← Book details Rayuwar Mace Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 66

Sashe 51

Rayuwar Mace Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya wuce ciki ya barshi a falon yana dariya, duddubawa yayi ransa fes yana jin kamar ya bud'e ido ya ganta a gabansa a cikin gidan, komai yayi kyau sai kamshi ke tashi ko ina, da k'yar ya baro dakin ya karasa dudduba sauran dakunan da toilets sannan suka tafi, ya shirya zuwa kananan kaya riga da dogon wando ya dauki hanyar gidan kunshin da tace masa taje a unguwar gidan Ya Hadizan.
   A hankali yake driving din cikin wani yanayi ya saka wakar Westlife cikin raguwar sauti sosai har ya karasa address din data turo masa, yayi parking daga gefen gidan ya fito daga mazaunin driver ya dawo na gefe ya kwantar da kujerar baya sosai ya kwanta ya ciro wayar sa ya tura mata da text message

"I'm out!"

Karasa mata ake dan yau ne karshen gyaran jikin da Amaryar Kb take mata dalilin masu kawo kayan yasa ta taho nan din, sosai ake mata gyaran yau dan tun safe ake abu daya har da wasu hadaddun turarukan tsuguno da na wanka. Babu in da baya kamshi a jikin ta ga wani santsi da sulbi da fatar jikinta tayi wanda ita kanta da kanta ta san babu karya ta hadu. Kunshin take turarawa yanzu a cikin wani rami aka saka turaren ta zura kafarta da hannun ta bayan kunshin yayi, sai ga text dinsa, reply tayi masa ta ajiye wayar a gefenta. Cikin mintunan da basu gaza talatin ba Amaryar Kb ta gama hada ta tsaf, dama tun jiya tayi gyaran gashi sai turara su da aka yi yau din. Doguwar riga ce abaya a jikinta baka, ta saka flat shoe dinta ta dauki yar karamar hand bag dinta ta saka wayarta tayi ma Amaryar Kb sallama ta fito tana cike da kunyar sa, hango motar tayi daga gefe chan bayan yaga fitowar ta yayi mata fitila, ta nufi wajen kai tsaye ta zagaya bangaren me zaman banza ta bud'e, duhun da ya mamaye wajen ya hana mata ganin sa, ta sako jikinta sosai sai ji tayi an riko ta, ya jawo ta jikinsa gaba daya kamshin ta na ratsa jiki na jijiyoyin sa, wani irin cool kamshi me sanyin dadi,

"Subhallah!" Ya furta sanda ya ji ya kama hannun ta da ya kara taushi sosai har wani tubus tubus yaji yayi,

"My wife."

"Ashe kana nan, ban lura ba."

"Ina sane na dawo nan din ai, I just wants to hold you, ."

Yayi mata whispering yana dan cizon gefen kunnenta, a saman chest dinsa ta dora fuskar ta tana murmushi k'asa-kasa, hakan da yayi ya haifar mata da kasala kwarai, kokarin tashi tayi daga jikin nasa ya sake rukunkume ta, ya manna ta da jikin nasa sosai yayi crossing kafarsa da tata waje daya, ya dago da ita a jikin sa ya jawo kofar motar ya rufe ta.

"Zaki rakani wani waje? Inaso naga kunshin da komai da komai, yadda zan ga nawa ya kamata na biya matar da ta gyara min ke."

" Ya Hadiza na jirana."

" Aina?"

" A gida, kasan gobe ne walimar."

" Gaskiya tayi hakuri, idan ba haka ba sai kawai mu wuce gida gobe sai na kawo ki walimar. "

" Wai,.. su Rauda su sakani a gaba kenan, yau da goben duk daya ne."

" Za'a min wayo, ni dai gaskiya a'ah, hakuri na ya kare. "

Shiru tayi bata sake cewa komai ba, yayi murmushi kawai ya fito ya koma wajen driver ya kunna motar suka bar layin. Wayarta ta ciro daga jakarta taga missed calls din Ya Hadiza, ta kirata tana ayyana me ma zata ce mata? Tana dagawa kuwa tace

"Asma'u shiru wai baku gama ba har yanzu?"

"Na'am, am ammm mun gama."

"Ok, bari Abbati yazo ya dauko ki toh."

"A ah ba sai yazo ba, mun taho ma amma wai zamu biya mu siya wani abun sai mu taho gidan."

"Oh toh shikenan sai kun dawo." Ta kashe wayar, kallon sa tayi shima ya kalleta yayi mata dariya

"Kin cika kunya, kice kin wuce gidanki kawai amma shine kike ta kwana kwana ko?"

"Ba zan iya ba."

"Da ma ni kika bawa na fad'a mata ai."

"Kamar gaske."

Tace tana dariya, dariyar ya saka shima ya maida hankalin sa kan driving din da yasan ko me yasha ba zai taba iyawa ba, shi din ma kunyar ce dashi kamar itan, a wajenta ne kawai yake ajiye kunyar a gefe shi kansa kuma be san dalilin da ya saka baya jin kunyarta ba sam.

"Your hand is very soft." Ya kamo hannun ya dora a saman geer, ya dora nasa akai yana murzawa.

"Me ake saka ma hannu ya zama haka ne? Kinji kuwa?"

"Uhum."

"I love it, I love everything about you in particular."

"Ka daina fasa min kai."

"Ba wani hyping, it's the truth, Alhamdulillah Ya Allah!"

Sautin murnushin ta kawai yaji, yayi murmushin shima yana jaddada godiyar sa ga Allah, yana kuma addu'ar samun nutsuwa da kwanciyar hankali a tattare da ita.

Office din nasa yau ma suka zo, yayi parking a daidai in da sukayi last, ya kuma kama hannun ta suka shiga ciki kamar wanchan lokacin amma wannan babu kowa kamar wanchan lokacin, bud'e kofar yayi suka shiga ciki. Ya kunna hasken office din, sai a lokacin ya ganta sosai, ya bud'e baki ba tare da yace komai ba, kamar wadda aka sauyata da wata ta daban, ga wani fresh da ya ga ta kara hade da wani shihirtaccen kyau na ban mamaki, be san lokacin da ya rungume ta tsam a jikin sa ba, ya dinga shakar kamshin jikinta. Ji yayi kamar zai zame a wajen, ya cikata yana rik'e hannun ta, ya bud'e wata kofa dake gefe a cikin kofar, suka shiga ciki. Dan karamin gado ne wanda be fi yaci mutum biyu ba a ciki, sai tarin wasu kaya a gefe kamar takardu ne ma suka fi yawa. Wajen gadon ya kaita ya zauna yana jawo ta saman kafarsa, ya zaunar da ita yana fuskantar ta, kanta a k'asa ta kasa bari su hada ido dan ta lura kamar akwai matsala a yanayin sa.

"Husnaaa." Ya kira sunanta cikin muryar sa me zurfi, kasa dagowa tayi ya sake kiranta a karo na biyu muryar sa na sake shigewa ciki sosai, dagowa tayi a hankali ta kalle shi tayi saurin sauke kanta k'asa ganin yadda fararen idanun sa suka shiga ciki sosai kamar wanda ya sha wani abu, gabanta ne ya hau dukan uku uku tunawa da tayi komai zai iya faruwa, bata manta kalar wahalar da tasha ba a hannun Adam duk da ta san ba zata taba shan irin ta ba amma kuma har ta gama zaman gidan Adam bata daina shan azaba ba, duk da nashi har da tsana amma ta taba karantawa wata macen har sai tayi haihuwar farko sannan take samun sauki, tsoron ta ne ya karo kokarin da taji yana shafa ta yana kokarin lallai sai ya saka idon sa a cikin nata

"Hakuri na ya kare Husna, I can't, I just can't! Ba haramun bane, ba laifi bane."

"Shikenan!" Ta furta zuciyar ta na tseren gudu, ta saddakar yau me rabata da Abdallan sai Allah, a hankali cike da nutsuwa da kamala ya shiga biyar da ita cikin salon sa me matukar kayatarwa, bata san lokacin da ta saki jiki ba, har ya samu nasarar maida ta kasan shi, yayi mata rumfa akanta yana hade bakin su waje daya, bayan ya gama furta mata kalamai masu ratsa zuciya.

A duk yadda tayi tunani ko hasashen abun ya wuce nan, soyayya ce me taushi da dadi ta danne duk wani ciwo da wahala da take tunani da hasashe, ba zata ce babu ba, musamman saboda gyaran da tasha na musamman amma kuma be barta ko da na sakan daya bane bare har hakan yayi tasiri a gareta, she's so gentle cike da charisma, full of energy amma ba na banza ba irin na Adam, a nutse yayi koman sa bakin sa dauke da addu'ar da annabi Muhammad SAW ya koyar damu a lokaci irin wannan.
Sannu yake ta faman jero mata babu kakkautawa, hade da saka mata albarka, tana kwance a saman kirjin sa hannun sa na zagaye da ita dayan kuma ya tura shu cikin gashin ta da ya wargaje yana tattaro shi, santsin sa da kamshin na shigar masa hanci. Sai da ya tabbatar ta dawo daidai sannan ya tashi ya nufi toilet ya hada mata ruwa me dumi sosai, ya zo yace ta taso,idonta a rufe da ya shigo dan wata sabuwar kunyar sa ce ta sake kama ta, har bata jin zata iya hada ido dashi , ga Ya Hadiza da tasan ta gaji da jiranta, da wanne ido ma zata fara shiga gidan su me ma? Za'a iya harbo jirginta wallahi, dan mara gaskiya ko a cikin ruwa gumi yake yi, bare iyayen da suka haife ka duk motsin ka sun san me kake nufi.
Da taimakon sa ta tashi tayi abinda yace din, ya tayata suka gama, kansa tsaye yake komai ko kunyarta baya ji, tayi ta jinjina hakan a ranta dama namiji in dai anan bangaren ne toh basu da kunya ko kad'an, kamar ba zai aikata ba, nan nan kawai yake da ita har ta gama ta saka kayan ta, ta dawo cikin office din ta zauna ta barshi a ciki, sai gashi ya fito rik'e da riga a hannu be saka ba, tayi saurin dauke kanta dan bata saba ganin namiji a haka ba, ko Adam iyakar ta dashi ya shigo yayi abinda zai ya kara gaba, yana lura da ita kunya taji, sai yazo ya tsaya a gabanta ya mika mata rigar yana marairace mata

"Help me pleaseeee."

"Um Um."

"Kina so mu kwana anan? Dan dama ni wallahi bana so ki koma."

Da sauri ta tashi zata karbi rigar ya rik'e yana girgiza mata kai

" Na ma fasa, anan zamu kwana kawai. "

" Dan Allah. "

" Zo ki kwanta ki huta sai gobe, ba zan iya fita yanzu ba. "
Chapter 51 · 0% Book details