAM ZAFAFABIYAR_*

*RM*
    *24*

***
Daren ranar Hajiya Mama bata runtsa ba, tana kan Adam da ya farka ya kuma nemi barcin ya rasa, sai magiya yake mata akan ta taimaka masa, tayi wa Abba magana. Ta rasa abinda yake mata dadi Abban ma da yace zai zo be zo din ba, tasan ba abu bane me sauki a wajen sa ba, musamman shi da aka batawa, amma ya zatayi? Bata da kamar sa kaf duniyar nan, dole dai shine sai sake rufa mata asiri a san abinda za'a yi kafin Adam din ya karasa zaucewa dan taga abun ba na wasa bane. Da safe ya tashi kamar bashi ba, kamar kazar da aka tsoma a cikin ruwan zafi, yayi laushi sosai, sallah Mama ta sakashi ya rama wadda ya rasa ya zauna aka kawo masa tea yasha tace yaje yayi wanka, maimakon ya tafi gidan sa sai ya nufi dakin sa na cikin gidan ya sake kwanciya yana dasa sabon tunani, ya dade be fito ba har Maman ta biyo sahun sa, ta ganshi kwance kamar ruwa, tashi ta saka shi yayi ya shiga wankan, sannan ta fito ta jawo masa kofar, yana wankan tunanin ganin da yayi wa Asma'u da gayen jiyan nan na bijiro masa, ya dinga huci shi kadai da k'yar ya karasa wankan ya fito ya shirya, ya bar gidan ba tare da Maman ta sani ba, ya nufi gidan Ya Hadiza, be duba karfe nawa ba, ya isa gidan ya fito ya hau kwankwasa gate din, weekend din saboda haka babu wanda ma ya tashi a gidan sai yara da su dama sabon tashin makaranta baya barin su baccin safen nan, Abeeda ce taji ana bugu da dan karfi, ta shiga dakin da Asma'u take ta hau tashin ta

"Anty Asma'u ana knocking a gate."

"Waye?"

"Nima ban sani ba, tun dazu ake yi, su Momy kuma basu tashi ba."

"Owk, Ina zuwa. Kar wanda yaje ya bude zanzo."
Chapter 30 · 0% Book details