← Book details Rayuwar Mace Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 66

Sashe 42

Rayuwar Mace Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yace mata yana nuna mata gefen sa bayan ya zauna, ba musu ta karasa a nutse ta zauna da dan tazara kad'an a tsakanin su, matsowa yayi ya jone da jikinta har kafadarta tana gogar tasa, hannun ta ya lalubo ya rik'e cikin nasa yana dan murza su a hankali, yanayin bugawar zuciyar ta ya sauya nan take, ta dinga jin wani irin yanayi da bata taba fuskantar sa ba. Ta zata wata magana xasuyi amma sai taji shiru har ta dago da niyyar ganin abinda yake amma sai taga kawai ita yake kallo kuri, duk sai taji kunya amma shi ko a kwalar rigar sa., Sai ma sake tsattsareta da yayi yana kokarin lallai sai ya saka idon shi cikin nata, sun jima a haka kafin yayi ta maza ya daure ya cikata yana mikewa

"Bana so na tafi, but i have to, kar Abba yaga rashin hakuri na."

Shafa kansa yayi ya mikar da hannun sa zuwa gareta, ya mikar da ita tsaye suna fuskantar juna

"My wife."

Ya kawo fuskarsa daidai tata ta hanyar rage tsawon sa, dan tsaf zai sakata a cikin rigar sa ya boye ta, dago idon ta, tayi da niyyar kallon sa, sai yaga kamar tayi masa fari, wani yarrr yaji tun daga kansa zuwa tafin kafarsa, bakin sa ya kai kuncin ta s kasalance ya manna mata kiss, ta duka da sauri tana damke idon ta

"Ki kula min da kanki kinji?"

Bata iya amsawa ba sai daga kai da tayi alamar toh, cikin sakannin da basu gaza goma ba ya fice fit daga falon dan abinda yake ji zai iya sashi aikata abun kunya. Yana fita ya tarar da driver yana jiran sa, MD ya tafi shine ya kirashi yazo ya dauke shi, babu bata lokaci ya fad'a bayan motar ya ja suka bar layin.

Tamkar wadda aka dasa a wajen haka ta kasa ko da daga kafarta ne, wani feeling me matukar dadi ya dinga mata yawo, soyayyar sa me sanyi da tsayawa a rai, bata taba experiencing hakan ba, baa taba nuna mata so irin haka ba, shiyasa take jin ta kamar wata bakuwa, kamar wadda aka chanja ta da wata ta daban. Da k'yar ta ja kafafunta zuwa cikin gidan nasu, kunyar Umma da Abba na sake dabaibaye ta. Idon Umma fes akanta ta shigo, sai taga kamar umman ta kara mata haske akan hasken ta da ta Santa dashi, bata sani ba ko tsantsar farin cikin da ta hanga a cikin idon ta ne ya sakata ganin farin nata ba, zuwa tayi ta zauna a gefen Umman tana jan mayafin jikinta ta sauke shi k'asa.

"Umma ina Abba?"

"Ya fita sallah, inaga ko ya tsaya wajensu liman."

Sai kawai ta fad'a jikin Umma, ta dora kanta a kafar umman ta runtse idon ta, tana tariyo abinda ya faru yanzu.

"Nasan ba dan dare ba, babu abinda zai hana yan uwanki zuwa, amma nasan gobe da wuri zaki gansu, dan duk munyi waya kowa murna wallahi."

"Umma wai ya akayi haka ta kasance?"

"Al'amarin Allah fa, ke dai ki bar sha'anin aure wallahi."

Maida idon ta, tayi ta kulle tana jin yadda Umman take yabon abun, tana kuma kwararo addu'ar dacewar Asma'un da fatan nasara a komai ma, a ranta take amsa amin, tana saka ram samun nutsuwa da Abdallan, wanda a yanzu take jin kamar ya karbe rashin ta ya tafi dashi, kamar akwai wani gagarumin abu da take jin tana kewa. Daina jin maganar Umman tayi sai sama-sama, ta fad'a tunanin shi da hoton fuskar sa, sajen sa da quarter million dinsa shi yafi komai tafiya da ita. Samun kanta tayi tana murmusawa, ta mike daga kan kafar Umman ta fad'a daki yadda zata more tunanin shi sosai ba tare da wani abu ya katse ta ba, wayarta ta jawo da nufin kiran Rauda ta tarar da missed calls da yawa sai text message dinsa guda biyu, budewa tayi tana fadawa saman gadon idon ta kyam akan wayar dadin kamalan na ratsa ta

_"The first time we met, I can see that you and i are meant to be together... Your eyes were so gentle, your smile so true... You walked lightly into my heart, captivating and lovely to my mind. For you are my heart, my soul and my oneness. With you i know that I will find my completeness,my eternal peace of mind. You are the one I want to spend my life with. Both of our hearts will forever bond into all happiness, falls, pains and sorrows. I promise together we will meet tomorrow. I love you so much my wife."_ #

Juyi ta dinga yi a saman gadon ita kadai kalamansa na ratsa ta, wayar da ke saman kirjinta ta yi kara, ta dan zabura kadan dan tayi nisa a tunanin, Rauda ce, dagawa tayi cike da zakuwa tace

" Rauda."

" Wayyo...Yaa Asma'u."

"Wallahi da k'yar zan iya bacci yau, kinji yadda nake ji kuwa? Farin ciki kamar na ganni a gida wallahi,dan ma Umma tace kar muzo ne da tuni nazo

"

" Yau da goben duk daya ai, idan da rai da lafiya."

" Haka ne,ya kika ji? Nasan ya hadu ba karya wallahi, irin wanda ya dace dake ba wanchan ya Adam din ba, fari kamar farin kosai. "

" Ke ko? "

" Allah kuwa, dan Allah kice ina gaishe shi da kyau da kyau, da wuri zan faso goben nan ba zan tafi ba sai na ganshi. "

" Kyaji dashi dai, kije ki kwanta ki huta kinga ba ke kadai bace. "

" Tom, sai da safe.*

"Yawwa, sai da safe."

Tasan da wuri duk zasu zo, shiyasa ma ta katse Raudan sun hadu gobe ayi duk maganar ma da za'a yi, Hidaya ta kira nan ma sukayi magana sannan ta kira Ya Hadiza, ita ce ma suka dan dade suna magana, har ta soma mata maganar gyaran jiki da duk abubuwan da ya kamata, ita dai jin ta kawai take bata ce komai ba, daga karshe sukayi sallama tace sai tazo goben.

RM
   32

***Kansa ya daga bayan motar ta paka a harabar gidan nasu, akwai alamun hadari a garin yadda iska me dadi take kadawa, taune bakin sa yayi yana zura kafafunsa wajen, sai a lokacin yaga motar Aunty Fati daga gefen sa, fitowa yayi yana nazarin harabar gidan, kansa tsaya ya wuce cikin gidan ya haura corridor ya tura kofar, ji yayi an watsa masa abu a jikinsa,

"Congratulations 🎉."

Suka hada baki wajen fad'a, daya bayan daya ya dinga bin su da kallo, su hudu ne cif sai MD dake bayan su yana dariya, Aunty Fati ce ta fara mika masa flower sai Aunty Asiya ta bi bayanta, ta mika masa tana masa dariya, Amira da Ihsan ne a karshe

"Congratulations Yah."

Suka fad'a a tare, murmushi ya dinga sakar musu daya bayan daya, daga nan suka dunguma zuwa cikin falon in da Mom da Ammi ke zaune a kujera daya, wajen su ya karasa cike da matsananciyar kunya, ya duka yana gaida su, kowannen su farin ciki ne kwance a fuskarsa, cikin yanayin da ke nuna tsantsar farin cikin su.

"Ango kasha kamshi, baku ji wani kamshi ba wai da ya shigo?" Aunty Fati tace tana zama a hannun kujera kusa da Mom

"Irin dai kamshin ango." Asiya tace suka saka dariya,

"Sai muka ji daurin aure, saukinta ma akwai enough time na shirya komai, biki zamuyi irin wanda baa taba irin sa ba."

"Ai sati zamuyi Muna biki Aunty Asy."

Wani kallo ya watsa ma Ihsan din irin na waya saka dake, ta gimtse bakin ta, tana shiga taitayinta, dama ta zata yau daya dai zai bar su su dan sakata su wataya amma sai gashi yana ankare da ita tayi magana. Ganin haka ya saka Amira tsuke bakinta itama ta bar aunty Asy da Aunty Fati suke mishi maganar tunda sune daidai shi, duk abin nan yaki magana sai murmushi kawai yake idan sukayi magana, sun san dama ba yi zai ba, dan ma MD ya kwashe komai ya fesa musu da irin yadda yake narkewa a gaban Asma'un kamar bashi ba, dan har sun fara tausaya mata saboda miskilancin sa, ashe ashe ita ba haka yake mata ba.
   Lallabawa yayi ya gudu ya barsu suna ta fama, ya rage kayan jikinsa ya zauna yana jawo wayar sa, yayi broadcast message ga dukkan mutanen da yake ganin sun chanchanta su san da maganar auren nasa ya tura musu, sannan ya kashe layin dan yasan zasu kikkirashi. Baya jin rage ayyukan sa a yau, wata irin kasala yake ji da son kasance tare da ita, ko da ya dauko system din sai ya gagara komai, ya rufe ta ya ture gefe yana mike kafarsa ya jingina da jikin kujerar, sha daya da rabi saura yan mintuna ya duba agogon dake jikin allon wayar sa, Private layin sa da ba kowa ya san shi dashi ba sai family members yayi amfani wajen kiranta dashi, tana kwance rigingine tana duba sakonnin whatspp din ta wanda yawanci group din sai na Adam da yake mata kusan kullum sai uku ko biyar bata ma budewa sun taru sosai, shiga kansu tayi tayi marking ta goge su dukka sannan ta jefa lambar tasa a block list, ta koma wajen call log nan ma tayi blocking dinsa. Zata fita daga kai kiran ya shigo, ta duba time taga kusan sha daya har da kusan rabi, haka kawai sai jikinta ya bata shine dan babu me kiranta a wannan lokacin, dagawa tayi tana dan karata a kunnen nata kamar me tsoron abinda zata ji, muryar sa ta tsinkaya a cikin wayar yana mata sallama cikin tausasa lafazi,

"Baki bacci ba?"

"Umm?"

"Kina jiran na ko?"

Dunkulewa tayi waje daya daidai lokacin iska ta kad'a alamun tasowar hadarin gaba daya, wani sanyi ya shigo ciki ya iske ta, hade da wani irin mixed feeling akansa

"Tell me, me ya hanaki bacci?"

"Ba komai."

"Ba wani, tunani na kike ko?"

"Um Um." Tace ta k'asa bud'e bakin tayi magana

" Then tell me, me ya hanaki bacci."

"Kawai yaki zuwa ne?"

"Ni na sani, tunani na ya hanaki bacci,

"Kinga message dina?"

"Na gani."
Chapter 42 · 0% Book details