← Book details Rayuwar Mace Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 66

Sashe 63

Rayuwar Mace Complete Hausa Novel · about 8 min read

***Gaba daya Adam ya sauya daga kamannin sa, ya fita hayyacin sa saboda matsin lamba, gashi ya rasa yadda zai musu yace bashi bane, ko yace shi aikin lalata kafar motar ya tura g-boy yayi be san da duk wannan abun ba, wannan din ma case ne me zaman kansa, duk da yana ganin kamar zai fi zuwar masa da sauki akan wanda ake tuhumar tasa dashi. Yana zaune ya daga sangalalin kafarsa zuwa sama ya tura kansa cikin kafar tasa yaji an shigo, ya dago da sauri sai yaga Capt Mausul ne da Oga Ogidi, kokarin mikewa yake dan yasan lallai akwai babban al'amari tunda suka shigo.

"Zauna a wajen da kake!" Yace masa yana jawo wa Oga Ogidi kujera ya zauna a gaban Adam din

"Malam Adam, menene alakar ka da Garba."

"Garba?"

"Eh g-boy."

"Abokin aboki na ne."

"Wanne abokin naka?"

"Usman;"

" Menene ya hada ka da g-boy din, har yazo gida ya same ka, kuma muka samu number sa a wayarka, sannan kuma muka ga yawan kiran da kayi dashi a ranar da abin ya faru? Kar kayi mana karya, hatta voice record din wayar da kukayi muna dashi. "

" Wallahi tallahi asali ban sanshi ba, ban taba ganin sa ba, ranar na gaji da zmaan gida sai na fita zuwa majalisar dake bayan layin mu k'asa, anan muka hadu dasu mukayi ta hira, har mukayi exchanging numbers dashi g-boy din, daga nan ne kuma muka fara magana a whatspp. "

" Ehen? "

" Shine, shine sai na bashi aiki, nace ya kwance notin kafar motar Abdallah,... "

" Muna jinka "

" Shikenan wallahi, bansan komai akan abinda aka gani a motar ba, wallahi bani da hannu a ciki. "

" Video da ya nuna ka fa?"

" Bani bane, wallahi bani bane. "

" Ka rubuta Capt, attempt murder case. "

" Yes sir! "

" Zamu cigaaba da bincike, meanwhile, we regret to announce the death of your wife, sorry for the loss."

" Fido? Ta mutu? Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, yaushe?"

"Allah ya jikinta ya gafarta mata, sun samu accident ne. "

Mausul ya dafa kafadar sa, cike da tausayin sa, maida kansa yayi cikin kafarsa, wani irin tashin hankali na bijiro masa, Fido dai Fido? Ta mutu? Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, mutuwa! Fita sukayi suka barshi dan yana bukatar hakan, kuka ya shiga yi wiwi, yana tuna rayuwar da suka yi da ita, rayuwar so da kaunar juna, sun saba sun shaku sosai kafin daga karshe ya juya mata baya, hakan ya sakata samarwa kanta mafita ta hanyar aurensa, auren da ba zai iya dorar da komai akai ba, tunanin sa ne ya tsaya akan Asma'u, da yadda ya dinga shigo mata da Fido cikin gidan aurenta, sun zalunce ta zalunci me girma.
   Ya jima yana kuka, irin wanda be taba yi ba, kukan nadamar rayuwar da suka aikata, gashi bata samu dama da lokacin da zata roki Allah gafara ba. Bare ta nemi yafiyar wadanda ta zalunta ciki har dashi. Har dare yayi sosai yana nan a halin jimami, babu wanda ya sake shigowa wajensa balle su yi kokarin dukan sa, abinci dai aka kawo masa ya k'asa ci saboda yanayin da yake ciki. Ya dinga tunani rayuwa da yadda ya dauke ta, azafafe baya ganin mutuncin kowa, duk girman ka zai iya takaka, yasha firgita tsofaffi a hanya da mota wasu su rikice su fad'a kwalbati ma, amma yyi tafiyar sa ba tare da ya dube su ba, a lokacin duniya tana kada masa gangar ta, baya tunanin komai da kowa sai karan kansa, kansa kawai ya sani idan zai samu abu baya duba yadda wasu zasuji.

Kwanaki hudu da kama Adam, zuwa lokacin Hajiya Mama ta san dalilin kamasan, anyi sadakar ukun Fido yan uwanta suka watse dan dama da yawan su sun dade da sallamata dan dai mutuwa aka ce, suna tafiya sai gidan Hajiyan ya koma tamkar kango, ta dinga tunani da sake sake, ba zaka taba cewa ita ce Hajiyar nan ta baya ba, me cike da kiba da kujari, tayi matukar ramewa, ko magana bata son yi sosai daga um sai a'ah, tana jin nadamar rayuwar ma baki daya, dama an ce duk dan da ka fiya so da nuna ma soyayya daga karshe sai yazo ya saka ka kuka, ita ba ma kuka kawai ba, harta guzurin ciwon da yake barazana da rayuwar ta. Morning duty Nadeeya ta koma yi zuwa 12 ta tashi saboda ta samu damar kula da Hajiyan, Abba ma kullum sai yazo dan kawai ya bata baki. Haka dai take daurewa amma ita kadai ta san halin da take ciki.
   Gajiya tayi da zaman falon ta koma cikin daki ta dan kishingida, sai ga Nadeeya ta shigo,

"Kinyi baki Mama."

"Su waye?"

"Asma'u ce da mijinta."

"Kai Kai, anya zan iya fitowa su ganni? Ai da kunya haba dan Allah."

"Daurewa zakiyi ai."

"Kai, dan dai babu yadda zan yi ne Nadeeya, gani nan."

Tace ba dan taso ba, fita Nadeeya tayi tace musu gata nan, ta zauna suka sake gaisawa da Asma'un da Abdallan, sai ga Hajiyar ta fito, duk suka zame suka gaishe ta, hawaye ne ya taru a idon ta, tana amsawa nutsuwar Abdallan ta burgeta, har ta dinga hango ace adam dinta ne wannan, gaisuwa suka sake yi mata da jajen abinda ya faru, ta amsa a kunyace sannan Abdallan ya fita yace zai jira Asma'un a waje, yana fita ta mike tazo wajen Asma'un, ta zauna a kujerar da take kai, sai tayi kokarin sauka amma ta hanata

"Dan Allah ki yafewa Adam Asma'u, ba dan ni ba dan Girman Allah Asma'u, ki duba zumunci ki yafe masa, wallahi hakkin ki ne yake bibiyar mu dukka, dan Allah."

" Wallahi Allah Mama ni ban rik'e ya Adam ba, na dade da yafe masa wallahi, Allah ma muna masa laifi ya yafe mana bare, ni ya wuce a wajena wallahi. "

" Allah yayi miki albarka, ya baki zaman lafiya a gidan mijinki, nagode Asma'u na gode. "

Nauyin hajiyan da tausayin takeji sosai ganin yadda ta koma, ta ciro kudi a Jakarta ta ajiye mata a gefe tace  a siya wani abun, har kofa ya rakota duk da jikinta babu kwari tana mata godiya da addu'ar fatan alkairi.
  Tana shiga motar ta sauke ajiyar zuciya, ya kalle ta yana nakaltar yanayin ta

"Cry cry baby, yanzu fa sai kice zaki mana kuka ko?"

"Wallahi abun tausayi, life din nan baki dayan ta lesson ce."

"Haka ne dama, Allah ya bamu ikon aikata daidai."

" Amin mijina. "

" Yanzu sai ina? My cry cry baby? "

" Ka manta? " Tace tana bud'e hannu

" Wai da kawai mu koma gida, mu shige daki muyi kwanciyar mu yadda garin nan yayi luf luf. "

" Rauda zata cinye ni danya, yanzu ma nasan sai tayi korafin rashin zuwa na da wuri, wai ni zanyi tsire. "

" Kar dai a wahalar min da matata wallahi, yawwa. "

" Rauda ce fa? "

" Raudan, kawai sai a saka min ke aiki? Ana zaune kalau. "

" Toh ai kamawa tayi your excellency, yau ne kadai. "

" Toh shikenan, yau kawai, kar a kara. "

" An gama ranka ya dade! "

Ta dage hannu ta russunar da kai irin yadda ake ma saraki, gaba daya Asma'un ta san lagon sa da abinda yake so, shiyasa a kullum yake kara son ta da kaunar ta. Sai da suka fara biyawa yayi ma Rauda siyayya me uban yawa, tamkar be san zafin kudin ba, sannan ya bata dubu goma yace ta rik'e a hannun ta, kin karba tayi da farko dan bata ma san me zatayi da kudin ba, dole ya sakata ta karba tayi masa godiya yayi kamar be ji ba, ya rakata da kayan har kusa da ciki sannan ya juya dan yana so ya samu wani akan maganar Adam din.

***Adam na zaune aka shigo da g-boy, ya mike da sauri yana kallon sa, shima shi yake kallo kafin ya sakar masa murmushi, wurgo shi wanda ya shigo dashi yayi ya fado a gaban Adam din,

"Oga walalhi wannan shine g-boy din, shine yasan komai wallahi shine."

"Mun fika sanin haka." Yace yana juyawa, wani shu'umin murmushi g-boy yayi masa kafin yace

"Ya kaji mutanen?"

"Me yasa ka yaudare ni, me yasa baka yi abinda na saka ka ba, kayi wani abun daban."

"Menene marabar abinda nayin da kisa? Kai fa cewa kayi ayi abinda zai rasa ransa, na saukaka maka ta hanyar nan ne fa, kuma ba wai naje da niyyar hakan bane, naje kenan Ina kokarin aiwatar da aikin sai ga kira nan daga oga, dan har na bud'e motar da spare key, ina kokarin tsinke wata waya kiran nasa ya shigo, yace nayi maza maza na bar in da nake ana bibiyata, shine fa kawai sai tunanin na saka masa kayan da nazo dasu yazo kaina, nayi maza na tura masa a kasan kujerar sa har da wayar, sannan na fece, ashe ashe shegun sun san takan aiki, nan da nan su kayi ram da kai dan dama kasan ai nayi maka maganar da fuskar ka zanyi amfani na shiga wajen saboda me gadin nan, be kuwa tambaye ni komai ba Ina zuwa na shige, shine dalilin da ya saka aka kama ka."

" Amma wallahi ka cuce ni, ka cutar da rayuwa ta. "

" Kai ka fara cutar kanka Baabaa, ta ya na cuce ka, kai kace ayi maka aiki, da kasan baka shirya ba, ka tattaro aikin da yafi shegiyar kwanyarka! Kai ai karamin dan iska ne a yan iskan ma wallahi. "

" Naji, nafi ka dai, banza jaki, ka saka ni a matsala ina zaman zaman,. "

" Karka sake ka sake zagina wallahi, zan iya yi maka shegen duka a wajen nan, kasan ni na riga na shigo ba fita zan ba, sai na dake ka, na daki banza wallahi. "

" An zage ka din, kayi abinda zakayi, bakin mugu azzalumi. "
Chapter 63 · 0% Book details