← Book details Rayuwar Mace Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 66

Sashe 4

Rayuwar Mace Complete Hausa Novel · about 8 min read

***Tsaye Ya Hadiza take a kanta tunda ta shigo take kuka ta ki fad'a mata abinda ya faru, ita kanta ji take kamar tayi kukan dan ta san yanayin da Asma'un take ciki wanda ta taba shiga kusan irin sa Allah ya kiyaye Abba ya sakko aka daidaita, shiyasa take matukar tausayin ta dan mutum irin Adam ace shine mijinka ba karamin tashin hankali bane.

"Ki fad'a min abinda ya faru dan Allah, hankali na ba zai kwanta ba kuma wannan kukan sai ya saka miki ciwo."

Bayan hannun ta, tasa ta share hawayen sannan ta hau ciro hijab din jikinta saboda zafi da hucin da jikin ta ke fitarwa. Duk Ya Hadizan na tsaye akanta har ta cire ta ninke sannan ta hau kokarin kakalo murmushi ta dora a saman jar fuskar ta.

" Wani abu yace miki?"

Da ka ta amsa mata tana jin wasu hawayen na neman zubowa.

" Karki yarda ki biye wa maganganun sa dan irin Adam xasu iya karar miki da hawayen ki tas babu abinda ya dame su. He's not worth your tears, ki nutsu ki shiga kai wa Allah kukan ki, sai kiga komai yazo da sauki ta inda bamu zata ba."

" In sha Allah." Tace tana kwanciya.

     Fita Ya Hadizan tayi bayan ta kara bata baki, ta barta tana sakawa da warwarewa, ta riga ta san rayuwar ta tazo karshe, dan tana jin komai zai iya faruwa a zaman ta da mutum kamar Adam, bata san yadda zata kasance ba amma tana da yakinin zaman ba zai taba dadi ba.

    Shirye shirye ya kankama sosai a baangarorin biyu, ita Umma dai tana yin komai ne domin ya zama dole amma ba wai don son auren ba, sai dai bata da damar nunawa saboda Asma'un da Abba dan ba zata yarda ta bata kofar da zata bijire wa mahaifin ta ba. Satin ta guda ta dawo gida a lokacin ne aka shiga yi mata yan gyararrakin mata na al'adah duk da ba wani zafafawa akayi ba amma kuma dole dai zaka yi auren 'yarka ka dan tabuka wani abu ko yaya.
    Komai baya mata dadi duk abinda ake mata kawai tana bi ne don babu yadda zata yi, saukin ta ma tun da yazo gidan Ya Hadiza be sake dawowa ba, sai magana da yayi mata a whatspp akan abinda take bukata tace babu, sai missed video calls dinsa da ta gani sau biyu bata bi ba, shikenan shima be sake bin kanta ba dama Nadeeya ce tace masa ana tambaya shiyasa ma ya tambaye ta, abinda tayi masa ranar yayi masifar bata masa rai shiyasa ya tattara ya watsar da ita ya cigaba da shirye shiryen sa dan babu fashi a auren dan yadda yake ji idan be aure ta ba akwai matsala.

Saura sati daya bikin suka kawo lefe, akwatuna goma cif masu kyau da tsada, tun daga nan hankalin ta ya kara tashi sosai, ta yarda da gaske dai auren babu fashi, babu abu daya da ya burgeta a kayan dan bata son duk wani abu da ya danganci Adam din, sosai take jin tsanar sa. Bayan an karbi lefen kowa ya watse su Ya Hadiza suka zauna zaman yi mata nasiha dan idan aka shiga satin bikin babu me sukunin zama yayi mata, jin su kawai take dan duk abinda suke fad'a bata jin zata iya yin guda daya, ita dai kawai ta riga ta san zatayi aure ne dan biyayya ga mahaifin ta.
    Da daddare kafin duk su watse sai gashi ya zo, gabanta ne ya fadi da taji Areef yace yazo, duk suka zuba mata ido tayi saurin zamewa daga zaunen da take ta kwanta kuka na taso mata.

"Tashi zakiyi kije, kiyi hakuri." Ya Hadiza tayi maganar tana mikewa, tashi tayi daga kwanciyar, ta ja hijab dinta dage gefe zata saka ta girgiza mata kai

" Musulunci ma ya halatta mishi ganin wani abu sashe na daga gareki, ki saka mayafi dan Allah, sai ki dauki Hibba kuje."

Bata yi mata musu ba, ta ajiye Hijab din ta karbi mayafin dake jikin kanwarta Rauda ta yafa, ta rik'e hannun hibba din suka fita, already ya shigo yana falon Abba shi da Abbaty da Yaya Ibrahim. Da sallama ta shigo duk suka juyo suna kallon ta, sannan suka amsa, murmushi yayi mata tayi kamar bata gani ba, ta samu gefe chan ta zauna sai suka tashi suka fita ya zama daga ita sai shi sai Hibba da ta makale a kusa da ita dan tana da kiwa. Tsam ya taso daga wajen zaman sa ya dawo kusa da ita, har tana jin kanshin turaren sa sosai, bata dago ba ta gaishe shi ya amsa yana bin ta da mayen kallon sa, riga da skirt ne a jikinta simple dinki amma tayi kyau sosai, fuskar ta fayau babu hoda sai yar rama da tayi akan ranar da ya ganta a kitchen.

"Fine baby, ya sunan ki?" Ya mika ma Hibba hannu ta noke yayi murmushi

"Madam ya gida?"

"Madam?" Tace a ranta

"Lafiya lou." Ta amsa tana mummuraza yan yatsun hannun ta. Kallon hannun yayi, ya kai nasa hannun ya kama tayi saurin janye wa a tsorace ta kalle shi, a lokacin ta lura da shaddar dake jikin sa an masa karamin dinki iya guiwa kansa babu hula ya rage gashin sa sosai.

"Menene haka? Kamar kin ga wani dodo." Ya tambaya cike da mamakin ta

"Ka daina taba ni." Tace kai tsaye tana kokarin tashi daga kujerar yayi saurin fizgo mayafinta yana zaro mata idon sa.

"Me kike nufi? Aure fa zamuyi? Me yasa kike behaving kamar baki san yadda rayuwar ta zama bane, bana fa son kauyanci."

Kallon sa tayi cike da mamakin sa, ta lura akan rayuwar da yake so yake ganin daidai ce nan da nan zaka ga fushin sa, ita kuwa ta gwammace duk abinda zai fad'a ya fad'a fushin sa ba komai bane akan fushin ubangiji. Tana jin sa ya cigba da gaggasa mata magana san ransa, tayi biris kamar ba da ita yake ba, tana da yakinin zafin zuciya ce dashi, kuma bakin sa bashi da control wejan gasa magana. Sai da ya gaji don kansa yayi shiru yana jan tsaki. Ya zaro wayar sa ya hau kira yana cigaba da huci akan kawai ta hanashi taba jikinta.

"Babe where are you?" Yace bayan an daga wayar

"Ok I'm on my way." Ya kashe kiran ya mike yana kallon ta

"Ba zan yi tolerating kina hana min abinda yake nawa ba, ba zan sake dawowa ba idan an kawo ki gidan zaki ga yadda zanyi dake."

Daga haka ya juya yana taku dai-dai yayi ficewar sa, be ko yi sallama da kowa ba ya kama gabansa sai gidan Fido, daga chan ya wuce wajen abokin sa ya karbi wasu kaya sannan ya wuce gida.

Tun ranar da ya tafi bata sake jin duriyar sa ba, Hajiya Mama dai tazo sau daya da maganar yadda bikin zai kasance tunda duk abu daya ne bangaren ta da na Abba, umma dai bata ce komai ba, duk abinda suka tsara suka yanke ita bata da ta cewa dan ko da tace din ma ba lallai suyi amfani dashi ba. Daga haka aka shiga satin bikin.
Ranar laraba aka je akayi kafi, gidan yayi kyau sosai sama da k'asa sai parking space, a jikin gidan Hajiya Maman yake dan katangar su daya, dama tace ko Adam zai yi aure yana tare da ita bata so yayi nisa ko kad'an, balle kuma da zai auri Asma'un sai take ganin ai shikenan ma dama Asma'un ikon ta ce itama. Alhamis aka shiga bikin gadangadan, gidajen biyu ko ina biki ya kankama Hajiya Mama dai saboda yawan mutanen wasu sai dan karamin hotel hotel din dake bayan gidan aka kama musu musamman abokan Adam din da sukayi karatu a turai tare suka zo daga wasu states din.

It's better to marry late than to marry wrong! (Kamar haka dai bature yace, na manta dai.

Don't marry out of desperation dan aure ya wuce duk tunanin me tunani!

_ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_

_ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

_BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_

_KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._

_WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU IN SHA ALLAH

_KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_

_SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_🥰

_BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍

_MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_🥰

_HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️

_NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍

***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_*

_BIYAR : DUBU DAYA (1k)_
_HUDU: 700_
_UKU: 500_
_BIYU: 400_
_DAYA: 300_

_AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE MU TA: _

*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*

*KATIN MTN*👇👇

09166221261

______________________

ZAFAFA BIYAR

VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA)

VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA.

TWO PAGES DAILY
INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE.

*_TEAM ZAFAFABIYAR_*

https://arewabooks.com/chapter?id=628b84d5aed642354ddce302

RAYUWAR MACE*
_Hafsat Rano_
Free Page (4)
Chapter 4 · 0% Book details