← Book details Rayuwar Mace Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 66

Sashe 48

Rayuwar Mace Complete Hausa Novel · about 8 min read

***Dakin ta koma ta samu Rauda har tayi bacci, cike da tausayin ta, ta gyara mata gefen gadon dan daga gani baccin dauke ta yayi babu shiri, wajen kayan ta, ta nufa ta zauna tana rarrabe su tana hade wanda data hada waje daya, har ta kammala sannan tayi shafa'i da wutri taje dakin umma ta dauko katifa ta saka a k'asa ta kwanta ba dan tana jin bacci ba, tunani ta shiga yi, tana ganin komai tamkar almara, kamar ba ita ba, tasan a aji da komai Abdallah ya fita yayi mata fintinkau, bata taba kawo irinsa ko kwatankwacin sa a irin mijin da zata aura ba, sai dai kuma tasan komai hukunci ne na Allah, duk abinda Ya tsara shine daidai. Wato ita rayuwar baki dayan ta challenges ne, daga wannan sai wannan. Juyi ta dinga yi har ta samu bacci barawo ya kwashe ta, me cike da mafarkan Abdallah.

Da wuri Ya Hadiza ta kira Umma tace Asma'un ta shirya Amaryar Kb zata zo ta fara yi mata idan Abban ya amince, zuwa umma tayi dakin ta tarar da Asma'un a zaune tana tilawa, Rauda kuma na bacci,

"Umma ina kwana?" Ta gaishe ta bayan ta kai karshen shafin,

"Lafiya lou, Rauda bata tashi ba!?

" Komawa tayi, tace bata jin dadin jikinta ma. "

" Yanayin ne, ga watan haihuwar ne kinsan sai a hankalin, idan tana jin ciwo dai tayi magana. "

" In Sha Allah. "

" Ya kukayi dashi? Abban ku yana jiran feedback

"Ya bari, sati daya wai."

"Yayi ai, anjima kad'an Amaryar Kb din zata zo, sai ta fara, idan yaso juma'a sai ayi walima kawai."

Juyawa umma tayi, tace

"Anjima sai kizo ki sanar da Abban dan yanzu be tashi ba."

"Ok tam."

Fita umman tayi ita kuma ta cigaba da karatun ta, sai da tayi daya cif sannan ta ajiye ta fito zuwa kitchen domin taga abinda zai samu na breakfast kafin Rauda ta tashi dan wasu masu ciki akwai saurin jin yunwa.

Wajen tara da rabi Abba ya kirata, ya tambaye ta yadda sukayi ta fad'a masa, Madallah kawai yace ya fita, ta koma daki tana zama Amaryar Kb na zuwa, ta jiyo muryar bakuwa suna gaisawa da Umma ta tashi ta leka ta window. Rauda na toilet tana wanka umma ta kwala mata kira, ta tashi da sauri ta fita, ta gaida Amaryar Kb din ta amsa tana tsokanar ta dan ta gane ita ce amarya, dakin Umma aka kaita Asma'un na zaune a gefe ta hada komai da zata bukata a gefe, Sudanese Scrub/Dilka aka fara mata cike da kwarewa irin ta gogaggun wanda suka san ta kan gyara ciki da waje, ita kanta ta yaba yadda take aikin nata balle ga Rauda a gefe tana sake kurantawa, tun kafin ma a gama na ranar kamshi ya bad'e ko ina na dakin, zuwa gabatowar azahar suka gama lokacin Rauda ta tafi sai Asma'un kawai da Umma a gidan, sallama suka ji ana kwalawa, umma dake zaune a kujerar dake kan hanya ta amsa tana zura kanta waje, Nadeeya ce tare da Fadeela sai wata yar uwar su Abba da take zuwa idan ta bushi iska daga Sumailan take zuwa tayi musu kwana biyu ta tafi, tashi umma tayi ganin masu sallamar tana musu lalle da zuwa, kunya Nadeeya take ji tun sanda adam ya saki Asma'u kamar ita tayi haka take ji shiyasa bata taba iya sakewa da su musamman Asma'un da suke shiri amma yanzu ko doguwar magana basa yi, yanzu ma Hajiya Mama ce tace suzo su kawo Inna balkin daga nan sai ta samu damar magana da Asma'un, ta farko bata so ba amma ganin halin da Adam din yake ciki ta saka ta zuwa, dan akwai hakkin ta sosai akan adam idan bata yafe masa ba haka zai ta shiga masifu dan ta cutar dashi, yanzu ma a kwance yake asibiti tun da ya samu labarin auren Asma'un ya fita hankalin sa har suma yayi.
Tashi Asma'u tayi daga zaunen da take, suna shigowa tayi hanyar fita bayan sun gaisa dasu, dakin ta, ta shige tana jin wani sanyayyan kamshi na tashi daga jikinta, wayarta ta dauka ta shiga whatspp tana dubawa, yau be kirata ba tun dazu take dakon kiran nasa amma ko da ta dawo dakin ma ta dauka zata ga missed calls dinsa amma sai taga babu komai, gashi ita ba abin ta kirashi ba, kunya ba zata barta ba, cigaba da dakon kiran nasa ta yi tana fatan ya kirata nan kusa, kwala mata kira Umma tayi, ta tashi ta ajiye wayar ta sameta a waje

"Ki shiga wajen su, zakuyi magana da Nadeeya, ashe Adam din ma yana asibiti ba lafiya, Allah ya bashi lafiiya."

"Amin."

Tace tana shiga ciki, ta samu Nadeeya ne kawai da fadeela a dakin babu Inna balkin, tun kafin ta zauna Nadeeya ta soma mata magana

"Dan Allah Asma'u ba dan ni ba, dan Allah ki yafe ma Adam abinda yayi miki dan Allah, soyayyar ki zata haukata shi, he's insane har baya iya tantance daidai da ba daidai ba, nasa yanzu ke matar wani ce, ba kuma na miki fatan sake dawowa wajen Adam a karo na biyu ko da bakiyi aure ba, duk da ina da yakinin ya shiryu, amma bana miki fatan zama dashi. "

" Ba komai fa Allah Ya Nadeeya, ni ban rik'e shi ba, Allah ya bashi lafiya. "

" Ki yafe masa dan Allah,. "

" Na yafe masa duniya da lahira, Allah ma muna masa laifi ya kuma yafe mana, kuma Allah yana son mutum me hakuri da yafiya, ina masa fatan alkairi. "

" Nagode sosai Asma'u, hakika Adam yayi rashin mace ta gari, ina miki fatan nasara a dukkan al'amuran ki, ya baki zaman lafiya da zuria dayyiba, idan na samu time zanzo naga dakin ki. "

" Nagode sosai. "

Tafiya sukayi suka bar Inna balkin anan, daga nan asibitin suka wuce suka tarar da Adam din a cikin mawuyacin hali, Fido ce a dakin kawai mama taje gida ta dawo, bata kula su ba har suka zauna, ta cigaba da danna wayarta dan bata jin ko digon tausayin Adam din musamman da aka ce akan mace ne yake wannan ciwon, jira take kawai ya dawo gida ya fara cin ubansa dalla dalla a hannun ta, dan ta samu tabbacin aikin yayi kuma zai fara aiki ne da zarar ya gama ciwo ciwon son nasa. Turo kofar akayi, ta tashi ta taro su, su Faiza ne su uku, suka hau hayaniya a dakin kamar ba dakin mara lafiya ba, tashi fadila tayi ta fita, Nadeeya ta kalle su tace

"Ku dan rage muryar ku dan Allah, baa son hayaniya musamman shi da jinin sa ya hau, hakan zai hana jinin sauka."

Kamar wadda tayi magana da duwatsu haka suka maida ta, suka cigaba da shewa shewan su da hirar su mara amfani, ranta ne ya baci ta kalli Fido din tace

"Fiddausi ki kaisu waje su zauna baa son hayaniya akan mara lafiya."

"A matsayin ki nawa? Mijinki ko nawa? Ko dan kin tsofe a gida baa da aiki sai gantali a kwararo shine zaki min bakin ciki dan kinga ni nayi auren?"

"Ikonn Allah,."

"Ikon gaske, idan ta miki zafi sai ki kaini gaba. "

" Allah ya kyauta. "

Tace ta bar dakin da ba zata iya dasu ba, tana fita Hajiya Mama na dawowa tare da yar aikinta ta riko kayan abincin, a wajen ta ajiye kayan ita kuma Maman ta shiga dakin, babu wanda ya nuna alamun mutum ya shigo bare su daidaita kansu,

Matsowa tayi tana kokarin duba Adam din amma sai Fido din ta babbake wajen tana tauna cingam ta gefen bakin ta

"Fiddausi ya jikin nasa." Tace bayan ta matsa baya

"Gashi nan ai." Ta sake juya kanta gefe

Dan jim Hajiya tayi a tsaye, sai kuma ta juya ta bar dakin dan mugun shakkar yarinyar take ji, har bata iya yarda su hada ido sam, maganar ta samu Nadeeya da Fadila na yi, taki saka baki sai ma ta saka sallaya daga gefen su tayi zaman ta, su kansu sun gano bata son laifin Fido din ko kad'an, gashi ita kanta bata raga mata bare su.

***Kwana hudu da fara gyaran jikin Asma'u ta chanja, tayi wani irin masifaffan kyau, kamar ba ita ba, ga wani kamshi me sanyin dadi da ke tashi daga jikinta, ko gifta ka tayi sai kaji shi gwanin dadi, tun bayan zuwan da Abdallan yayi be sake zuwa ba dan ya gane zuwan nasa akwai matsala, sai dai waya da chatting da suke kusan raba dare suna yi, a yan kwanakin suka sake shakuwa da juna shakuwa ta ban mamaki.
Da safe yana shiryawa yaji ana danna masa door bell, sai da ya gama fesa turare sannan yaje ya bude ya tarar da Ihsan a tsaye har ta soma kosawa da jiran sa ta kuma san yana ciki dan motar sa tana nan,

"Ya akayi?"

"Anty faty ce tace idan ka shirya ka shigo ciki."

"Tazo ne?"

"Eh dazu tazo ita da Anty Asy."

"Ok zanzo." Ya maida kofar ya rufe, ya karasa shirin sa a tsanake sannan ya fito ya shiga gidan, tun daga shigowa ya hangi manya manyan akwatunan na alfarma a ajiye a gefe, sai wasu yan kwanduna masu kyau da akayi musu ado da purple kyalle, zama yayi yana kallon kayan, suka gaisa sannan Anty Faty tace ya duba kayan ne, anjima zasu je su kai da rana.
Chapter 48 · 0% Book details