Sashe 20
Rayuwar Mace Complete Hausa Novel · about 8 min read
" Ok." Yace yana juya motar zuwa hanyar teaching hospital din garin. Tun da suka dauki hanya Abba yake waya, wanda umma ta fuskanci ransa yayi kololuwa a baci, dan duk a fusace yake maganar karshe ya kirawo Ya Hadiza ya sanar da ita umman naji, dan ita ko kiran kowa a cikin su batayi ba saboda bakin cikin da take ciki.
Asibitin Abba ya saka aka sake duba masa Asma'un sosai aka kuma tabbatar masa da babu cikin ya fice idan kuma taji wani abu daga baya sai ta dawo a sake dubawa, magungunan ta da aka bata likitan ta gani ta chanja mata wasu sannan ta ce zasu iya tafiya.
Har sun mike tsaye, sai Abban ya tsaya yace wa likitan yana bukatar ayi wa Asma'un gwajin jini, ta rubuta musu tace aje lab, akaje aka biya komai aka dauki jinin nata akayi mata dukkan tests din da suka shafi HIV, Hepatitis da sauran su, duk suna cikin zulumi har sai da result din ya fito babu matsalar komai, ajiyar zuciya Abba ya sauke da karfin gaske, duk suka kalle shi, yace su tafi bayan an tsaya an sai ma Asma'un abinda zata dan ci duk da sam bata da taste a bakin ta.
Gidan tsoho suka wuce, dama tuni Abba ya sanar dashi zuwan su ya kuma saka shi kiran Hajiya Mama itama yace tazo tare da Adam, toh tace amma zuciyar ta fal take da mamakin yadda Abban ya dau zafi dan tun dazu take kiran sa amma yaki dagawa, tasan yana da hakuri matuka tun yana yaro musamman a abinda ya shafe ta, baya hada ta da komai amma kuma a wannan karon, yana son nuna mata yar sa ta fi masa akan ta, bayan kuma abubuwan da Asma'un tayi wanda shi be sani ba. Mayafi kawai ta yafa tace Adam din ya taso, da farko yace ba zai je ba,amma tace dole ne dan bata isa ta tsallake maganar tsoho ba, ba asan ransa ya shiga motar ba, suna kokarin barin gidan Nadeeya na shigowa a tata motar, ta tsaya tana bin baasin in da zasu, sai kuma ta hango fuskar Adam din da tayi suntum, ya kuma hade rai tamau hakan ya sake taimakawa wajen hayewar fuskar. Dariya ce taso kwace mata, ta daure ta kanne cikin nuna kulawar ta tace
"Boy me ya same ka!?"
Banza yayi mata, Mama tayi kwafa tana sake kallon fuskar tasa
"Wai Umar ne ya shigo dan rashin mutunci har gida ya dake shi, akan wai dan ya tarar dashi yana yiwa asma'u fad'an taki yi masa breakfast, ni wannan masifar da na san haka auren nan zai zama da ba'a yi ba wallahi, daga taimako da zumunci sai kuma abu duk ya lalace."
"Daga kawai ya same shi yana mata fad'a sai ya hau dukan sa? Anya kuwa boy?"
Tace tana kallon shi, juyar da kanshi yayi gefe yana jan karamin tsaki
"Ina ita Asma'un toh, tana gidan ne ko yaya?"
"Sun tafi dai da ita, yanzu haka tsoho ne ya kira ni akan na same shi a gida na san kuma akan maganar ne."
"Gaskiya Mama akwai boyayyen abu da baki sani ba game da zaman Adam da Asma'u, ya fad'a miki gaskiyar komai kafin kuje kar azo ana jin kunya."
"Toh, dama na dade da ganin take taken ki, yanzu maimakon ki goyi bayan kanin ki, sai ki goyi bayan ta? Toh dai idan ma wani abun yayi mata ina ruwan Umar din? Ba mijin ta bane da zai shiga?"
"Idan kuma samun sa yayi yana kokarin kashe musu ya fa?"
"Driver wuce mu tafi dan Allah, sai mun dawo."
Maman tace a kufule, dan ma dai Nadeeya din ce har ta tsaya tana gaggasa musu wannan maganar da wani ne da ba zancen da ake kenan ba. Girgiza kai Nadeeya tayi, ta matsa suka fice tana jin rashin kyautawar maman, da na kowa ne kuma Asma'u da Adam duk na ta ne, duk daya suke a wajenta ya kamata ace tayi mata adalci kamar yadda take kokarin kare Adam din, ita fa duniyar nan kaso naka ne, duniya taki shi, kaki shi kuma duniya ta so shi, shi da da dukiya baa musu mugunta dan baka san wanda zaka mora ba.
Har ga Allah bata ji dadin abinda yake faruwa tsakanin Maman da Abban su Asma'un ba da tun da suka taso suka san yadda Abban yake daukar Maman da yadda itama yake a wajen ta, wanda suka san shine dalilin da har ya iya daukar Asma'u da tafi kowacce yar sa hakuri da saukin kai ya bawa mutum kamar kanin nasu Adam da su kansu watarana basu tsira daga rashin mutuncin sa ba.
***Ganin motar Abba a kofar gidan tsohon ya saka mama tabe bakin ta, tana jin ta shirya wanke Abban har an kawo matsayin da ba zai tsaya shi da ita su fahimci juna ba sai ya kawo maganar wajen tsoho. Kamar Adam ba zai fito daga mota ba, dan ya dan dau sakanni a ciki kafin ya fito tamkar bijimin sa, yabi bayan Maman yana sake tamke fuskar sa.
A tsakar gidan suka tarar da su Abban a zazzaune an shinfida tabarmi guda biyu Umma da Asma'un ba kai daya sai su kuma mazan na daya, wajen su umman Maman ta nufa ta zauna daga gefe sosai shi kuma Adam din ya tsaya a tsaye yaki karasowa har sai da tsoho ya buga matsa tsawa
"Zo ka samu waje ka zauna ka yi mana tsaye aka!"
Sai da ya maula yana daga tsayen suna kallon sa sannan ya dosana duwawun sa a gefen tabarmar ya zauna.
Sai alokacin Mama ta gaida tsohon ya amsa a sake yana tambayar ta bayan saduwa, sai kuma umma ta gaishe ta, ta amsa a gadarance, idon ta na kan Abba da yayi kamar be san da shigowar ta wajen ba, abinda yafi bata mata rai fiye da komai ta dinga satar kallon wajen su sai taga yayi mata kwarjini sosai kamar ba shine kaninta me kaunar ta da kaunar duk abinda ya zama mallakin ta ba.
"Toh Alhamdulillah, abinda ya tara mu anan ba wai boyayyen abu bane, magana ce akan Adamu da matar sa Asma'u, wanda muke so kowanne a cikin su ya dubi girman Allah, ya fadi gaskiyar abinda ya hada su. "
Da sauri Abba ya tare shi,
" Allah ya baka hakuri Baba, ban tari numfashin ka ba, amma Adam ya bawa Asma'u takardar ta kawai, shine dalilin zuwan mu nan ba maida magana ba, maganar abinda ya hada su kuwa duk wanda ya zalunci wani a cikin su, toh Allah yayi masa sakayya tun a duniya."
" A ah karami, ba'a shishigi a cikin al'amarin ubangiji, bari mubi komai a sannu, bamu san abinda Allah ya boye ba."
" Babu abinda Allah ya boye, kuma dai kamar yadda Karami yace ne, babu bukatar a zauna ana maida magana, kai Adam, saki Asma'u anan ba sai an bar nan ba, ka tashi mu tafi."
Ran tsoho ne ya baci, ya kalle su, duk su biyun yace
" Idan har zaku iya yanke hukunci haka menene amfanin zuwa gareni? "
" Allah ya baka hakuri Baba, duk abinda kayi daidai ne. "
Abba yace yana jan bakin sa yayi shiru, itama Maman bata sake cewa komai ba, ya kada kansa yana duban Adam
" Adamu kaine gaba da Asma'u ba a shekaru ba kawai hatta a wajen Allah saboda kai din shugaban ta ne, kuma mijinta, inaso ka dubi girman Allah, ka sanar damu abinda Asma'u take maka a zaman ku da ita."
" Menene ma bata yi min ba, gata nan ai, tasan koma a tambaye ta."
" Bana son sakarci, tambayar ka nayi kuma kai nake son ka amsa min, ai na ganta din kai nake so ka fada min. "
Shiru yayi dan bashi da abin fad'a, kallon sa Hajiya ta dinga yi tana masa signal yayi magana, ya kasa cewa komai har sai da tsoho ya sake maimaita maganar sa sannan yace
" Ta raina ni ne, bata bani girma na a matsayin na, na mijin ta. "
" Muna sauraron ka, kamar wanne irin raini? "
" Raini dai kawai, idan nace tayi abu sai ta ga dama zatayi, ko gaishe ni bata yi bare na samu kuautatawa irin ta mata da miji. "
" Toh Adam, bayan wannan fa? "
" Naam. "
" Bayan wannan fa sai me take maka, karka ji komai ka fada mana. "
Shiru yayi yana kokarin tuna abinda zai ce,
" Shikenan abinda take maka ko? "
Shiru ya sake yi nan ma,
" Toh Madallah, ko zaka iya fad'a mana abinda ya faru har ka daga hannu ka dake ta."
" Duka? " Yace sai kuma ya kalli Umar ya dauke kansa da sauri
" Eh duka, mahaifiyar ta da dan uwanta sun tarar da kai kana dukan ta, shine muke son sanin dalilin hakan. "
" Ita ta tunzura ni, na dake ta ai, magana nayi mata ta tashi ta hada min breakfast tace ba zatayi ba, ta hau zazzagi na, shine ni kuma na sake ta."
" Zagi? Wanne irin zagi kenan? "
Kafin ya bud'e baki Mama tayi karaf tace
" Zagi dai kowanne iri ai sunan sa zagi, ni kaina na san abinda ku baku sani ba, akan faduwar da tayi wanchan karon, duk a dalilin yana bin ta akan hakkin sa ne ya saka ta wannan faduwar saboda ta tsani ta hada inuwa waje daya dashi. "
Maido da hankalin sa yayi kan Mama, yayi murmushi yace
" Asabe ban tambaye ki ba, amma naga alamar kamar kin fi Adam sanin matsalar gidan sa, sai ki sanar damu abubuwan da kika sani. "