Sashe 22
Rayuwar Mace Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wayar ta dake cikin jakar hannun ta, da ta dire a falon ta wuto gidan Adam din Nadeeya ta kira, sai taji ringing din a falo, ta taso tazo ta duba sai taga jakar, a tunanin ta Maman na daki ko ta shiga toilet, amma kuma shiru har lokacin yaja sosai bata fito ba, zuwa tayi ta kwankwasa jin shiru shiru ya sakata turawa ta gani,babu kowa a ciki, nan da nan sai hankalin ta, ya tashi ta shiga duba Maman lungu da sako a cikin gidan, ganin dai da gaske maman bata nan, duk kuma masu aikin babu wanda yaga shigowarta, kiran Adam ta yi, har ta karaci ringing dinta be daga ba, tana kokarin kiran Asma'u taji ko har lokacin basu gama bane, sai ga Maman ta shigo a cikin yanayin da ya tsorata su, duk sun yi cirko cirko tazo ta wuce ciki Nadeeya tabi bayan ta da sauri tana tambayar abinda ya faru.
"Nadeeya na cuci kaina, na cuci Karami na kuma cuci Asma'u da zumunci, ashe Adam shine bashi da gaskiya, kinga dukan da yayi wa yarinyar nan, ya kuma zubar da cikin da yake jikinta, cikin da na kwallafa rai nake dakon zuwan sa, ashe wai har yana da bakin magana, hmm."
"Subhallahi, gaskiya boy be kyauta ba, be yi adalci ba sam, daman ni nayi tunanin haka, saboda kusan abinda ya faru kenan lokacin da tayi rashin lafiyar nan, ban sanar dake bane amma Adam sai da ya kusan yi mata illa, dan kusan fyade yayi mata."
"Na shiga uku na, amma shine baki fad'a min ba? "
"Toh gani nayi ba wai abun fad'a bane, da kunya kuma tunda hakan sirrin su ne, babu ma kyau fadar, amma nayi masa fad'a sosai wallahi, yayi min alkawarin ya daina kuskure ne ma, shi yasa na kyale maganar ma."
Dafe kanta tayi da hannu bibiyu,
" Adam yayi asarar mace, yayi asarar mace daya tamkar da dubu, ya cuci kansa kuma sai yayi dana sani."
" Ya rabu da ita ne? "
" Saki uku yayi mata, sakin wulakanci,. "
" Ya Salam, ya Salam! "
***Wuni Maman tayi a daki, dan sai da Nadeeya ta dubata tayi mata bp dan jinin ta ya hau sosai, shi kuwa gogan ko sake waiwayo gidan be ba, a dole fushi yake da Maman akan ta mare shi, gidan Fido yayi tafiyar sa ya kwanta yayi bacci, yana farkawa ya ganta a zaune a gefen sa cikin yanayin damuwa.
" Lafiya?"
Yace dan har ga Allah ya bashi tsoro da farko. Takardar hannun ta, ta mika masa tana tabe bakin ta,
"Duba ka gani."
Karba yayi ya hau dubawa, be gane komai ba , ya mika mata cikin son jin ta mecece yace
"Ban gane komai ba, takardar menene?"
"Takardar ciki ce, I'm pregnant with your baby."
Wani yimm yaji akansa, ya daga ido yana kallon ta, kallon karki rainawa kanki hankali mana, itama kallon nasa take a dake, dan ta riga ta shirya komai ba zata taba jin tsoron hargagin sa ba.
"Ciki kuma, kamar ya?"
"Ciki dai ciki dai."
Mikewa yayi ya zabure
"You must be kidding, ciki ana zaune kalau, ta yaya kika samu ciki?"
"Ka fini sani ai."
"Kin ga... Bana son wasa please"
"Allah ba wasa bane, ciki ne dani kuma cikin ka!"
Chakumar wuyan rigarta yayi
"Ni zaki raina wa hankali? Wallahi karya kike kije tun wuri ki nemo ubansa, tun dare be miki ba. "
"Akwai ubansa da ya wuce kai ne, saki ne malam!
Tayi masa nuni da hannu, kin sakin ta yayi, ta fincike tana mikewa
"Ko kaki ko kaso wallahi kaine uban cikin nan, idan ma baka yarda ba toh, kanka, zan je in da za'a saka ka karba ta karfin gaske."
Kiranta ya dinga yi amma tayi masa banza tayi ficewar ta ta bar gidan ma, tsaki yaja ya mike shima ya fito, sai ya koya mata hankali sannan zata gane shi ba sa'anta bane, kuma ciki ba zai karba ba, dan be shirya daukar dawainiyar kowanne yaro ba bare ya takura masa ya hanashi more rayuwar sa, da zarar ka haihu shikenan sai duk tsufa ya kamaka, ina ba zai iya ba, idan ma tun wuri zata nemi uban yaronta ta nema ba sai dare yayi mata ba.
Mota ya shiga a fusace ya tada kura, ko gefen sa baya dubawa gudu kawai yake yi a cikin layin, duk wajen da yazo sai an kalle shi an kara kalla, masu Allah wadai nayi masu matsawa da sauri nayi dan har wani tsoho ya kusan zubarwa akan keken sa, kwana yazo zai sha wanda yayi daidai da fitowar su, suma zasu sha kwanar, yadda ya shigo da mugun guda babu horn ba komai ya sakasu kusan hadewa Allah ya takaita amma dai sai da suka taba juna.
Fitowa yayi a fusace, a dole an masa laifi yayi wajen motar yana zage zage, a dole an masa laifi, babu wanda ya motsa a cikin su, suna zaune daga motar suna kallon sa har ya karaso ya daki glass din gefen driver din, tint ne a motar shiyasa be iya ganin na ciki ba, hakan ya taimaka wajen sake kular dashi sosai, zuge glass din akayi, yayi masa kallon raini yace
"Malam haka ake tuki a garinku?"
"Ban sani ba." Adam yace a fusace
"Idan ka iya koyawa ai sai kazo ka koya min yadda ake yi din."
"MD let him be please, kasan bana son hayaniya, menene damage din da akayi masa, ya fad'a sai a biya shi."
A dage Adam ya kalli na gefen da yayi magana, ya watsa masa banzan kallo
"Kai waye da har zaka iya biyana,ko an gaya maka ni matsiyaci ne."
Wanda aka kira da MD ne yace
"Kai fa na lura kamar baka da aikin yi, mu bamu da lokacin batawa, idan zaka fadi abinda za'a baka ka fada, idan baka fad'a mu wuce."
"MD... " Ya kira shi yana saka masa ido
" Abuya, please ka bari mu kyale guy din nan, kasan sauri muke, yaci kansa kawai."
Daga haka ya daga glass din sama, ya take motar suka bar Adam a wajen tsaye yana zage zage, da kyar ya tattara ya koma wajen motar sa cike da haushin na gefen dan shi yafi bata masa rai dan yadda yake magana kawai ya lura dashi, hakan ya sake kular dashi, ya rike number din motar watarana zasu gauraya ko ba yau ba,sai ya nuna musu shi din gogaggen dan duniya ne na ajin farko!
Gida ya wuce kai tsaye, tun be karasa kofar gidan ba, ya hangi motar Fido a fake a kofar gidan su, wani irin wrong parking yayi ya fito da sauri, ya fad'a cikin gidan nasu jikin sa har rawa yake yi!
*RM*
*17*
***A durkushe ya samu Fido din a tsakiyar falon su tana kuka wiwi, daga gani bayani ta gama yi, wajen da Hajiya take zaune ya kalla sai yaga tana hawaye. Kan Fido din yayi gadangadan, ta mike da sauri tayi tsalle zuwa bakin Nadeeya da take tsaye cike da mamakin Adam din.
"Karka kuskura ka taba ta."
"Me tazo tace muku, wacce karyar tazo ta sanar daku?"
"Ka santa kenan ashe." Hajiya Maman cike da takaici, sai a sannan ya tuna tabargazar da yayi, da ya sani ya nuna be gane ta ba, a kada a raya yace shi sam be gane ta ba.
" Kina ina fiddausi."
" Gani Mama." Tace kamar ta kirki
" Kiyi hakuri dan Allah dan darajar annabi ki bar maganar nan, idan ta fito ba Adam ba, ni kaina na shiga uku, ki fadi ko nawa kike so zan baki amma ki tafi kiyi nisa sosai da nan, dan Allah na roke ki."
" Gaskiya ba zan iya ba, saboda ni ba yarki bace? Bayan shi ya bata min rayuwa ya raba ni da nawa iyayen sannan kice na hakura na tafi, ina zanje da ciki?"
" Toh a zubar, dan Allah ki taimaka min."
" Mah ya zaki tsaya kina bawa wannan yar iskar hakuri."
" Idan ka sake magana sai naci mutuncin ka wallahi, duk ba kai ka jawo min ba."
" Atoh, ni dai wallahi bansan yadda zan da cikin nan ba, ba zan kuma iya zubarwa ba, ko Adam ya karbi cikin sa ta cikin lumana ya yarda ya aure ni, ko na kaishi kotu wallahi."
Sai ta mike,
" Zan dawo gobe, kafin nan sai ku yanke abinda zai fi muku."
Ta harari Adam din, ya kai mata duka ta goce, kunya kamar zata kashe mama, ga takaici ga baccin ran abinda ya faru ga kuma wannan masifar, yanzu ya zatayi da wannan yarinyar? Daga ganin ta, tatacciyar yar bariki ce, ba abinda ya dame ta, bata ki ayi duk abinda za'a yi ba, dan babu kunya ko digo a al'amarin ta.
Tana fita ya dawo kan Maman zai yi magana ta daga masa hannu
" Bana son naji komai, kaje yadda ka ja ra'ayin ta babu wanda ya sani kaje ka roke ta, tayi hakuri ta zubar ko a bata kudi."
" Allah ya kiyaye walalhi, ita din banza, babu abinda ta isa tayi wallahi, karya take ni ban mata komai ba, ta san in da dare yayi mata dan babu shegen da zai sakani na karbi abinda ban yi niyya ba."
" Har ni!?" Maman tace
Kunkuni yayi, ya wuce ta rafka tagumi zafi goma da ashirin kenan, ina zata saka kanta ne taji dadi. Sakayyr da Adam din zai nuna mata kenan bayan duk irin gatan da ta nuna masa.
****Har suka karbi sakon suka bar unguwar MD be daina tsaki ba, gayen yayi masifar bata masa rai, dan dai Abuya yaki barin sa ne da sai ya gane cewa su ba sa'annin sa bane.
" Still dai baka hakura ba MD?"
Ya tambaye shi yana dora kansa saman kujerar motar daidai lokacin da suka shigo layin su
" Kana ganin fa yadda yake daga mana kai, shiyasa ni fa yanzu ban fiya son fita tare da kai ba, ka fiya hakuri wallahi, dani kadai ne da ya gane shayi na ruwa me."