← Book details Rayuwar Mace Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 66

Sashe 14

Rayuwar Mace Complete Hausa Novel · about 7 min read

Shin Ina matan suke🗣️🗣️🗣️maza kuhanzarta kumatso kusa kuma kubani aran kunnuwanku domin sanin albishir dawannan shahararran company yazo muku dashi😃🤩
Hakika tabbas duk macen data amsa sunanta bazataso afita b Koda da kwayar zarra domin hakane wannan shahararren company yazomuku da ingantattun hadaddun kayan gyaran jiki masu matukar gyara fata cikin kankanin lokaci batare da sunyima fata lahani ba domin kayan mg's organic products ne bawai na bleaching ba zasu gyara ma mutum fatane yafiddomashi da ainihin natural beauty din mutum👌hakika duk wacce batayi anfani da kayan mg's b anbarta acan karshen bayama kuwa domin Koda sabulunsu kadai kuka dana fatanku seya fita dasauran mata ballentana Kuma kuyi anfani da gbdy beauty kit dinsu wohoho wani abun baa mgn sewanda yajaraba shine zai tabbatar❣️
Shin kinafama da
Pimples, black spot,sunburn, stretch mark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama duk wani matsalan fata?
Shin fatanki tana tattarewane ko kinshafa cream yabatamiki jiki😫
Shin inamasu cewa sunjaraba Basu dace b bi'iznillah sister's duk Wanda yayi using mg's sai godiya domin Koda iya herbal whitening black soap din kikayi anfani dashi zakiga ynd fatanki zaiyi clear Yana walwali jikinki zeyi fresh kina glowing my dear bare Kuma ace set dinne gbdy 🤗ga amare uk wnd yy using bridal set dinnan baya bukatar kowani gyaranjiki domin yadda jikinki zekoma yazarce misali DNT be left behind
Bridal kit:18k
Beauty kit:11k
Student package:7k
Herbal whitening soap:3k
Chat
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Facebook: mg's skincare
Instagram:glow_with_mgs
Take note pls iya wadannan numbers dinne kawai zakusamu kyn mg's babushi akasuwa🤝
Do you guys wanna achieve that milky skin that turns head wherever you go🤩
Then @mgs skincare gat you covered 💯
Now is time to glow😍
Pamper ur skin🦵
Shine like bride👰🏻‍♀
Glow🧖‍♀️

💯 tested nd trusted🤝
Guarantee

Sannan muna da hadaddun frames masu kyau gamai bukata yayi mgn 07046881166

RM
   11

Akan hannun ta ta fadi, tayi kara me karfi, be fito ba, ya tabe baki cike da haushin ta. Kokarin tashi tayj amma sam ta kasa motsa hannu, wani irin zugi yake mata ga goshin ta da yake fidda jini sosai. Kuka take sosai ta shiga kiran sunan sa 

"Ya Adam! Ya Adam! Zan mutu dan Allah ka taimaka min!"

Yi yayi kamar ba zai zo ba, sai kuma wani abu ya darsu a ransa ,ya mike da sauri yayo wajen, a yanayin da ya ganta ne ya saka shi karasowa a guje

"Tashi! Tashi!" Ya hau ce mata a kideme dan be yi tunanin hakan ba, ganin ta soma zama unconscious ya saka shi dagata chak ya sauka da ita da gudu gudu, ya shiga kwala wa me gadi kira,sosai kanta yake zubda jini ga hannun nata da ya tabbatar da ya samu matsala. Direct asibiti ya wuce da ita, bayan ya kira Nadeeya da wayar sa daya da ya bari a mota, a kidime ta amsa masa tace gata nan sannan ta kashe ta kira Hajiya Mama tace mata Asma'u babu lafiya sun tafi asibiti, itama Hajiyan ta tsorata sosai, ta dinga kaiwa da komowa har sai da driver ta da ta aika ya dawo, sannan suka dauki hanyar asibiti .

   Taimakon gaggawa aka shiga bata, aka samu aka tsaida jinin goshin mata amma sai da akayi mata dinki a wajen, sannan aka tabbatar masa da ta samu karaya a hannun da ta fadi a kansa, ji yayi kamar almara, ya dinga kallon ta a karon farko yaji burburshin tausayin ta ya wanzu a zuciyar sa, dakin da aka kwantar da ita ya tura ya shiga, ya tarar tana kwance tana fitar da numfashi daidai na azaba, wayar sa ya daga da Nadeeya ta kirashi, ya juya ya bar dakin yana amsa wayar da kwantancen dakin da suke, kusan a tare suka iso da Hajiya mama dan ita Nadeeya din daga nesa take, dukkan su a rude suke, suka isa dakin Nadeeya ta riga mama isa gaban Asma'un tana kallon hannun ta

"Karaya?" Tace cike da tashin hankali

"Innalillah wa inna ilaihi rajiun!" Hajiya mama ta fad'a tana kallon Adam din cikin son karin bayani

"Faduwa tayi wallahi mah, a wajen sauka daga stairs bansan dame ta zame ba, wallahi ban sani ba."

Wani kallo Nadeeya ta masa, ta kalli Maman ta fita zuwa wajen Drs din.

"Garin yaya haka ta faru Adam? Garin yaya?"

Girgiza mata kai yayi, yana jin wani iri, abun da be taba ji ba.

"Fad'a kukayi? Ko dama chan har yanzu akwai matsala ne?"

Girgiza kai ya sake yi, ta matsa ta taba jikin Asma'un da ya rure da zazzabi me zafin gaske

"Me zance wa mahaifanta? Waye kake ganin zai yarda da cewa faduwa tayi? Bayan kowa ya san yadda akayi auren nan, sannan kowa ya san halin ka."

Bashi da bakin magana, domin shi kansa be san bakin da zai yi amfani dashi wajen kare kansa ba, adah idan aka ce zai russuna haka har yaji tausayi irin haka zai karyata, amma kuma ya rasa dalili, sosai yake jin tausayin ta musamman ganin irin bakar wahalar da tasha a yanzun, karaya ba abu bane me sauki musamman a wajen wanda ya soma girma ba kamar yara kanana ba, ya taba samun dislocation sanda yana tashen ball ya san wahalar da yasha a lokacin ballanta na ita, yana jin Maman tana ta maganganu be ce komai ba, be kuma bar dakin ba, har zuwa sanda Nadeeya ta dawo da ya lura tana fushi dahsi sosai, har zuwa lokacin da Maman ta kira Abba a waya ta sanar masa.
   A tunanin sa zasu zo a take a lokacin, amma babu wanda yazo, da Hajiya Maman ta sake kiran Abban sai yace mata babu komai su ma sun isa zasu shigo da safe, hakan ya sake karyar wa da Hajiyan guiwa, taji da gaske bata kyauta ba, bata yiwa Asma'un adalci ba kuma ba ta yiwa mahaifin yarinyar hallaci ba, ya dauke ta ne tamkar uwa mahaifiya ya kuma amince mata yana bata dukkan girman ta, son kai ya kwashe ta da aikata abinda ba zata taba yafewa kanta ba.
   Kwanan zaune sukayi saboda yadda hannun ya matsa mata, sun tausaya mata dukkan su, har shi uban gayyar da ya zama so silent kamar bashi ba, sai gabannin asubah sannan ta samu wahalallen bacci ya dauke ta.
   Toilet mama ta shiga tayi alwala Nadeeya ta tsaida shi ganin zai fita, ta tsare shi da ido cikin tuhumar sa tace

"Me kayi mata?"

"Naam?"

"Tsorata kawai tayi ba, shine ta fito da gudu ta fadi, wallahi ban mata komai ba."

Ranta ne ya sake baci sosai, ta nuna masa kofa jin Maman zata fito, ya fice da sauri yana sake rejecting kiran Fido da take ta jera masa shi tun daren.

***Abbati ne yazo tare da Abba wajen takwas lokacin Adam din ya bar asibitin yaje dauko mata kaya, nan fa Hajiya Mama ta saka wa Abban kuka, ya dinga bata baki yaki yarda ya nuna damuwar su ko wani abu, ya kuma sake jaddada mata hakan kaddarar Asma'un ce, babu wani da ya isa ya hanata faruwa. Be jima ba yayi mata addu'a ya tafi, ya bar Abbati saboda ko za'a nemi wani abin tun da Adam din baya kusa.

***Waya umma suke da Ya Hadiza ta fad'a mata abinda ya faru, kuma Abba yace ta kyale Hajiya Maman suyi jinyar kar ma tace zata je ta zauna, hakan ba karamin bata mata rai yayi ba, a kalla dai a barka ka zauna da danka dan yafi bukatar ka akan kowa, hakuri Ya Hadizan ta bata tace gatanan zuwa gidan zata kuma kira Abban a waya, ajiye wayar sukayi umma ta cigaba da shirin tafiya asibitin dan ma yace ta jira Abbati ya dawo ya kaita da tuni ta tsufa a chan dan ba zata iya jurewa ba, dama ta san za'a rina ai tunda aka hada Asma'un da mahaukacin miji.
   Har Yaya Hadizan tazo Abbatin be dawo ba, sai kawai umman ta fito suka tafi, a hanya take fad'a mata yadda sukayi da Abban, yana nan akan bakansa be yarda Umman taje ta zauna ba, ya dai amince taje kullum amma ba wai da zuwan zaman jinya ba, ran Umman ya sake sosowa ainun, bata taba yi wa Abban bore ba, tun auren su take masa biyayya daidai gwargado, ba zata bijire masa ba a yanzu musamman da girma yazo, amma bata ji dadi ba, kuma shima ya san be kyauta mata ba.

"Allah Umma kina da hakuri sosai, anya akwai wadda tayi hakurin ki kuwa a cikin mu?"
Chapter 14 · 0% Book details