← Book details Rayuwar Mace Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 66

Sashe 17

Rayuwar Mace Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Ka kyauta kwarai da watsa min k'asa a ido."

"Mah! Me kuma akace nayi?"

"Yanzu ka kyauta ka bar matar ka ita kadai ta kwana, bayan magiyar da kayi ta min akan na kyale ka, dama kawai ka shirya wulakanta ni shiyasa kayi haka ko?"

" Comman, yanzu mah kin yarda da maganar ta? Wallahi sharri tayi min, baki zo kin same ni a dakin ba? Bafa muyi bacci ba sai wajen asubah fa, ina zaton dai zafin ciwo me ko kuma kiyayyar da take min ce har yanzu bata hakura ba."

" Kiyayya?" Tace tana kallon sa

Juyar da fuskar sa yayi kamar wanda yake cikin yanayi yace

" Kwata-kwata bata kauna ta wallahi, babu yadda ban yi da ita ba amma tun auren taki sakewa dani, haka nake hakuri dan ko hakki na bata bani, wannan tsautsayin ma wai dan kawai nazo dakin ta shine ta tashi ta fita garin sauri ta zame a kafar bene ta fadi, amma kinga yan uwanta da kowa kallon ni ne me laifi, saboda ni aka sani me matsala."

" Haka take dama Asma'un? Ikon Allah!"

"Saboda ni ne me matsala shiyasa kowa laifi na yake gani, amma itama bata san ya kamata ba. "

" Bansan haka take ba, kallon mutuniyar kirki nake mata, ashe itama kwalla kanta ce, ai shikenan, duk da na zata laifin ka ne, ko wahalar musu da ya kake. "

" Ko daya, ni me ma zan mata na wahalar da ita? Ko fa gaishe ni batayi balle tayi min magana, dan dai ma Ina da hakuri ne wallahi. "

" Ah gaskiya bansan bata da hankali ba sai yau, amma babu komai zamuyi magana."

" Shikenan, amma dan Allah kar ayi mata fad'a, ni ba dan kin matsa ba da ba zan ma fad'a ba. "

" Sai ka zauna a haka? Bayan anayin aure ne saboda a samu nutsuwa da kwanciyar hankali. "

" Zata daina ne. " Yace yana mikewa

" Har sai yaushe? Zan same su ita da mahaifiyar ta ta dana lura itama haushi na take ji, zan fada mata komai sai ta fad'a min idan haka ake zaman aure a garin su. "

Kada kansa yayi, ya fice ransa fes, yayi shigewar sa gida yayi kwanciya sa sai wajen tara ya sake shiryawa ya fice abun sa. Da kwarin guiwar ta, ta isa asibitin dan tayi alkawarin yi wa umman magana ko ita da ita ne idan yaso sai ta nuna wa yarta gaskiya dan idan ba irin Adam ta samu ba babu me hakuri da hakan da tuni anji kansu. A yadda ta shigo dakin kadai ya saka Umma tunanin akwai wata a k'asa, ba kamar jiya da ta kasa sakewa ba, daga tsaye ta duba Asma'un ta fita wajen ta samu kujera ta zauna tana kallon masu shige da fice a asibitin, ta dade a wajen har aka soma zuwa, umman ta fito wajenta ta saka musu carpet babba tace Maman ta dawo, ba musu ta dawo ta zauna ta dubi umman da take hade kan kwanukan abincin jiya waje daya tace

"Magana nake so muyi dake ta fahimta."

Barin abinda take tayi, ta zauna kana tace

"Ina ji, Allah yasa dai ba wata matsala bace."

"Kusan hakan, amma dai ko kin tambayi Asma'u yadda akayi ta fadi?"

"Tsautsayi ne ai da yake kan kowa, ban tambaye ta ba gaskiya dan ban ga dalilin tambayar ba."

"Aikuwa akwai dalili, ya kamata ace kin bincika kinji, nidai na binciki Adam, kuma dai har ga Allah maganganun babu dadin ji, ban tsammaci hakan daga wajen asma'u ba. "

" Me ya faru? "

" Eh toh, Adam dai yace min zaman nasu babu dadi dan ko magana bata masa, gashi bata bashi hakkin sa na aure, wannan tsautsayin ma ya faru ne sanadiyyar yazo wajenta tayi niyyar barin dakin sai ta gamu da tsautsayi! "

" Kinga ai ba'a haka, miji daraja ce dashi duk kuwa da halin sa, ki hango ace da ba Adam din bane, da tuni ba zancen da ake kenan ba."

A tunanin ta umma zata ce wani abu, ko ta nuna rashin kyautawar Asma'un amma sai tayi kamar bata gane ba ma, tace kawai

" Allah ya rufa asiri."

Hakan ya kular da Hajiyar, ganin Umman na niyyar mikewa tace

" Iyakar abinda zaki ce kenan?"

" Toh me zance Yaya? Yaran yanzu ka haife su ne baka haifi halin su ba, kuma dai kinga halin da Asma'un take ciki ya kamata a daga mata kafa har ta samu sauki kafin a tuhume ta, a gani na hakan ya dace."

Shiru ya biyo bayan maganar Umman, Hajiyan ta rasa me zata ce,da n ta gane sarai magana Umman ta gasa mata me zafi, ganin bata ce komai ba ya saka ita kuma Umman tashi ta bar ta a wajen. Kwafa tayi cikin jin haushin ta bar asibitin, ba zata lamunci sakarci ba dole ta takawa abun birki.
Sosai umma taga son zuciyar Hajiyan fiye da ada ma akan batun auren, ko makaho ya shafa Asma'un ya shafa Adam din zai gane komai, amma saboda tsabagen son zuciya har mutum na kwance a gadon asibiti amma kazo da irin wannan maganar.
Tun ranar da hakan ta faru, Hajiyan bata sake lekowa ba, tana dai aiko da abinci kullum sau biyu a rana, Nadeeya ce kawai take zuwa kullum ba fashi amma shi kansa gogan sai ya ga dama yake dan lekowa fisha yayi gaba abin sa yana sake rura wuta a wajen Hajiyar tana jin zafin umma sosai tana ganin da saka hannun ta Asma'un tayi duk abinda tayi ma.
Satin ta uku a asibitin aka cire cast din da aka saka mata a hannun sannan aka sake mata x-ray aka tabbatar da yana healing sosai kuma very fast, gentle hand therapy aka cigaba da yi mata wanda aka fara tun kafin a cire cast din, hakan ya sake taimaka mata wajen samun karfin hannun har tana iya motsa shi sosai. Sallamar su akayi sannan aka basu appointment, Hajiya na jin an sallame su ta kira Abba ta sanar dashi gidan ta za'a kawo ta ba gida za'a wuce da ita ba, Abba yace toh ya kira umma ya fad'a mata a wuce da Asma'un gidan ta ko mijinta ya dauke ta kawai su tafi ba sai sun je ba, shiru umman tayi masa ya gama ya kashe. Dama ita bata ce zata tafi da ita gida ba tun da dai da mijinta. Gidanta suka fara kaita wanda Maman ta saka aka gyara shi kafin su dawo, shine zuwan umman na farko suka dan zauna zuwa azahar sannan suka tafi gida ita da Ya Hadiza da Abbati.
Suna tafiya ta tashi ta lallaba ta hau saman tayi wanka ta shirya, tana kokarin shinfida sallaya ne taji alamun an shigo kasan saboda babu motsin komai shiru gidan, ajiye sallayar tayi ta fito sai ta tarar da Hajiyar da kanta zaune a falon tana dan kallon gidan.

"Sannu da zuwa." Tace tana kasowa falon, ta tsuguna ta gaishe ta amma yadda ta amsa ya saka ta jin wani iri,

"Lafiya." Tace a yangace tana kalle kalle a falon, tayi zaton ko duba jikin ta, ta sake yi tunda ta jima bata zo ba sai aike amma sai taga akasin haka.

"Fad'a nazo yi miki tunda ita umman taku ta kasa ba zata iya ba, ni da kaina zan miki kuwa, kinsan hakkin miji akan matar sa kuwa?"

" Naam!? "

" Kin jini sarai, daidai gwargado ai kunyi karatu both na addinin da na bokon, kuma dai ke ba yarinya bace gasu Hidaya nan ai gaba kike dasu, amma ace ba zaki iya yiwa mijinki abinda yake so ba? Har sai yana binki kina butsarewa, duk da irin rokon da nayi miki na ajiye girma na? Ban zaci haka daga gareki ba. "

" Hajiya wani laifin yace nayi? "

" Laifi ? Laifufuka dai, babban laifi wanda ko a wajen ubangiji kin yi babban laifi, dan gayun nan dan tarairayar nan ace duk baki iya ba, kamar wadda ta fito daga kauye, kauyen ma kayau, lallai ki gyara kanki, ba zan lamunci shashanci ba. "

Sai ta mike tsaye

"Dole kiyi wa mijinki biyayya kiyi masa kuma duk abinda yake so, batun hakkin sa kuma ke da Allah wannan idan kika ki bashi. "
Chapter 17 · 0% Book details