Sashe 28
Rayuwar Mace Complete Hausa Novel · about 8 min read
***Tunda Adam ya koma gida ya kasa zaune ya kasa tsaye, abin duniya yayi masa mugun yawa gashi ya gama saddakarwa da gaske son ta yake, irin soyayyar nan me zafin gaske, irin wadda mutum yake jin zai iya komai akai, sanda ya shiga gidan su sai da Mama ta dube shi ta sake dan ya rame sosai tamkar bashi ba, abinci tasa aka kawo masa amma sam yaji bashi da taste ko kad'an, a tunanin ta ko akan maganar auren sa ne da ta matso sosai, ba zata fasa ba dan haka ma ba zata bashi fuskar da zai zo da wata magana ba, idan ma akan auren ne duk zai sauke idan akayi auren, su Nadeeya ma sun mata mitar sun hakura sun zuba mata ido dan da gaske abin yafi karfin su kuma ba fasawa zatayi ba dan ta kafe. Gidan sa ya koma ya tarar an kwashe kusan komai na gidan da yake a mazaunin na Asma'un, kamar ya ari hauka haka ya koma gidan su ya samu Maman yake tambayar ta kayan gidan
"Na aikawa Asma'u kayanta tunda da sunanta akayi su, ita kuma fiddausi sai tazo da nata."
"Innalillah, amma Mah da baki aika ba, ina so wallahi."
"Me zakayi dasu? Kai da za'a kawo maka sababbi."
Idan ma yace zai tsaya mata bayani ba zata yarda ba, juyawa kawai ya koma ya shige dakin sa ya rufo, ya dauko album din da Nadeeya tasa akayi musu na bikin ya bud'e ya hau kallo tamkar gaula, idan yazo kan nata sai ya dau dogon lokaci yana kallo yana murmushin, sai yanzu ya kara tabbatarwa da kansa ya kamu sosai, kamu me wahalar gaske. Be san ta ina zai fara gyara kuskuren da yayi ba, ya riga ya bata komai wanda gyaruwar sa zatayi matukar wahala. Da hoton ta ya kwanta rungume a kirjinsa, yayi mafarkin tana zaune a dinning tana zuba masa daddadan abincinta ya sauko yazo ya zauna, ta shiga bashi a baki tana masa kallon da yake sake narkar dashi, juyi yayi be san yazo karshen gado ba, sai ji yayi ya fado tim, ya mike a zubure yana zazzaro ido, ya sake daukar hoton ya koma tsakiyar gadon ya kwanta, mafarkin da yayi na dawo masa, tsaki yaja da ya gane da gaske mafarki yake, ya dinga juye-juye kafin ya samu barcin ya sake dauke shi.
***Tun da suka tashi da safe, suka hau shirye shiryen tarbar bako, ya sanar da Abban su Abeed zaizo da yamma wajen hudu da rabi bayan sallar la'asar, seat room din da yake saukar baki ya gyara da kansa har da daga kujeru da su sharar yana ko ina yayi fes, snacks Ya Hadiza ta saka Asma'u tayi me dadi, sannan ta sakata gyara jikinta tayi wanka wajen uku da rabi, tasan ba gwanar kwalliya bace itama kuma tafi son mace ta fito a natural dinta shiyasa bata ce tayi ba, zuwa hudu komai ya zama ready, sukayi sallar la'asar wajen hudu da rabin kuwa sai gashi yazo, da Abban su Abeed suke waya har ya karaso kofar gidan, ya fito ya taro shi zuwa ciki, ya kaishi har falon bayan ya kunna gen kasancewar babu wuta a garin. Ciki ya shiga bayan sun gaisa yace wa Ya Hadiza ta turo Asma'u, tare suka dawo ta riko hannun ta, yana tsaye ya tsokaneta sukayi dariya, a kunyace ta shiga seat room din bakin da dauke da sallama tana kokarin daidaita kanta da yanayin faduwar gaban da take ciki, ga wani irin bugawa da kirjin ta yake yi zuciyar ta tamkar zata hudo ta fito waje. A bayyane ya amsa sallamar tata muryar sa tar idon sa akanta sai dai ita kasa take kallo har ta samu waje ta zauna sannan ta gaishe shi.
"Ba zan amsa ba, haka ake gaisuwa babu kallon mutum?"
Dagowa tayi kad'an, ta kalle shi sai mamaki ya kamata ganin na jiyan nan ne a supermarket din nan
"Yauwa ko kefa, kina lafiya!?"
"Lafiya lou."
"Masha Allah, ya gida ya komai."
"Alhamdulillah."
Daga nan sai sukayi shiru, shi be san yadda ake magana da mace ba gashi dama ba gwanin magana ba, balle ita kuma, yaso MD ya rakoshi amma yaki yace sai dai yaje da kansa idan yaga kamun ludayinsa sai ya rakoshi gaba, baran baran sukayi akan haka, still yaki biyoshi dan har mota ya rakoshi yana tsokanar sa yayi masa banza yayi tahowar sa bayan ya karfafi kansa akan zai iya, sai gashi ya rasa duk kalaman bakin nasa da yayi ta tsarawa a cikin kansa tun jiya, amma ya nemi guda daya sam ya rasa. Kiransa akayi, hakan ya taimaka wajen rage shirun da wajen yayi
"Kana da matsala wallahi." Yace
"Ban sani ba, idan abinda ka kira ka tambaya kenan, toh zan kashe."
"A ah tsaya, Mr love karka kashe dan Allah, kira nayi dama na tuna maka da ka bar note din da ka rubuta na abinda zaka ce idan kazo, bani address na kawo maka yanzu."
MD yayi saurin tsaida shi yana danne dariyar sa.
" I have no time to waste, sai anjima malam! "
Ya kashe wayar yana murmushi, idon su ne ya hadu lokaci daya, tayi saurin janye nata gabanta na sake bugawa da karfi, shi kansa sai da yaji wani abu me kaifin gaske, ya sake murmusawa yana taba zoben azurfar dake hannun sa. Shigo da tray akayi, Abeeda ce ta ajiye ta gaishe shi ya amsa a sake sannan ta fita, ya jawo tray din ya zuba ruwan yasha hade da Bismillah tana jin shi, sai taji ya burgeta hakan da yayi, ya koma ya zauna yana tattaro dukkan nutsuwar sa
"Husna." Ya kirata da sunan da ba wanda ya taba kiran ta dashi idan ta cire Abba da shi ma yawanci Asma'ul Husna yake cewa idan yaso hakan, muryar sa me taushi ta ratsa dukkan sassan jikinta, tayi tsam a zaune wani yanayi na ratsa ta, sake kiranta yayi
"Husnaaa, ga Abdallah yazo da kokon barar sa, yana fatan zai samu karbuwa, ba da wasa nazo ba, da gaske nake so mu fahimci juna."
" Uhum. "
" Pleaseee karki ce a ah, ko kice na miki tsufa, yaro ne daidai dake wallahi. "
Sautin dariyar ta yaji, yayi murmushi yana jin kamar ya samu lagon ta tunda har tayi masa dariya
" Kin yarda? Zaki bawa wannan bawan Allahn dama? "
Shiru tayi dan bata san amsar ba, eh zatace ko a'ah, yasan ta taba aure ko kuwa? Zai karbe ta a haka ko kuwa? Wannan tambayoyin su suka dinga mata yawo aka tun daren jiya, sai da kuma aka zo gabar sannan taji da gaske Adam ya cuce ta, ko ta ina kuwa.
"Baki ce komai ba?"
"Bansan me zan ce ba."
"Kice eh, please kice eh kinji? Ki bani dama kawai, ba zaki danasanin hakan ba."
"Na taba aure." Maganar ta fito ba tare da ta shirya ba, bata ga yanayin sa ba, bata kuma san tasirin da maganar tayi masa ba, kafin ya bata amsa aka danno kai ta hanyar banko kofar da take ta bangaren harabar gidan, Adam ne a tsaye tamkar mahaukacin zaki, yana huci fuskarsa a hade
" Dama tun ranar da na ganka naji bana son ka, ashe ashe abinda zai faru kenan, Malam wanann din matata ce, ka kwashi tsummokaran kafafunka kafin na saka a babballamaka su ka bar nan wallahi. "
Murmushi kawai Abdallah yake daga zaunen da yake ko gezau be yi ba, duk hargagin da Adam din yake be saka ya motsa ba, hakan ya sake hassala Adam din, ya kalli Asma'un ya daka mata tsawa
" Dallah tashi ki shiga ciki. "
Wani banzan kallo tayi masa, kallon da ya saka shi shiga taitayinsa, ta kuma juya wajen ABDALLAH da yake hakimce yana kallon komai hankalin sa a kwance tace
"Na amince Allah ya yi mana zabin alkhairi."
"Amin Ya Allah my soon to be wife, nagode sosai da wannan damar, in Sha Allah ba zaki nadama."
Kamar basu san dashi a wajen ba, haka suka yi, ba kamar Abdallah da ya nuna kamar Adam din be dame shi ba, nan kuwa haushin sa ne sarke a ransa, be niyyar tafiya ba a lokacin amma ba zai iya cigaba da zama inuwa daya da Adam din ba, tashi tayi zata raka shi, ya dakatar da ita dan baya so ya tafi ya barta da wannan mahaukacin, rakata yayi har kofar da zata shiga cikin gidan yana take mata baya, cikin wani yanayi kamar na me tsaron lafiyar ta, sai da ta shiga ciki sannan ya juyo, ya fice daga dakin yana kokarin hana kansa jin kalaman da ke fitowa daga bakin Adam din, a daidai lokacin Abban su Abeed ya dawo daga bayan da ya zagaya, ya hango motar Adam din shiyasa yake ta sauri be san already ya riga ma ya shiga gidan ba.
"Har zaka tafi?"
Yace masa yana waige waige ko zai ga Adam din
"Eh wallahi, amma zan dawo, kamar kayi bako ma,."
"Bako? Yana ina? "
" Yana ciki. "
" Adam! Kayi hakuri dan Allah, babu wanda ya san da zuwan sa, kamar yadda na sanar da kai ne, babu wata alaka yanzu tsakanin su illa ta yan uwantaka, ba dan wannan ba ma na tabbata da yanzu shari'a ake, dan ba zamu kyale ba, dalilin da ya saka na sanar maka kenan, saboda ba'a boye maganar aure a nema. "
" Babu komai, da gaske nazo zan auri Asma'u ko da aure dari tayi ta fito, kuma shi Adam din zan yi maganin abun, so karka damu. "
*RM*
*22*
***Ciki ya shiga bayan Abdallan ya tafi, ya tarar da Adam din yana kai komo a compound din gidan, yana ganin shi yayo wajen shi da sauri
"Adam kana cikin nutsuwar ka kuwa?"
Ya fad'a ganin yadda kirjin sa je bugawa da karfi, dafa shi yayi jin You know what I don't remember the number Now kamar zai zube a wajen, ya taro shi yana furta
"Subhallah;"