← Book details Rayuwar Mace Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 66

Sashe 21

Rayuwar Mace Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Ga Asma'un nan a tambaye ta ai, idan ba hakan ne ya faru ba, dan har Umman tasu nayi wa maganar amma ta nuna ko in kula akai, kuma da kaina na tambayi Asma'un ko Adam din ne ya sakata faduwa amma tace min a ah, duk wannan abun Adam yayi hakuri ya zauna a haka da ita, amma shine har Umar yana da damar da zai shiga har gidan sa ya dake shi, saboda ya taba yar gwal. "

" Ko akwai hukuncin duka a musulunci? Irin wanda Adam din yayi wa Asma'u?"

Juya zancen tayi zuwa wani daban, Abba ya girgiza kai yana cike da mamakin Maman.

" Toh duk ba wannan ba Asabe, kinsan a sanadiyyar dukan da Adam yayi wa Asma'u har da barin ciki da tayi? "

" Ciki? "

Tace tana zaro ido, sai a lokacin ta kalli Asma'un, sai tsoro ya kamata ganin yadda fuskar Asma'un tayi, tana masifar son jikoki dan bata da su, musamman ta bangaren Adam din, amma shine har akayi cikin har ya zube bata san dashi ba, da ta san dashi ko kuda ba zata taba bari ya hau kan Asma'un ba, bare har wani abu ya sameta. Tayi nisa a tunanin ta, duk basuyi aune ba, sai tsinkayar muryar Adam din sukayi a tsakar kansu, muryar sa cike da izza da rashin mutunci yake furtawa

"Na saki Asma'u saki uku!"

Wani irin zillo Hajiyar tayi ta rafka salati tana kwala kiran sunan sa, tuni har ya suri takalmin sa yayi hanyar barin gidan, duk suka bishi da kallo Abba ransa fes, fuskar Umma tamkar gonar auduga, ita kuma Asma'u hawaye ne ya gangaro mata a saman kuncin ta, ba wai hawayen bakin ciki bane, hawaye ne kawai da ba zata iya tantance na menene ba, ta dai ji sun zubo mata kawai.

"Alhamdulillah." Abba yace daga zaune,

"Allah ya ga niyyata ta son karfafa zumuncin mu Yaya duk da sanin waye Adam da irin halin sa, amma na dauka cewa Adam da Umar duk nawa ne, kuma hannun ka baya rubewa ka yanke shi ka yar, ki gafarce ni idan nayi miki ba daidai ba, itama Asma'u tana da hakki akaina a matsayin ta na yata, na bi mata hakkin ta kar Allah ya kamani da hakkin ta ranar gobe kiyama. "

Wani abu ne ya daki Maman, ta kasa motsa ko da yan yatsun ta ne daga wajen, tana ji tana gani suka tashi dukkan su, sukayi wa tsohon sallama suka fice. Da k'yar ta mike ta fito sai ta tarar babu motar da suka zo, Adam tafiya yayi ya bar ta kenan, Nadeeya ta kira a waya bata daga ba tana wanka, sai ta shiga takawa a hankali zuwa titi, ta tsaida napep ta hau zuwa gida!

_ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_

_ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

_BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_

_KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._

_WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU  IN SHA ALLAH

_KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_

_SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_🥰

_BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍

_MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_🥰

_HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️

_NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍

***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_*

_BIYAR : DUBU DAYA (1k)_
_HUDU: 700_
_UKU: 500_
_BIYU: 400_
_DAYA: 300_

_AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE  MU TA: _

*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*

*KATIN MTN*👇👇

09166221261

______________________

ZAFAFA BIYAR

VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA)

VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA.

TWO PAGES DAILY
INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE.

*_TEAM ZAFAFABIYAR_*

*RM*

     16

***Suna isa gida suka tarar da Ya Hadiza tazo, yanayin da ta gansu ya sakata rage damuwar da ta tawo da ita, falon Abba suka wuce gaba daya, Asma'un ta kwanta su kuma duk suka zauna. Ajiyar zuciya Abba ya sauke bayan ya nutsu yace

"Toh dai kunga yadda Allah yake al'amarin sa, tun farko ba wai na aurawa Asma'u Adam bane dan bana son ta, babu iyayen da basa son yayansu kuma ba zan taba cutar da Asma'u ba, ina so ki saki jikinki, ki cire komai a ranki ki dauka hakan shine kaddarar ki, in sha Allah Allah zai kawo miki miji na gari ko dan hakurin da kikayi."

"Haka ne." Ya Hadiza tace tana kallon umma da taki saka baki

"Wai har yanzu fishin ne hajjaju?"

Abban yace wa umma yana son tabo ta

"Toh ga yayanki nan dai suna kallon ki, ku tayani bawa gimbiya hakuri Umar."

Dariya suka saka dukkan su har Asma'u, suka mike daya bayan daya suka fice Ya Hadiza ta tallafa mata zuwa dakin ta, tsohon dakin ta da ta tafi ta barshi ba tare da ta shirya ba.

  Suna fita umman ta mike itama tabi bayan su, Abba yayi murmushi kawai dan yasan halin kayarsa, fushi take dashi sosai amma yasan zata sakko ne. Fita suka sakeyi da Umar suka biya aka siyo wa Asma'un nama me yawan gaske, Abban yace ayi mata farfesu ta ci sosai sannan a sarrafa mata wani, Ya Hadiza ce tayi aikin kafin ta gama ma sai gasu Hidaya da Rauda kusan a tare, dukkan su da tsohon cikin su, tare suka zauna da ita har dare sannan suka tafi, suna tafiya bacci ya dauke ta dan dama ta gaji sosai ga ciwon kan da yaki barin ta.

***Sau biyu me napep na nanatawa Hajiya Mama an zo, kafin taji dan tayi nisa a kogin tunani, sauka tayi ta bashi kudin sa ta wuce zuwa cikin gidan, ta ja kafarta zuwa cikin falon da tunanin ganin Adam din a falon, baya nan babu kuma alamar ma ya shigo gidan, fasa zama tayi ta juya zuwa gidan nasa, ta kwankwasa kofar megadin sa ya bud'e, ya matsa da sauri ganin ta, ta wuce ciki ba tare da ta iya amsa gaisuwar sa ba. A kwance a falon ta tarar dashi yana waya sama-sama, cikin bacin rai yake maganar ta riski karshen in da yake cewa

"To hell with her."

Yaja tsaki ya kashe wayar, sai a sannan yaga Maman, ya kawar da kansa gefe a dole yayi fushi, bata zauna ba, daga tsayen ta kira sunan sa sai dai yadda sautin muryar ta, ya fita ya saka shi tashi dan ya ji fushi sosai a muryar tata

"Adam!"

Da ido ya amsa mata, ta nuna shi da da dan yatsa tace

"Ni ka watsawa k'asa a ido, a bainar jama'a? "

" Mah wallahi ba zan iya cigaba da zama a wajen nan ba, dan rainin hankali kina ganin yadda tsohon nan yake min wasu banzayen tambayoyi kamar dan jarida, Asma'un gwal ce? Da za'a dinga raina min hankali haka. "
Sakar baki tayi tana jin sa, ya cigaba

" Idan ma banda dai kaddara ni me zan da ita, taimaka mata fa nayi, kwantai tayi a gida na taimaka mata, shikenan sai ace za'a daga min hankali akai, babu dole ai dan ni dama ba wai ina son ta bane. "

" Adam! "

" Yanzu Adam ni kake kallo kake faffadawa wadannan maganganun? Duk abinda nayi maka a rayuwa? Yanzu har ni zaka iya wulakantawa a gaban mutane kayi saki irin sakin da yake mafi muni sannan ka taho ka barni. "

" Raina ne ya baci, su je su jika yar tasu su sha, idan ta rube musu a gida su suka jiyo, mtsw! "

Dauke shi tayi da mari, mari me karfin gaske, rik'e wajen yayi cikn tsananin mamaki, Mama ce yau ta mare shi, abinda bai taba faruwa ba a kaf rayuwar sa, akan wata banza, akan wadda be taba dauka a cikin jerin mutanen da suke da muhimmanci ba.

"Bansan baka da mutunci ba wallahi sai yau, nayi dana sanin barin ka da nayi haka sakaka, dama duk abinda ka fada min akan Asma'u karya kayi mata, ka saka na musgunawa yar mutane saboda farin cikin ka, karshe ka dake ta, dukan da yayi sanadiyyar zubewar gudan jininka, amma ko gezau baka ji ba!? Baka ji komai ba?"

"Ni tun chan dama bana bukatar haihuwa, it's too early ni ban shirya hayaniya ba, yara stress ne kawai, da damuwa su ishi mutum. "

Saura kiris ta fadi daga tsaiwar da tayi, ta rik'e gefen kujerar da take kusa da ita, bakin ta ya kasa sake furta komai saboda kaduwa, haka tayi sakaci? Haka tayi sakaci da rayuwar Adam har ta lalace haka? Ashe shima namiji kamar mace kana bukatar jajircewa wajen tarbiyyar sa, kamar yadda zaka kula da mace a tsare mata mutuncin ta haka da namiji ma ya kamata kayi masa? A tunanin ta babu wani abu da yake tsakanin iyaye da yaran su maza, musamman iyaye mata basa iya tsawatarwa yayan su maza da zarar sun kai wani lokaci, sai a sake su da tunanin duk abinda namiji yayi ado ne, hakan shine silar gurbacewar al'umar mu, domin namijin shi ne zai dawo ya fara bata rayuwar yara matan da aka tsare aka kare!

   Zagaye kujerar da take kai yayi ya fice daga gidan yana kunkuni, zuciyar ta, ta dinga bugawa da sauri, jinin ta nan da nan ya hau saboda bacin rai, ji tayi ba zata iya tashi ba, sai kawai ta zauna a wajen tana kokarin ganin ta samu daidaituwar zuciyar ta.
Chapter 21 · 0% Book details