Sashe 44
Rayuwar Mace Complete Hausa Novel · about 7 min read
Bata da zabi illa tayi godiya ta tashi rik'e da kudin ta fito tana juya su a hannun ta, dakin ta koma Rauda ta mika mata wayarta da sauri sanda kiran ya sake shigowa a karo na uku, tsoron haduwar su da Abba ya hanata kai mata wayar dakin Abba shi kuma ogan be daina kira ba, har ma ta yanke shawarar kai matan sai gata ta shigo,
" Ya Asma'u Uncle Abdallah sai kira yake, gashi nan ya sake shigowa ma kiran."
Hannu tasa ta karba sannan ta jefa mata kudin kan cinyarta tana fita zuwa dakin umma dan bata son yin wayar a gaban Raudan. Sai da ta shiga dakin sannan ta daga tana ji ya shaki iska ya fesar, sannan ya amsa sallamar da tayi masa
"Ina kika shiga ne my wife?"
"Wajen Abba naje, ashe ka kira."
"Eh so nake naji muryar matata kafin na tafi office."
"Uhmm."
"Kar naje na kasa aikin Oga ya sallame ni, kinga ai da matsala ko? Abinki da karamin ma'aikaci."
" Ka iya tsokana."
" Ba wani tsokna, da gaske nake, kinsan yanayin aikin kasar tamu."
" Ummm... Haka ne."
" Toh kin gani?"
Ya fad'a yana danne wayar a tsakanin kansa da kafadar sa, ya duka yana saka socks sannan ya saka takalmi ya mike wayar na makale da kafadarsa har lokacin yana magana k'asa k'asa, brush ya dauka ya sake kwantar da sumar kansa wadda tasha gyara,
"Idan na gama daga office din zai biyo, sai muyi maganar abinda ya kamata ko?"
"Tam shikenan.... Sai ka dawo. "
" Yawwa, take care of yourself for me. "
" In sha Allah."
Tarkacen kayan sa ya dauka bayan ya tura wayar aljihun sa, ya rik'e dayar da tab dinsa a hannu ya fito falon, yasan ba zai samu MD ba dan yace masa yana da sakon da zai karba a airport da duku-duku, dan haka shi kadai ya shiga cikin gidan nasu, ya gaida su Mami sannan ya nufi wajen Baba Alhaji, ya tarar ya koma bacci be tashi ba, sai kawai ya fito ya bar gidan dan dama kunyar haduwar su yake bayan abinda MD din ya shuka masa, yanzu yasan duk wani kallo yan gidan zasu dinga masa bayan shi ba haka yake ba, MD ne duk ya jawo amma shima zai rama ne, yana kallon irin kallon da Mom take masa jiyan nan yasan idan ya dawo sai ta zaunar dashi dole ne, be san me zata ce masa ba dai amma yasan bata da zafi da tsawwalar da zata ce bata karbi auren ba. Be sani ba, tun a jiyan suka fara tunanin hada lefen sa bayan Baba Alhaji da kansa ya kirasu ya basu labarin duk yadda al'amarin ya kasance, kuma duk cikin su dama babu me ja da hukuncin Allah, shiyasa ma yayi komai kansa tsaya dan yasan yayi sa'ar mata na gari masu son duk abinda yake so, shi da kansa ya basu kudi yace a hada wa Asma'un lefe, Mami ce ta karba dan dama itace uwar Abdallan, ita kuma zatayi komai ita Mom yar kallo ce kawai. Aunty Fati ta dora itama akai nan da nan aka soma hada kaya na gani na fad'a a daren aka siya wasu online kafin yau da zasu shiga kasuwa sosai dan ma abin yazo a kure da Dubai Mami zata ta hado lefen Abdallan na nuna sa'a, amma duk da hakan ma zasuyi abu me kyau da tsari.
Yana zaune a office din yana duba wasu motoci ya ga MD na shigowa cikin building din ta cikin CCTV din dake cikin office din wadda take nuna duk shige da ficen da ake a cikin compay, tashi yayi ya murda key a kofar tasa ya dawo ya zauna ya cigaba da aikinsa,kansa tsaye ya murda kofar amma sai ya jita a rufe, ya sake murdawa yaji da gasken a rufe take, sai ya juya a tunanin sa ko Abdallan baya nan, murmushin mugunta yayi lokacin da yaga ya juya dan yasan zuwa zai ya isheshi ya hana shi aikin gabansa gashi yana so yaje yaga matarsa kuma baya so aikin ya kai masa yamma sosai dan so yake ya dauki hutu daga satin da zai kama. Sai da ya gama aikin tas wajen biyu da rabi sallah kawai ta tashe shi sannan ya bud'e kofar ya dauki waya ya kira MD din yace yazo ya sameshi a office da yake building din da suke daban daban ne amma duk cikin gini daya, shi yana bangaren karan kansa shi kuma MD na kula da business din Baba Alhaji
"Na zata ko Amaryar ce a office din dana ga ka saka key ai, shiyasa ma ban zafafa ba na koma."
"Ina sane ai, damu na zakayi ban gama aikin ba. "
" Nima fa aikin ne dani da yawa wallahi, ba zan iya zuwa ba gaskiya. "
" Dan Allah kazo, abu zaka tayani dubawa, kayan sun zo suna nan Lagos, kazo mu duba sai ka zabi daya. "
" Dan Allah da gaske? "
" Idan ba zaka zo ba shikenan. "
" Ah wallahi gani nan, jira ni yanzu zaka ganni. "
" Ok kayi sauri kafin na chanja shawara. "
" Yanzu kuwa. "
Yana ajiye wayar yana shigowa, ashe suna wayar ma yana tahowa, murmushin mugunta yayi masa ya tura masa system din gaban sa bayan sun zauna
" Kai ne mayen mota, ga latest nan, sai ka duba ka bani ta wajenka sai naga nawa zaka cika?"
" Dan Allah da gaske? "
" Oho. "
" Wow..bari muga." Yaja system din gaban sa yana dubawa a hankali har yazo kan wadda tayi masa, wadda dama tun da ya saka order su ya kwallafa rai akanta, juya masa system din yayi yace
" Wannan nake so. "
" Banda ita. "
" Why? Haba Abuya kaifa kace na zaba. "
"Eh amma banda ita, it's for my wife. "
"What?! " Ya mike yana kallon sa
" Abinda kaji, ka duba wata dai ina sauri ne, zan tura ma wani Alhaji ya gani, sai na cire su a ciki
"Amma ai this is not fair, kaifa kace na zaba na zaba kuma..."
"Nace banda ita ba, it's for my wife."
"Ai shikenan, tunda ta fini."
"Wait... Wai ka zata daya kuke dama?"
"Na fita ma nake tunani."
"Tab! Zabi kayi sauri, na gaji da magana, ko ka jira next order idan sun sauka. "
" Bari naga, ita din dai wallahi nake so, haba angon Ma'u, haba Alhaji Abdallah Motors, haba Yaya Abdallah me kudin duk Nigeria, pls pls ka bar min ita, ga ta mata nan masu kyau u can choose one for her, dan Allah, inaso na kare yawa da ita wallahi, akwai wata babe dana tama. "
" Ajiye min system, baka shirya ba har yanzu, kuma wai a haka Baba yake cewa kai kayi min aure, wannan ai insult ne babba, idan baka nutsu ka shiga taitayin ka ba, sai dai kaga ana raba alawa da goro. "
" Auren dole? Zaka min? "
" Oho, ka dame ni kasa ina ta bata baki na, tashi zan kulle office dina. "
" Ina kayi daga nan? "
" Gari zan shiga, karma kace zaka bini. "
" Nima garin zan shiga ai, hanyar ina kayi?"
" Baka zo da mota bane?"
" A ah zan dawo nan ai, bana so na fita da ita ne. "
" Toh ba hanya daya zamuyi ba."
" Why are you avoiding me, ko dai chan zaka? "
" Ina? " Ya harare shi yana tura kofar ya rufo ta suka jera
" Chan din, idan ma chan zaka ni ba zuwa zan ba, ba zaa barni a waje a shige ciki ba, kuna chan kuna shan dimi ni an barni waje, nah nima inada gata na. "
Duka ya kai masa yana dariya
" Allah baka jin magana MD. "
" Ai gaskiya ne. "
" Toh yafi maka ai, nima takura min kake. "
" Yanzu sai ka dawo kenan? Ko gida zaka wuce daga chan? "
" Noo zan tsaya zooroad, zan iya dare ma, anyways muyi waya idan akwai wani abun. "
" Ok, safe! "
Ya saki kofar ya rufe masa ita yana ja baya, juya motar yayi ya fice shi kuma ya koma saman dan ya tattare sauran ayyukan da zai kafin time din da zasu shiga meeting, lokacin ma ya taho shiyasa zai yi sauri yaga yayi rounding up idan yaso gobe sai ya fara wasu kawai.