← Book details Rayuwar Mace Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 66

Sashe 23

Rayuwar Mace Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Menene amfanin rashin hakurin? Beside ba wai yayi mana wani abu bane me muni, ko da ace yayi din ai be kamata mu biye masa ba ko?"

Dukan sitiyarin motar yayi,

" Kullum haka kake cewa, ai kai kam kana da heart of gold, matar ka ta huta wallahi."

Dariya ya saka yana maida ganin sa zuwa cikin katafaren gidan nasu sanda gate din gidan yake budewa, sai da suka shiga ciki motar ta daidaita sannan ya bashi amsa

" Kai kuma matar ka ta shiga uku da mitar ka."

Balle murfin motar yayi ya fita, ya zagayo ta bangaren MD din yace

" Mika musu sakon ka same ni a masallaci,."

"Okh Ya sheik!"

Murmushi kawai yayi, ya nufi masallacin cikin gidan yana nannade hannun rigar sa.

Ciki MD din ya shiga dauke da sakon Baba Alhaji, ya tura kofar falon ya ajiye saboda babu kowa, ya fito ya nufi masallacin dan yasan duk suna chan.
Sallah sukayi tare da ma'aikatan gidan da makwafta na kusa da suke shigowa ta kofar waje, ana idarwa suka zauna karatun bayan magriba har zuwa lokacin isha, sannan suka yi sallar kowa ya fito, tare suka jero da Baba Alhajin suka saka shi a tsakiya suna maganar aiken da yayi musu, MD ne yake bashi amsar duk tambayar da yayi dan shi gogan dama mafi yawancin lokuta MD din ne ke aron bakin sa yaci masa albasa, sai ayi abu sau tari sai dai yayi murmushi kawai, baya dogowar hira idan ba da MD din ba, shi kadai yake sakewa suyi hira sosai, mutane har tambaya suke anya Abdallah yana magana kuwa, dan sai ka wuni dashi baka ji yace komai ba.

Sai da suka rakashi har ciki, ya zauna sannan suma suka zaune cike da girmamawa, ya kalle su dukka, yace

"Abuya, miko kayan nan na gani."

Tashi yayi ya dauko ya kawo masa gabansa ya ajiye,

"Kai kuma Mudassir, tashi ka bud'e mu gani, Allah dai yasa an yi abinda ya dace."

"Amin, suka amsa MD ya bud'e kayan suka dudduba, komai yayi yadda ya kamata, maida su gefe akayi, suka dan taba hira kad'an kafin su tashi su wuce zuwa shashen su.

Suna shiga MD ya fad'a saman kujera ya sauke numfashi,

" Mitar ce?" Yace yana kokarin shiga chan ciki

" Kana da matsala wallahi."

" Toh ai naga abu baya wucewa wajen ka ne fa."

" Wannan din ma be wuce ba, har sai na hadu dashi na koya masa hankali."

" Allah ya bada sa'a."

Ya wuce ciki, ya sauya kayan jikin sa sannan ya dawo falon nasu, ya tarar da MD din yana waya, yana kashe murya tamkar bashi ba, girgiza kai yayi ya jawo laptop dinsa ya jona ya shiga rage ayyukan dake kansa.

***Bangaren Asma'u kuwa, sosai ta kwantar da hankalin ta, dan dama ba wai ta damu bane, kawai dai tana bukatar healing daga abubuwan da suka faru, gata babu irin wanda Abba ya nuna mata, yana dawowa gjda zai saka a kira masa ita su zauna yayi ta hilatarta da hira, tun tana nokewa har ta saki jikinta, tana jin ya dawo idan ta daidaici ya huta take zuwa, hakan ya taimaka kwarai wajen samun nutsuwar ta, bata tuna Adam bare shirgin sa, ranar suna zaune Hajiya Mama ta kira Abba, tunda abin ya faru bata kira shi ba, dan bata da bakin da zata masa magana, yanzu ma maganar Fido ce ta hana ta sakat dan yarinyar babu alamun zata hakura, ita kuma a yanzu duk yadda zatayi ta kare mutunci da martabar gidan ta zatayi. Tashi yayi ya saka Abbati ya kaishi, sai yayi mamakin ganin ramar da Hajiya Maman tayi, kana gani zaka gane bata da lafiya sosai,ji yayi duk babu dadi, ya zauna ya gajshe ta, ta amsa masa a kunyace ta saka aka kawo musu ruwa, fita waje Abbati yayi ya barsu su kadai, ta shiga sansr dashi matsalar da take fuskanta tun bayan rabuwar Adam din da Asma'u, shiru Abban yayi yana nazarin maganar a zahiri, a badini kuwa girman Allah yake sake gani, ko babu komai Asma'u ta wanko, kuma tayi biyayya irin wadda ba kowa ne zai yi ba, ganin yaki cewa komai a tunanin ta ba zai taimaka mata ba, sai ta fashe masa da kuka tana bashi hakuri, da sauri yace

"Dan Allah Yaya kiyi hakuri, komai ya wuce a waje na, yanzu kokarin yadda zamu kauwar da matsalar da take gaban mu ce kawai, abu daya za'a yi, shine tirsasa Adam auren yarinyar nan, idan ba haka ba, matsalar da zata jawo gaba sai tafi haka, kuma kince dalilin sa take zaune a garin nan."

"Haka ne."

"Toh shawara daya, ya aureta,tunda sun fahimci juna sun san junan su, zaman zai musu sauki, sai ta haihu a dakin ta cikin rufin asiri."

"Na shiga uku, yanzu Karami ina rufin asiri a haihuwar tit."

" Toh ya za'a yi Yaya? Ko kina da wata shawarar."

Girgiza masa kai tayi,

" Kin gani, hakan shine rufin asirin mu dukka."

Shiru tayi kamar ruwa ya cinye ta, ta dinga jan maganar ta gaza furta abinda zata ce, bata san da wacce fuskar Abban zai kalle ta ba, kila ya kirata da wadda tafi kowa son kai a duniyar baki daya, har tsawon mintuna ta gaza cewa komai, yana lura da yanayin ta, magana take son yi ta kasa, mikewa yayi yana gyara babbar rigar sa

" Zan koma Yaya, idan akwai wani abu sai a sanar dani."

" Toh toh, nace ba... Dan Allah ba zakayi hakuri Asma'u ta dawo dakin ta ba?"

Chak ya tsaya da abinda yake, ya kalli Maman, tayi saurin dauke kanta, shiru ya biyo bayan maganar ta ta, dan be san me zai ce mata ba, kunya ce ita kanta ta kamata, tayi saurin cewa

"Bansan na furta ba, kayi hakuri."

"Allah ya kyauta."

Yace kawai yayi mata sallama ya tafi, yana fita ta dafe kanta tana jin kamar zai tarwatse mata, sakamakon makauniyar soyayyar da ta nuna wa Adam din kenan, karshe ita zai saka a masifa dan ta lura shi be damu ba da duk abinda yake faruwa ba, kwana biyu ma bata saka shi a idon ta ba, an dai tabbatar mata a gidan sa yake kwana amma baya shigowa nan din, hankalin ta duk yana kanshi tana tsoron kar yaje yayi wani abun.

Ranar da wuri ya shigo gidan, ya kalli dinning area din yaga wayam, tsawon kwanaki uku kenan duk sanda ya shigo gidan sai idon sa ya jashi zuwa dining din, daga nan sai zuciyar sa ta tunzura shi ya kawar da tunanin da yake neman hanashi sukuni, shiyasa baya zama a gidan kwata kwata, da ya shigo sai yaga tamkar ita din zai gani, yau ma dalilin dawowar sa gidan da wuri saboda kansa da yake masa ciwo, neman Fido yake ido rufe amma sam ko a waya baya samun ta saboda ta shirya ci masa mutunci, sosai ya shiga matsala sanadiyyar hakan da shi bashi da burin auren mace irin Fido din gashi kuma tana neman sakashi dole, duk da yana ganin babu uban da ya isa ya sakashi auren da be niyya ba.
Kai tsaye sama ya hau, ya nufi dakin ta, inda koman ta yake a yadda ta barshi sai kayan sawarta kawai da Ya Hadiza tazo ta kwasar mata tun ranar da ta tafi, babu wanda yazo yace zai dauki wani abu kuma bayan nan, saman gadon ya fad'a mayen turaren ta da yake jin yana shigar masa hanci yana nan manne da zanin gadon da blanket din da ta rufa dashi a ranar da ya dake ta, kwanciya yayi, ya rufe kansa da blanket din kamshin na ratsa shi, ya jima sosai a hakan har sai da abun ya dawo kansa, ya tuna a inda yake, ya kuma tuna abinda yake, ya mike zumbur yana yin jifa da bargon ya sakko yana jan tsaki, cikin son karfafa kansa akan abinda yake ganin ba me yiwuwa bane, amsa kuwwa muryar ta, ta shiga yi masa a kunne tana ratsa shi, sanda take masa magiya akan ya daina dukan ta, muryar ta tar cikin yanayin wahaltuwa, kama kansa yayi da hannayen sa biyu ya damke, ya toshe kunne yana girgiza kansa, yana magana da sauri yana barin dakin

"Na tsane ta, bana son ta bana kaunar ta, na tsane ta, na tsane ta!"

Ji yayi zuciyar sa ta karyata shi, ta maida masa da martanin karya yake, da sauri ya suri key din motar sa, ya shiga ya bar gidan gaba daya, sai dai maimakon hakan ya taimaka masa wajen samun saukin abinda yake bijiro masa, sai ma abinda ya karu, yawo ya dinga yi a titi, ya shiga nan ya sauka nan ya rasa in da zai kai kansa, a ganin sa yana da damar da zai iya yin fatali da banzan tunanin da banzar zuciyar sa take saka masa ba, be san cewa, addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi da Allah, kai tsaye Allah yake amsata.
Wasa-wasa sai gashi ya kusan kure duk titinan, gangarawa yayi wata babbar unguwa dake kusa da in da yake, ya shiga wani layi yayi parking motar ya kashe kawai ya kwanta a ciki. Ya dan dade a cikin motar dan layin babu mutane babu hayaniyar kowa duk suna cikin gidajen su, ji yayi an masa knocking a window din sa, ya dago ya kalli mutumin dake tsaye.

"Malam lafiya?"

"Kamar ya?"

"Eh naga kazo nan ka zauna ne tsawon lokaci, idan wata matsalace sai ka fada ko?"

"Ina ruwan ka? Ko tsabar shishigi!? Ku me yasa sam mutane bakwa minding business dinku ne, da kunga mutum sai kuzo ki ishe shi da tambayoyi, mtsw bana son irin haka."

"Daga tambaya? Naga ka dade ne a wajen, kuma a ka'idar unguwar nan matsayin mu na masu kula da tsaron wajen bama barin bare ko wanda bamu sanshi ba, ya zauna haka babu wani abu, ka dauke motar ka kayi gaba, ko kuma ka fuskanci hukunci. "

" In naki fa? "

"Jikinka ne zai gaya maka. "

"Babu in da zani, tunda dai nan din ba gadon gidanku bane ai, idan kuma gadon ku ne sai naji."
Chapter 23 · 0% Book details