Sashe 62
Rayuwar Mace Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Oya, muje toh, baya kawai zan taimaka maka, sai ka karasa sauran."
"Ni dukka nake so."
"Toh muje." Tace ganin yana sake jan lokacin, sai da suka je toilet din sannan ta jawo masa kofar ta gudu ta barshi, babu yadda ya iya haka yayi wankan a gurguje ya fito, yayi la'asar ya fita zuwa masallaci don yin magriba. Ana idar da magriba ya dawo ya same ta tayi sallar itama tana warming masa abincin dazun da be ci ba, a plate ta zuba masa kawai ta sako spoon daya ta doro ruwa da glass cup ta kawo masa, tare suka ci abincin its ta dinga bashi a baki kamar baby har sai da ya koshi sannan yace mata zai je wajen MD ya dawo, har ya tashi sai taji ba zata iya hakura bata tambaye shi ba..
" Adam ne ko?"
Tace tana kallonnsa. Tsaye yayi shima yana kallonta be tanka ba, sai da ta sake magana sannan ya dawo ya zauna yace ta zauna itana zasuyi magana.
RM
54-55
***
" Adam ne ko?"
Tace tana kallonnsa. Tsaye yayi shima yana kallonta be tanka ba, sai da ta sake magana sannan ya dawo ya zauna yace ta zauna itama zasuyi magana.
"A yanzu haka Adam yana hannu, kai tsaye ba zamu yanke cewa shi bane sai abinda bincike ya tabbatar, for now ki bar maganar, bana son wani yaji, muga yadda bincike zai kasance ko? Kar kuma ki damu kanki ki saka abin a ranki, komai zai wuce."
"Kinji?"
Daga masa kai tayi, ya tashi ya fita, ta kasa zama kwata kwata, ta dinga zagaye a falon kamar ta daga hannu sama tace wayyo. Tana tsaye a falon suka dawo tare da MD, kunyar sa ta kamata, tayi saurin wucewa daki bayan sun sake gaisawa, shi be ma gane komai ba, dan baya alakanta ta da abinda ya faru, kawai iskancin Adam ne kuma dole sai ya karbi hukuncin sa. Zamu sukayi suna maida zancen yadda abun ya kasance. Kiran Abba ne ya katse maganar tasu, ya daga suka gaisa da Abdallan sannan ya tambaye shi abinda yake son tabbatarwa
"Dan Allah Adam yana da hannu abinda ya faru ne? Tun rana ake neman sa wallahi, wasu mutane wai sunzo har gida sun tafi dashi, kaga mahaifiyar sa a kwance ba lafiya. "
"Eh toh Abba, ni kaina bansan ainihin abinda yake faruwa ba, tunda ba sanar mana da komai sukayi ba, amma dai Adam yana hannun su, wai sun samu video dinsa ta cikin camera dake cikin motar a lokacin da yake ajiye abinda aka samu a motar. "
" Subahanallahi, wallahi bamu sani ba, bamu da masaniya akai, tirkashi, toh dan Allah kuyi hakuri Abdallah, babu da masaniyar komai wallahi. "
" Haba haba, babu komai Abba. "
"Shikenan, nagode. "
Ya kashe wayar, ya kalli Umar ya kalli Abbati, zufa na karyo masa
" Tirkashi, Adam ya saka kansa a matsala, ya zanyi da Yaya Atine ne? "
"Wai shi ake zargin kenan? Labari fa har ya watsu a kafafan sadarwa dan wanda suka ga abinda ya farun a hanyar kt din sun sassaka a shafukan su, lallai Adam ya shiga matsala. "
" Babba ma, wannan wacce irin musiba ce?"
" Yanzu matsalar baa san ya bincike zai kasance ba, idan har aka gano yana da hannu shikenan fa wallahi sai dai a hakura, dan su DSS babu ruwansu. "
" Toh Allah ya takaita wahala, Allah ya rufa asiri. "
" Amin ya Allah. "
" Muje kawai a maida Yayan gida Nadeeya ta kula da ita sosai, ni kuma zan cigaba da bibiyar yadda ake ciki, dole sai munyi hakuri sun kare binciken su kaf."
" Owk toh. "
Gidan suka shiga, umma na zaune gefen Hajiya Maman tana mata sannu, Fadeela ce kawai ta karaso Nadeeya ma na shigowa kafin jikin Maman ya rikice aka sake kiranta a asibiti dole tayi saurin komawa. Tana ganin Abban ya shigo ta yunkura ta tashi da k'yar
" Karami ya ake ciki? An samu Adam? "
" Eh an same shi, kuma in sha Allah komai zaizo da sauki. "
" Su waye suka tafi dashi? Kuma laifin me yayi? "
" Eh toh, duk dai zato ne da hasashe, sun roki mu basu lokaci su kammala binciken su, zasu sansr mana da komai. "
" Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, ni dai ina ganin rayuwa, ya Allah! Dan Allah duk wanda nayi wa laifi ya yafe min, Asma'u ma ta yafe min, watakila hakki ne yake bibiyata da ni da Adam, mun yi kuskure a baya, dan Allah ku yafe mana, ummansu kema dan Allah ki yafe mana. "
" Haba Hajiya, ai ya wuce tuntuni, yanzun ma jarrabawa ce, komai zai wuce in sha Allah. "
" Allah yasa, muje gidan ko za'a zo nema na." Ta tashi da k'yar suka taimaka mata, aka sakata a mota suka nufi gidan. Suna zuwa DSS din na zuwa, sun zo bincike gidan Adam din dan suna zargi akwai wasu makaman a gidan, Abba ne ya same su sukayi magana, sannan ya basu damar shiga gidan suka hau duddubawa, basu ga komai duk iya dubawar da sukayi, daga kayan gidan sai tarkacen su shikenan. Wayar Adam din da ya manta a saman gado ce take ta kara, daya daga cikin DSS din ya matsa ya dauki wayar ya daga wayar
" Hello Adam ne ko?"
" Eh shine." Yace
" Toh dan Allah kayi sauri kazo asibitin murtala, matarka da wata sun yi hatsari anan kan titin shigowa gari."
" Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, gamu nan zuwa in sha Allah."
" Yawwa idan kun karaso a kirani da wannan lambar, kuyi sauri dan Allah."
" Me ya faru?" Abba yace dan yana tare dasu a cikin gidan
" Adam yana da mata ko?"
" Eh yana da mata."
" Toh sun yi accident suna asibitin murtala."
" Subahanallahi."
" Sai muje chan din ko?"
" Toh shikenan, Allah ya takaita wahala."
Motar su suka shiga su kuma Abba Umar yaja su, suka nufi asibitin murtalan bayan ya aiki Abbati ciki ya sanarwa Hajiyan abinda yake faruwa.
***Abinda ya faru bayan su Fido sun gama je kura sun dawo ne a hanyar su ta dawowa sukayi karo da wata mota, hannu daya dama ake bi ganin kamar zasu wuce ne sai tayi kokarin yin overtaking ashe shi ma ya shigo, daga nan ne aka kwashe su akayi asibitin Malam dasu aka tarar suna yajin aiki daga nan aka wuce dasu murtala, Fido ko shurawa batayi ba a take a wajen wuyanta ya karya, ita kuwa Faiza buguwa tayi a cikinta, wayar Fido din aka dauko da k'yar a cikin jakarta, Adam shine last da ta kira suna hanyar be daga ba, kuma tayi saving da Hubby shiyasa aka samu number Adam din aka kira daidai lokacin da suka shigo gidan bincike.
Gaba daya Abba ya rasa me yake masa dadi, abubuwan sun hade baki daya tausayin Hajiya Mama yake yi, ita din uwa ce kuma mace me rauni, yasan tayi kura-kurai a baya amma yayi mata uzurin kasancewar mace, yanzu da abubuwan suka hade mata yake kyautata zaton zata iya samun heart attack ko jinin ta yayi mugun hawan da zata kasa komai. Shiyasa a ko dayaushe ake so mu zama masu tunani da hangen nesa, mu kyautata zamantakewar mu sannan mu yi kokarin bawa yaran mu tarbiyya nagartatciya, saboda mu samar da mutanen da al'uma zasuyi alfahari dasu.
Lamarin be gama tsinka shi ba, sai da suka je suka tarar da mummunar labarin mutuwar su dukka, ita ma Faizan ana zuwa tana mutuwa. Mutuwar matasa a lokacin da suke cike da cin ganiyar rayuwar su, sun dauki duniya sun dora akansu har suka manta da akwai irin wannan ranar, ka tafi bakayi sallah ba, sannan ka tafi domin yin shirka, baka san wacce irin kaddara ce take jiran ka ba, shiyasa a kullum ake so mu zama masu aikata daidai, mu zama masu kokarin kare martaba da dokikin Allah, mutuwa bata sallama ko gargadi, kana tsaka da jin dadin rayuwar ka zata dauke ka, daukewa ta har abadah, a lokacin baka da dama ko ikon gyara kuskuren ka, lokaci ya riga ya kure maka. (Allah yasa muyi kyaykyawan karshe) muji tsoron Allah wallahi, muji tsoron Allah.
***Sun dade ana ciku ciku kafin a sakar musu gawarwakin, zuwa lokacin labarin ya karade ko ina, Hajiya Mama tayi kuka tamkar idon ta zai makance, dan sai a lokacin hankalin ta ya dawo jikinta, ba zata iya tuna komai game da yadda akayi auren Adam din da fiddausin ba, wannan kadai ya kamata ya zame mana ishara da duk wani da yake ganin zai wulakanta dan wani, saboda nasa. Gidan aka kawo gawar Fido bayan an nemi iyayen ta sunzo, ita kuwa dama faiza yar gari ce, ita ma gidan iyayenta aka kaita, daga nan aka shiga kokarin yi musu janaza domin kaisu gidansu na gaskiya. (Kada ki yarda akan duniya da kyale-kyalen cikin ta, ki saida imanin ki, mutuwa bata sallama)
*** Asma'u na kwance tayi filo da kafar Abdallah, kiran umma ya shigo, take sanar mata da mutuwar matar Adam din, sosai mutuwar ta dake ta dan ta santa alokacin da suke zuwa gidan da Adam din, harda kwallar ta na tausayin yadda mutuwar tasu tazo musu ba tare da sun tuba ko sun yi nadama ba, duk da tayi aure amma kuma kowa ya san yanayin zaman da suke da Adam din. Ajiye wayar tayi jiki a sanyaye tsoron Allah na sake shigarta. Tambayar ta yayi abinda ya faru, shi kansa sai da yaji mutuwar duk da ba wai ya santa bane, ba dan dare yayi bama a lokacin zasu je amma sun bari da safe, dan dama tana son komawa gidan Raudan ta sake ganin baby.