Sashe 57
Rayuwar Mace Complete Hausa Novel · about 8 min read
Satin sa biyu iyakar sa yar karamar unguwa su fita da MD shima basa dadewa, ba karamin sabo tayi dashi ba a yan kwanakin har takan ware suyi ta hira kamar ba gobe, ga wata irin zazzafar soyayyar sa da ta sake kamata. A dan zaman nan nasu ta gane wanne irin miji Allah ya bata, me cike da tarin abubuwan mamaki, mutum ne me tsananin addini da kankan da kai, baya taba ketare iyakokin Allah yana kums kokari sosai wajen sauke nauyin dake rataye a wuyan sa, ba zata ce tafi kowacce mace sa'a ba, sai dai tana da yakinin zata iya jerawa a cikin matan da sukayi dace da sa'ar miji a wannan zamanin.
Washegari zai koma aiki duk kuwa da shine ogan kansa amma ta lura baya sanya wajen aikata duk abinda yake ganin zai sake kafashi, a hakan ma yana gidan ko yaushe yana kokarin rage ayyukan nasa ne, wanda yake daukar kaso mafi rinjaye a aikin company din nasa, be zauna ya nade hannu da kafa ba, shiyasa har yanzu yake samun cigaba a al'amarun sa.
Da wuri tashi ta shirya masa abin kari ta kuma taimaka masa wajen shiryawa, ya tsuke abinsa a cikin suit ash colour, ya makala necktie ya saka half cover shoe da black socks saboda bakin da zasuyi yau din wannan shigar ita ta dace da zama dasu. Be sani ba, ta dauke shi hoto ya juya yana tattaro wayoyin sa da system dinsa, fuskar sa a kasa ya dan dukar da kan, yayi kyau a hoton ga wani irin haske da ya kara tun bayan auren su, so take ma ta tambaye shi zuwa gida amma ta kasa, gashi yau yace mata zai iya kai magriba be shigo gidan ba, dan ma su Amira na zuwa ko ita taje anan zata dinga rage zaman.
"Kayi kyau."
Ta samu kanta da furtawa bayan ta karbi jakar hannun sa ta rataya a kafadarsa suka shiga takawa zuwa falo. Hancin ta ya lakace mata yana murmushi
"Har na kaiki kyau? Kin ganki kuwa? Gaskiya na iya kiwo wallahi, bul-bul fa ko ina, har nan."
Yace yana pointing din kirjinta, hararar sa tayi a wasance tace
"Dama a haka nake."
"Ummm... Ba wani."
"Allah!"
"Shikenan bani jakar nan kar nayi late, MD na waje yana jirana ba sai kin rakani ba."
Mika masa tayi sannan tace
"Allah ya kiyaye ya bada sa'a."
"Amin my wife, nagode ki kula min da kanki."
***A birkice yake tunda ya tashi a yau din baya jin komai baya ganin kowa sai ita, ga Fido a gefe da ta hana masa sakat idanun ta na kan duk motsin sa, kwana biyu kenan yana bibiyar motsin Abdallan har office dinsa yaje akace baya zuwa, gashi babu damar zuwa unguwar tasu saboda polisawan nan dan ba karamin aikin su bane su nada masa na jaki yanzu bashi da kwari.
Ganin yau Monday ya saka shi son sake komawa yaga ko yazo, ga Fido taki fita dan tun sassafe yake saka ran zata fitan,amma shiru, yana nan zaune bayan ya gama shan tea da slice bread biyu yaji tana wayar zata fita, murna ya hau yi ya labe yana kallo ta shirya, tazo ta sameshi ta ja masa warning, ya amsa da toh tana fita ya saka kai shima ya fice sai K'AREFA MOTORS
RM
48-49
***Kallon gidan Hajiya Mama yayi, ya wuce ba tare da ya shiga ba, pcap ce a kansa sai wayarsa da suke magana da g-boy, yana gamawa ya tura wayar aljihu ya tsaida napep yace ya kaishi site din, zuciyar sa ta riga ta kekashe zai iya aikata komai, ya tsani Abdallan tsana me tsanani, shiyasa yake ganin idan ya barshi tamkar yaci banza ne, ya kuma samu damar shi sosai. A gefen gate din aka ajiyeshi, ya bashi kudin sa ya karasa gate din da kafarsa, me gadin wajen ne ya kalle shi, yayi saurin cewa
"Oga ya shigo kuwa!? Kwana biyu bana samun sa ga shi alhaji ne ya aiko ni a duba masa wata mota idan tayi zai siya wa Madam."
"Wanne ogan a ciki?"
"Abdallah!"
"Ok yazo kuwa yau tun dazu ma, yau kayi sa'a."
"Lallai kam, hala ma baya kasar ne kasan su manya."
"Ina, aure yayi ai! Ango ne hutun aure ne shiyasa ma kuke ta sabani, ka shiga yana main part din amma ka fara samun sakatariyar sa kaji idan zai ganka direct ko kuma kaje wajen manager in dai maganar mota ce kawai."
" Ok toh nagode kwarai, ga wannan ka sha ruwa."
" A ah ba zan karba ba, akan me?"
" Shinfidar fuska ai tafi ta tabarma,kyautatawa ce kawai nayi maka."
" Toh shikenan nagode, Allah ya kara arziki."
" Amn." Yace yana kada kansa zuwa ciki. Motoci ne birjik a wajen iya ganin ka, be tantance motar Abdallan a ciki ba, sai chan ya hango motar da suka taba haduwa har suka dan yi rigima, matsawa yayi wajen motar yana kare mata kallo, sai ya kada kansa zuwa gaba yana cigaba da duduba su, wani daga cikin ma'aikatan wajen ne yazo, ya sameshi yace masa me yake so? Sai yayi masa karyar yana duba motocin ne, kiran sa akayi ya bar wajen hakan ya bawa Adam damar labewa a wajen yana monitoring duk movement din wajen. Abdallah na zaune suna meeting da shareholders na companyn nasu MD ya shigo bayan ya nemi excuse ya ja Abdallan gefe sukayi magana sannan ya fita, shi kuma ya dawo ya basu hakuri sannan suka cigaba. Har wajejen sha daya suna meeting din kafin ya rakosu wajen motocin su, su hau su tafi, juyawa yayi ya koma ciki, Adam na kallon sa, ya kusa shiga sai yaga ya dawo da baya, ya tsaya wajen wata Lexus Fara ya bud'e ya dauko abu a baya, sannan ya rufe ya koma cikin building din, girgiza kai Adam din yayi, ya dawo wajen motar ya dauki hoton ta ya turawa g-boy sannan yayi wa gateman din sallama akan zai dawo be samu ganin Oga Abdallan ba, ok yace masa sukayi sallama ya kama hanyar sa, yana addu'ar Allah yasa Fido bata dawo ba, har ya koma kuwa bata dawo ba, yasan kila nesa tayi sai kawai ya sake ficewa zuwa wajen wasu abokan sa a chan kasan layin su.
***Suna zaune dasu Amira da Ihsan suna hira, bayan sun gama cin abinci a part din, dan yanzu kusan kullum anan suke cin abinci suna santin abincin ta, da taga haka sai take kwasar su, su shiga kitchen din tare dan ba wani iya girkin sukayi ba, ba yi suke ba dan masu aiki ne suke musu komai sai dan dafa indomie da soya dankali abubuwa dai marass nauyi da wahala, su dai ko dan ba mssu kudi bane? Tun suna kanana umma take jan su kitchen take koya musu abubuwa har suka goge dan kaf cikin su babu wadda idan tayi maka girki ba zaka yaba ba. Tasowa tace su yi ganin rana na neman yi, ta duba kullin sinasir din taga ya tashi sosai, dan ba laifi ana rana a garin, tare sukayi aikin komai suna kallo dan baa taba ma yin sinasir a gabansu sun gani ba, dan haka sai ya zamar musu wani sabon abu da suke daukin sa. Raba musu aikin tayi ita kuma ta karasa hada miyar sinasir din wadda sun kusa gamata dama tun dazun, sunayi tana kara wayar musu da kai har suka kammala nan da nan, ta zuba musu nasu a flask daban sai na Abuya shima tare da MD dan tasan tare zasu dawo, nata kawai ta bari a wani flask din daban bayan ta jera musu nasu a tsakiyar falon. Amira ce ta gyara mata kitchen din sannan suka tafi da nasu shashen su, suna fita ta kunna turaren wuta ta sake gyara falon.
Tana zama taji karar motar su a compound din part din nasu, curtains ta daga ta leka ta hange su suna fitowa, shine a side din da take kallo, ya rataya rigar suit din a kafadar sa ya nuna alamun gajiya sosai, murmushi ta saki ta wuce daki ta dauko madaidaicin mayafi saboda MD, ta yafa ta dawo falon dai-dai lokacin da suka shigo.
"Sannun ku da zuwa."
Tace tana tsaye bayan kujerun falon, MD ne kawai ya amsa yana zama gogan sai ya zarto wajenta ya bud'e hannun sa alamun ta rungume shi, ya riga ya saba mata da hakan shiyasa ma bata ji komai ba, tayi abinda yake so ya sauke ajiyar zuciya yana sakin ta
"Ba abunda yafi dadi kamar ka dawo gidan ka, ka samu matarka tana nan ga wani kamshi me dadi yana tashi."
"Anty I'm hungry, idan na tafi sai ku cigaba da soyewar."
MD yace a kufule, dariya suka kwashe masa dukka dan dama Abdallan yayi masa haka ne da biyu.
"Idan anyi zuciya ayi auren mana, ka kusa daina biyo ni gaskia kana takura mana."
"Anty, zan iya fara ci?"
Yace yana zamowa,
"Zaka iya, Bismillahi."
"Muje ki taimaka min na watsa ruwa, I'm damn tired! "
" Ok sir! "
Ta sara masa, sukayi dariya suka wuce suka bar MD ya fara kai loma.
Wanka ta taimaka masa yayi, ta dauko masa jallabiya me gajeran hannu dan yace ba zai sake fita kuma ba ya gaji, falon ya fito ita kuma tayi zaman ta barsu suci abincin. Be dade ba sai gashi ya dawo ya haye gadon yana rufe idon sa
"Bacci!" Yace yana miko mata hannu, noke kafada tayi tace
"May be next time!"
"Zan kama ki ne." Ya rufe idon sa nan da nan baccin ya dauke shi. Falo ta fito ta tarar sun kwashe kwanukan sun maida su kitchen, dabi'ar su kenan in dai sun ci abinci toh zasu kwashe kayan ba zasu barsu a wajen ba, ba kuma shi kadai ba hatta MD din haka yake idan yazo yaci abinci.
Game take a wayarta ta mike a doguwar kujera sai ga kiran Umma, ta daga cike da zakuwa dan ba kasafai umman ke kira ba sai dai su kusan kullum sai sun kirata sun yi waya da ita
"Rauda ta haihu."
Wani tsalle ta daka kamar wata karamar yarinya cike da farin ciki tace