Sashe 58
Rayuwar Mace Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Me ta haifa?"
"Mace!"
"Wayyo, yanzu zan taho in sha Allah, gani nan."
"Ke gandoki, bata dawo gida ba ai, tana asibiti kuma kamar idan aka sallameta ma gidan ta zata wuce."
"Wai, ba zai barta tazo gidan ba umma?"
"Yaki, nima ta wani bangaren ban ga laifin sa ba, sai a tura Mama Gaji kinsan kokarin ta, zata kula da ita kuma surukar tata ma zata kula da ita sosai nasani."
"Ai umma da ya barta ko sati biyu ne, wayyo ta tama zuwa gidan nan wallahi. "
" Sai ta hakura ai tunda ba dole bane, al'adah ce kawai dama."
" Haka ne kuma, bari na shirya naje."
" Yawwa, idan kinyi abinci ki dan tafar musu dashi dan duk suna chan tun dazu,ke kadai ce har su Abbati."
" Shine baa fad'a min ba."
" Zuwa zaki ki tashi hankalin ki,ki tashi nasu, gwara da aka saukan kinga ai yafi kai waye."
" Zan kama Hidaya nasan ita duk tasa aka ki fad'a min "
" Kun fi kusa, sai anjima ni dai karki cinyen katin."
" Sai anjima."
" Wace ta haihu? "
Bata ji fitowar sa ba, har yazo ta bayan ta yayi maganar, da sauri ta waiga yana tsaye a bayan kujerar.
" Ba bacci kake ba dama? "
" Na tashi ai tun dazu, MD ne ya tashe ni wallahi wai zai fita a mota ta, ya zata keys din na hannu na, a chan office na barsu daga nan kawai sai naji baccin ma ya tafi gaba daya! "
" Ayya, Rauda ce ta haihu, an samu baby girl."
" Masha Allah, Alhamdulillah; Allah ya raya yasa cikon addinin musulunci ce. "
" Amin, suna asibiti ma. "
" Zaki je ko? "
" Eh. "
" Ok, bari naje na sauya kaya sai nayi dropping dinki ko? "
" Owk...nagode. "
" sshhssh! "
Ya dora hannun sa a saman bakin sa,
" Babu godiya tsakanin mu. "
Ya juya ya barta tana murmushi, abincin ta zuba musu a wasu warmers din ta hada a babban basket ya fito ya dauki basket din suka fito, motar MD ce a ita suka dawo dama dazun, suka shiga suka nufi asibitin da tasan Raudan na zuwa ANT.
Sai da suka shiga asibitin sannan ta kira Hidaya tace mata suna postnatal, chan suka nufa yana rik'e da basket din suka jera abin gwanin ban sha'awa. Ya Hadiza ce ta fara hango su, ta taba Hidaya tana nuna mata su, murmushi sukayi cike da jin dadin yadda rayuwar Asma'un ta juya a lokaci guda. Wajen suka karaso ya gaida su Ya Hadiza sannan suka shiga ciki ya duba Raudan yaga baby, ya dade rik'e da babyn a hannun sa yana admiring babyn, dan taba ta yayi ta juya ya nuna mata babyn yana murmushi
"Irin wannan nake so ki haifa mana, very cute kamar ke."
Kin tanka masa tayi ta juya kawai dan su Ya Hadiza na ankare dasu, tashi yayi bayan ya ciro kudi a aljihunsa masu dan kauri ya ajiye sannan yace mata zaije ya dawo ya fita, hararar ta Ya Hadiza tayi tace
"Maza tashi ki rakashi."
Bin sa tayi ta sameshi yana sauka baranda din, sai da tayi da gaske ta cimmasa tayi masa adawo lafiya sannan ta koma aka dasa hira. Wajen magriba aka sallame ta, ta kirashi yace taje gidan Raudan zaizo ya dauke ta a chan.
Har wajen tara be kirata ba, kowa ya dade ya barta sai ita kadai da Raudan, kiran sa ta gwada yi amma har ta gama ringing be daga ba, sai ta barshi a matsayin yanayin wani abun ne. Shiru har goma ta kusa ta sake gwada kiransa wayarsa a kashe, mamaki ya kamata dan bata zaton zai rasa charge a wayarsa, kira ta cigaaba da yi amma still a kashe har hankalin ta ya soma tashi, ta fadawa rauda shiru Abdallan har yanxu, gashi bata da number kowa a gidan bare ta kira, tunanin tafiya kawai tayi tace ma Raudan zata tafi, ganin dare ya soma yi sai ta fad'awa mijinta yace tazo ya kaita kawai, ta fito suka tafi duk tana jin babu dadi.
***Kiran G-boy yayi bayan ya dawo daga majalisar da yaje sukayi magana, ya gama abinda ya saka shi sai jiran result dan ba zai iya cigaba da jira ba, he wants his wife back, ko a mutu ko ayi rai be damu ba, kawai dai asma'u ta dawo wajen sa, he can't take any chances da zata kubuce masa har abadah. Gaba daya baya right senses dinsa, kansa yayi masifar kullewa baya ganin komai da kowa sai ita kadai.
RM
Page 50
*** Manyan motocin yan sanda ta gani acikin layin nasu, shi kansa mijin Rauda sai da yayi mamakin taruwar su a wajen duk da dare ne, tasowa wani daga cikin masu tsaron karamin gate din yayi yana haska motar da touch light,
"Wajen wa zaku je?" Yace yana sake dalle su, ta bayan sa ta hange shi a tsaye yana magana da wani babban mutum, daga gefen sa Baba Alhaji ne sai wasu mutane uku masu farin kaya,
"Me yake faruwa?" Ta ayyana a ranta tana jin mijin Rauda nayi musu bayanin Asma'un dake baya
"Kiyi hakuri Hajiya ban gane ki bane." Yace mata yana bud'e musu gate din, a dan gaban su yayi parking duk suka bi motar da kallo, ta bud'e kofar ta fito tana masa godiya. Rik'e kansa yayi da yake masa wani irin ciwo, ga kalleta da shanyayyun idanun sa da suka rine suka zama ja saboda bacin rai, be manta da ita ba kwata-kwata amma kuma a dan wanna takin ya manta da komai har ita kanta dan be sake tuna tana jiran sa ba, da saurin ta ta shige cikin gidan, sai ta samu harabar gidan har taso tafi wajen cika da mutane, bata gane komai ba, tunda maza ne dukkan su bare ta tsaya tambayar su, maimakon taje part dinta sai ta zarce nasu Amira, ta shiga da sallama sai dai duk suna zaune jigum jigum kamar wadanda akayi ma mutuwa haka ta tarar dasu, a sanyaye ta zauna tun daga farkon falon ta gaishe da su Mami wanda ta amsa mata a wani yanayi abunda ya sake tsorata ta, ta gasgata lallai babu lafiya a al'amarin. Zama tayi duk sukayi jigum jigum babu me magana a ciki. Suna zaune Baba Alhaji ya shigo duk sukayi kansa
"Ya ake ciki?" Mom tace kafin kowa yayi magana.
"Babu wani gamsasshen labari har zuwa yanzu, abu daya muka samu labari shine DSS ne suka tafi dashi, yanzu abinda ya rage a samu communication da su chan DSS office din, idan har hakan zai yiwu a daren nan Abuya zai samesu, kinsan basa wasa da aikinsu ba zasu bamu wata dama ba har sai sun gudanar da bincike akai, amma koma menene muna da yakinin shiri ne, anyi hakan ne dan a tarwatsa rayuwar Abuya, tunda a motar sa aka samu wayar da sauran makaman. "
" Innalillahi wa inna ilaihi rajiun. " Suka hada baki wajen fad'a ita da Mami, sai kuma suka koma suka zauna Baba Alhajjn ya sake fita.
Kan Asma'un ne ya daure jin an ambaci waya da kuma makamai kuma a motar Abdallah, bata san wa zata tunkara ta samu karin haske ba, gashi tana da bukatar sanin ko kad'an ne daga cikin abinda ya faru.
" Ku shiga dakin su Amira Husna, babu abinda zai faru in sha Allah sai alkhairi. "
Mami tace tana ganin kamar zaman nasu a haka zai takura Asma'un, tashi sukayi tare da Ihsan suka shiga dakin nasu, hakan ya bata damar tambayar su abinda yake faruwa.
" Ya Mudan ne aka kamashi, wai an samu waya da bullets a motar da yake ciki, wayar sukayi tracking shine suka kama a motar sa yana hanyar zuwa katsina da Baba ya aike shi, ana zargin sa da kaiwa masu hari makamai wai kuma da case din kidnapping, kuma babu wanda yasan a yanzu yana wanne hali. "
"Subahanallahi! " Tace tsoro na cikata, tasan illar case da DSS kuma takan ji labarin yadda suke aikwatar da aikin su akan duk wani me laifi, idan har za'a samu wadanda abubuwan a motar Abdallan ta to tabbas wanda yake son ganin bayan sa ne, bata yi tunanin yana da wani makiyi na kusa ko na nesa haka ba, yanayin halin sa be yi kama da na wanda haka kawai wani zai daura masa karan tsana ba, dan bashi da aibu ko kad'an shi din mutumin kirki ne kuma me nagarta.
Suna zaune a dakin kowa yayi tsit text message ya shigo wayarta, ta duba a tunanin ta ko Abdallan ne sai taga bakuwar number, ta bud'e ba tare da ta maida hankali sosai wajen karatawa ba, sai da ta gama rufe kafafunta da take jin sanyi sanyi na shigar ta sannan ta kalli wayar,
_" You belong to me!"_
haka tagani a text din, ta sake duba number din taga ba na Abdallah bane, sai kawai ta share ta barshi a matsayin wrong number ne, ta kifa wayar ta dora kanta a saman gadon.
Turo kofar akayi bayan an yi knocking sau uku, ya zuro iya kansa yace ta taso su tafi, tashi tayi tayima su Amira sai da safe bata samu kowa a falon ba sai kawai suka wuce be ce mata uffan ba, yanayin tafiyar sa ma ta nuna kadai halin da yake ciki na rashin kuzari da nutsuwa, sai da yaje kofar shiga sannan ya tsayata ta karaso ya bud'e mata kofar ta shiga sannan shima ya shiga. Kai tsaye bedroom ya zarce tabi bayansa da sauri kafin ta karasa har ya jona system dinsa a jikin socket yana kokarin kunna ta, ta shigo. Kallon sa tayi shima ya kalle ta da rinannun idanun sa, da sassarfa ta isa gareshi ta rungume shi, tana jin sanda ya ja gauron numfashi ya kankame ta tashin hankalin sa na raguwa.
"Babu abinda zai faru dashi in sha Allah, kayi masa addu'a Allah zai wanke shi daga zargin da ake masa, kuma koma waye Allah zai tona masa asiri."