← Book details Rayuwar Mace Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 66

Sashe 24

Rayuwar Mace Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Owk, tunda haka kake so, fine! "

Sai ya kalli bayan sa

" Kuna ina!? "

"Gamu sir."

"Ku dauke shi daga nan, ku dan sassamamin shi ko zai koyi manner's."

"An gama sir, Adam na zaune wai shi uban taurin kai, sai gani yayi sun karaso, suka bud'e motar suka fizgoshi, suka shiga lallasa shi tamkar yadda ogan nasu yace. Gate ne ya bud'e mota ta fito daga gidan Baba Alhaji, Abuya ne, shi kadai babu MD shima zai je ya siyo perfumes ne saboda nasa sun kare, ganin kamar suna dukan wani ya sakashi danne horn, suka dakata ya fito da sauri

" Lafiya kuke dukan sa? "

" Barawo ne! "

" Barawo? " Yace yana leka fuskar Adam din, nan da nan ya shaida shi, dan yana da saurin gane mutum

" Satar me yayi? "

" Tun dazu yake zaune kamar bashi da gaskiya, shine oga yace bari yayi masa magana amma sai ya hau oga da cin mutunci, shine muke dan koya masa hankali."

"Ku kyale shi, tashi."

Ya mika masa hannu. Adam da yaci bugu sosai a wajen yan sandan majiya karfi ya kasa mikewar, bakin sa ya mutu murus dan har ya soma basu hakuri, be taba dakuwa irin ta yau ba tun da uwar sa ta haife shi, sai gashi a banza masu warin kashi sun daddaka shi saboda shegen bakin sa.

Taimaka masa Abuya yayi, ya tashi sannan ya rakashi wajen motar sa,. Ya bud'e masa gefen me zaman banza ya shiga, sannan yace dan sandan guda yazo ya kaishi chemist sannan ya kaishi gida, ba musu yazo ya shiga, ya kalli Adam din da yaki yarda ya kalli bangaren sa yace

"Kayi hakuri aikin su kenan, da ka basu hadin kai duk hakan ba zata faru ba."

Kin magana yayi, ya juyar da kansa dan iyakar muzanta ya muzanta, har baya son ganin mutumin gashi ya tsaya yana bata masa lokaci da wasu maganganun sa na banza, kila ma su suka saka aka sake shi akan abinda ya faru ranar, amma koma menene, ai ba zasu dawwama a cikin unguwar tasu ba, idan kere na yawo, zabo na yawo toh dole zzsu hadu, kuma sai ya rama wulakanci da akayi masa.

*RM*

     18

***Har kofar gida ya kaishi ya ajiye ya wurga masa mukullin sa ya tafi, gidan su ya shiga a maimakon nasa gidan da ji yake ya tsani duk abinda ya danganci gidan nasa, yana shiga Hajiya Mama ta dauke kanta kamar bata ga shigowar sa ba, sai dai yanayin yadda yake tafiya ya saka ta kallon sa, ya wuce zuwa tsohon dakin sa ya shiga, akwai matsala, ta lura abin ka da uwa mahaifiya sai ta kasa jurewa har sai da ta tashi ta bishi zuwa dakin, ta tarar ya cire rigar sa yana kallon bayansa a mudubin dakin, zaro ido tayi ganin layin bayan sa, yayi kamar be ga ta shigo ba, ya hau maida rigar sa

"Me ya same ka?"

"Ba komai." Yace yana to maida rigar jikin sa,

"Karka fad'a min din, jikinka ne ai ba nawa ba, mun yanke shawarar aura maka fiddausi saboda rufin asirin mu."

" Wa zai aure ta? Ni wai? Karya ma fa take bata da cikin komai, idan ma dashi ai baa aure da ciki ko? "

Ya kyalkyale da dariya, shiru Hajiyar tayi, tunanin hakan sam be zo mata ba, tabbas musulunci yayi hani da aure da ciki, duk da akwai masu yi saboda son zuciyar su, itama sam bata tuna hakan ba saboda idon ta ya rufe, amma me yasa Abba ya bata wannan shawarar toh? Shima ya manta ne ko kuwa dai yana daukar ta a yanzu xata iya komai ma don biyan bukatar ta, shiyasa ma be tsaya nuna mata ba yayi komai a dunkule, nufin sa duk abinda zatayi kawai tayi ko da hakan ya saba wa addini, girgiza kai tayi ta juya ta bar dakin, jirin da take ji yana kara karuwa, kwanciya tayi ko zata samu sa'idah amma sai taji a kwancen ma jirin take yi, kiran Nadeeya tayi da ta tafi chan gidan kanin baban su da rikicin nan be bar Hajiyar ta samu halartar komai na bikin ba, saukin ta dama ba a gidan ake taron ba girki dai ne akayi anan da sauran abinda ba za'a rasa ba, shiyasa yau tace Nadeeya din taje ta kara basu hakuri, jin jikin nata ya kara rinchabewa ne ya sakata kiran Nadeeya din, tace ta dawo bata jin dadi, bata dade ba sai gata, ta tarar da Hajiyar zazzabi ya rafke ta, ga jirin da ya dameta a kwance ma yin shi takeyi, auna bp dinta tayi, taga yayi high sosai, ta shiga bata taimakon gaggawa, zuwa dare jikin ya sake rikicewa, dole ta dauke ta, ta tafi da ita asibiti, nan da nan akayi admitting dinta, aka daura mata drip, nabeela ta kirawo sannan ta kira fadeela ta fad'a musu an kwantar da Maman dan duk abinda ake su ba wani sani sukayi ba, nan da nan sai gasu, lokacin Maman ta samu bacci , ta rame sosai kamar ba ita ba.
   Tare duk su ukun suka kwana da ita, dan dama duk babu me wani nauyi akansa, nauyin miji ne kawai babu wacce ta haihu cikin su, basu kira Adam ba, dan haushin sa suke ji sosai, duk shine yayi sanadiyyar shigar Maman halin da take ciki, kuma kamar be damu ba, kansa kawai ya sani.
   Da safe ya shiga cikin gidan ya tarar basa nan, ya tambayi mai aiki suna ina, sai anan yake jin an tafi da Maman asibiti, ya ciro wayar sa ya kira Nadeeya amma bata daga ba, ya dinga jera mata kira har ya gaji, ya dauki mota dan yana da yakinin asibitin su zata kaita.
   Yana zuwa ya samesu a chan dan a barander suka hadu da fadeela ta fito siyan abu, ta share shi yana mata magana tayi tafiyar ta, sai ya bin bayanta har ta siya abinda zata siya ta juya sannan yaga dakin da Maman take. Babu wanda ya kulashi a cikin su, ya shigo ya zauna kusa da Maman yana rik'e hannun ta a cikin nasa, baya so wani abu ya samu Maman dan bashi da tamkar ta kaf duniyar nan, ji yayi yana nadamar wasu abubuwan da ya aikata, wanda ya tabbata su suka janyo shigar matsalar Maman, ba zai kyale Fido ba, duk ranar da ya kamata wallahi sai yayi mata rashin mutuncin da bata taba zato ba, dan yasan ita ce ta sake assasa matsalar da Maman take ciki.
   Ko da maman ta farka bata nuna ta ganshi ba, suka dinga maganar su, su kadai babu wanda ya saka shi a ciki, haka ya cigaba da zaman sa ba tare da ya damu ba, dan yasan babu wadda a cikin su zata hanashi zama a dakin.  Waje azahar Abba yazo dan sai a sannan ya samu labarin, ya dubata ya wuce da daddare suka sake dawowa da Umma itama ta duba ta, umma ta lura duk kunya ta hana Maman sakewa dasu, har suka tafi bata iya yin magana sosai ba, da safe Abban ya sake dawowa tare da Abbati da breakfast yace da rana umman zata zo ta sake dubata.

   Asma'u na kwance umma tace ta tashi ta shirya zata rakata dubiya, tun da ta dawo gidan fitar ta biyu ce shima asibiti kuma tare da Umma suka je da Abbati, Hijab kawai ta saka me hannu maroon ta saka flat shoe ta rik'e wayar ta a hannu ta fito, ta samu umman tana karasa shiryawa. Titi suka fita kasancewar a napep zasu Abbati baya nan Umar ma haka, babu me mika su, shiyasa umma ta bar abincin sai da daddare wani a cikin su sai ya mika musu idan sun dawo.
   Sai da suka shiga napep din sannan take tambayar umma in da zasu

"Waye ba lafiya!?"

"Hajiya Mama ce, kwananta biyu a asibiti kamar."

"Allah ya kara sauki." Tace ta ja bakin ta ta tsuke har suka isa, suka nufi dakin kai tsaye tunda already Abba ya riga ya fad'a ma umma room number din.
   Dakin a cike yake da mutane yawanci kawayen Maman ne sai su nabeela da fadeela sai sirakar fadeelan da tazo da kannen mijin nata, a waje suka dan tsaya na ciki suka fito sannan suka shiga, Hajiya na ganin su ta washe baki tana kafe Asma'un da ido, daga bayan umman Asma'un ta gaishe ta, ta dubata amma sai ta yafito ta da hannu, ta matsa gaban gadon a darare.

"Ina wuni?"

"Lafiya lou Asma'u, kina lafiya."

"Lafiya lou." Ta amsa tana sunkuyar da kanta k'asa,

"Zauna mana." Ta nuna mata kujerar gefen gadon, ta zauna ba musu tana zama Nadiya ya shigo, ta gaida umma cikin girmamawa sannan ta isa wajen Asma'u fuskar ta na bayysna farin cikin ganin ta, ita kanta Asma'u taji dadin ganin ta ko babu komai Nadiya ta nuna mata soyayya irin ta Yaya da kanwar ta, kuma ta sota da gaske ba kamar Hajiya da dan lelen nata ba, su dama Fadeela da Nabeela ba wani haduwa suka cika yi ba, amma duk da haka ta san ba kamar Nadiya da ta nuna mata soyayya fiye da Adam din da suka fito ciki daya ba.
   Ita dai umma nata ido ne ganin yadda suke nan nan da Asma'un, wato baka gane muhimmancin abu sai ka rasa shi, wajen la'asar umman tace Asma'un ta tashi su tafi, fuskar Maman ce ta sauya zuwa bacin rai, tace

"Har yanzu fushin ne umman su?"

"Fushi? Akan me yaya?"

"Akan abinda ya faru."

"Ai da mun dauki fushi ko zuwa nan ba zamuyi ba, ko kuma nazo ni kadai na barta a gida, mu babu komai a zuciyar mu wallahi, ai ya wuce."

"Toh idan da gaske ne, dan Allah ki bar Asma'u ta zauna zuwa anjima sai ta dawo."

Girgiza kai Umma tayi

" Kiyi hakuri."

Sai ta kalli Asma'un da ta riga ta mike amma kuma bata taho ba

" Muje, Allah ya kara sauki Hajiya."
Chapter 24 · 0% Book details