← Book details Rayuwar Mace Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 66

Sashe 61

Rayuwar Mace Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Akwai wanda muke bibiya tun daga jos muke bin sa, bama iya samun sa, sai mun fara bin sa sai mu rasa signal din, haka muke hakura amma kuma muna zama alerted da duk wani motsi nasa, in dai ya kunna wayar toh lallai zamu same shi, jiya zan shiga wanka kenan har na cire kaya, sai ga waya ana nema nayi maza maza na fito an samu signal din wayar, a guje na saka kayan na fita, kuma muka bi wayar har muka gano a motar ka ne aka samu kayan da muke nema, munyi mamaki dukkan mu kasancewar na san waye mahaifin ku, na kuma sanka dan har na taba siyan mota a company ka munyi mu'amula me tsafta na kuma gamsu da nagartar ka, duk da ance zuciyar mutum birnin sa amma ina kyautata maka zato, dalilin hakan ya saka muka kama shi Mudassir, kuma muka gabatar da bincike a tsakanin jiyan zuwa yau, mun yi duk binciken mu karshe muka samu evidence a cikin motar ka, har muka samu nasarar chafke wanda muke da yakinin shine wanda ya aikata laifin ko kuma yana da masaniya akan wanda muke nema."

" Waye?"

"Tsohon mijin matarka. Adam."

" Adam!"

"Shi muke gani a cikin video din, guda biyu ne na lokaci daban daban."

"Ya Salam! Adam!"

"Dama akwai matsala a tsananin ku ne?"

"Akwai duk da wani abu ne be taba hada ni dashi ba, amma shi yana jin haushi na,har yayi attempting fad'a sau wajen uku, amma ban bashi attention ba cox naga kamar he's into drugs kuma kamar baya hankalin sa, I never thought he can stoop this low."

"Allah ya kyauta, zamu karasa binciken mu akansa, idan mun samu duk bayanan da muke so muka kuma tabbatar shine me laifin toh in sha Allah kwana goma yayi yawa mun gama da babin sa, wannan shine hukuncin duk wanda aka kama da irin wannan laifin, as for your car, a ka'ida duk motar da aka kama da irin wannan kayan a cikin ta, muna kwace ta ne mu kona ko dai ta zama under government, amma babu komai, zanyi magana da Capt Ogidi, sai ku dawo in a week or two, zuwa lokacin an yi duk arrangement an saki motar."

" Thank you very much Sir, Allah ya kara kiyaye ku ya baku sa'a a duk abinda kuka saka a gaba, I admire your courage tun ba yanzu ba, ina kuma kyautata muku zaton cigaba da zama nagartattu a aikin ku, domin ceto kasar daga irin wannan bala'in da yayi mana yawa."

" In Sha Allah, Amin Amin."

" Zaka je babban falon nan zaka saka hannu, daga nan zaku iya tafiya, Allah ya kiyaye gaba."

" Amin Sir!"

" Sai anjima."

Ya juya zai bar office din sai kuma ya tsaida shi

" Sir Karefa, idan kunje gida ayi wa iyaye godiya domin addu'ar su ce ta fitar da Mudassir daga wannan siradin, idan kun tara duniya da abinda yake cikinta idan har mukayi bincike muka ga bashi da gaskiya ba zamu taba sakin sa ba, haka kuma idan har kune kuka fi kowa talauci a duniya idan yana da gaskiya babu sisin ku da zatayi kuka, saboda haka addu'ar iyaye ta taka muhimmiyar rawa a wajen samun saukin binciken mu, a cigaaba da rik'e gaskiya da kuma biyayya da iyaye. A gaida Madam!"

Jinjina masa kai Abdallah yayi cike da gansuwa da jawabin sa yace

" Nagode sosai Sir!"

"Take care!"

Ya fita ya ja masa kofar, kafin ya karasa har Mausul din ya kira yace a saki Mudassir din, bayan Abdallan ya saka hannu. Yana shiga MD yana tsaye, be san sanda ya rungume Abdallan ba, gani yake da kamar shikenan ba zai sake ganin su ba, rayuwar tayi masa zafi. Idon Abdallah na kan Adam da yake durkushe yana fidda numfashi bayan ya gama cin uban duka. So yake ya rik'e shi, ya tanbaye shi dalilin sa na son ganin bayan sa har haka, da ba dan akwai tsaro da hukuma ba, sannan duk wajen suna girmama shi ba, da babu abinda zai hana shi fasa bakin Adam din har sai yayi jini, amma ko a yanzu zai nuna masa cewa shiru shiru ba wasa bane gudun magana ne, ya riga ya shigo ramin kura, fitar sa sai yasha matukar wahala. Hannun su sarke dana juna suka fita daga wajen, MD ko waiwaye bayayi dan ko makiyinsa baya fatan ya shiga tashin hankalin da ya shiga a yan sa'o-in, Abuya ne ya bud'e masa mota ya shiga, ya zauna sannan ya rufe masa kofar ya zagaya ya shiga ya tada motar,ya daga musu hannu suka fita daga wajen.
Tuni labarin ya kai gida dan Baba Alhaji da suka rabu da Abuyan gida aka kaishi, murna kowa yake har Asma'u da tayi saurin komawa part dinta, ta dora musu girki sharp sharp, ta matsu ta saka Abdallan a idonta, ko ba komai zata rage masa zafin da yake ji na abinda ya faru. Tana aikin girkin ne taji hayaniya a compound din gidan, mayafin ta, ta dora akanta ta fito sanye da slippers ta tarar da su Anty Faty duk sun fito suna jiran Abuya ya gyara parking, yana kuwa tsayawa sukayi kansu, Ihsan ta dane MD tana fashewa da kuka, Amira na tayata. Shi kansa hawayen tausayin kansa da tashin hankalin da yan uwansa suka shiga yake yi, Mom ce ta janye Ihsan din ta riko hannun sa, duk sun ci kuka sun koshi, ta jashi zuwa ciki suka bi bayanta. Hada ido sukayi bayan sun dunguma sun yi ciki, ta langabe kanta alamun tausayawa kwalla na cika idon ta, girgiza mata kai yayi ya rungumota gefen sa suka shiga takawa zuwa part din su

"Karki yi min asarar hawayenki masu tsada."

"Ka ganka kuwa? Ka rame sosai."

" Ba dole ba, na shiga tashin hankalin da ban taba shiga irin sa ba, bansan ya zan iya rasa daya daga cikin mutane biyar masu matukar muhimmanci a rayuwa ta ba, you, MD, Baba, Mom and Mami."

" Ba zan iya dauka ba "

" Babu abinda zai faru sai alkhairi, in sha Allah."

" In sha Allah."

Zama yayi a daya daga kujerun falon ya mike kafarsa da yake jin kamar an sude masa dunduniya ga wani irin ciwo da take yi, ruwa me sanyi ta kawo masa akan tray da ragowar kunun ayan sa yayi kankara ma, ya dan tashi yasha ruwan shima kad'an ya koma ya sake mikewa. Kitchen ta koma ta kwashe jallop spaghetti da nama da tayi sharp sharp kuma favourite din MD kenan, ta saka masa nasa daban ta hada a dan madaidaicin basket, sannan ta dora na Abdallan ya tray ta ajiye masa

" Bari naje cikin gidan yanxu na dawo kaji?"

" Karki dade please."

" Ba zan dade ba, I promise."

Ta dauki basket din ta fita, ta samesu a falon an baje MD na kusa da Mom ana maida zance, kayan hannun ta Ihsan dake kusa da hanya ta karba ta karaso dashi ciki, ta ajiye a tsakiyar falon

" Yaya MD ina wuni? Haka abu ya faru? Alalh ya rufa asiri ya kiyaye gaba."

"Amin Anty Asmy."

"Amin Amin." Suka amsa

"Abinci nane wannan ko?"

"Acici!" Anty Faty tace tana jawo basket din

"Naka ne."

"Thank you matar yaya, ke kadai kika san better thing."

"Bakin ka be mutu ba ko?"

"A zuba min abincin dan Allah, sai naci sai na watsa ruwa."

" Dauko plate Amira."

" Toh." Ta tashi taje ta dauko plate din aka zuba masa, ya karba ya shiga ci a yunwace, babu wanda be ji dadin abinda Asma'un tayi ba, tasan ya kamata kwarai da gaske, shiyasa suke kara son ta, babu wanda yayi tunanin yi masa abinda zai ci, kuma yana bukatar abincin kafin komai ma. Fad'a aka farayi akan ragowar abincin tsakanin Amira da Ihsan bayan Anty Faty da Anty Asy sun dibi nasu, da haka ta sulale ta koma wajen Abdallan da hankalin ta kachokam yake wajen sa.
Samun sa tayi yana bacci, ya kwanta a kan sangalalin hannun sa, dan gyara masa hannun tayi ta zauna daf da saitin fuskarsa kamar me gadin sa, kiranta akayi a waya ya dan motsa tayi saurin maida ta silent ta tashi ta shiga daki ta daga, Umma ce dama take son tambayar ta akan labarin halin da ake ciki anan din, barka tayi tace zasu zo daga baya yanzu ana neman inda Adam yake ne, a sanyaye tace Allah ya sa a ganshi, kasan zuciyar ta na raya mata, Adam yana da hannu a abinda ya faru. Bata son abinda zai jawo mata matsala da cikin gidan su Abdallan dan daidai gwargado suna nuna mata soyayya, tsoron ta daya kar iyayen su ji cewa Adam tsohon mijin ta na da hannu a shigar yayansu wannan tashin hankalin, zasu iya chanja mata. Falon ta dawo ta koma wajen da ta zauna ta cigaba da zama tana duba agogon wayarta time to time.
Sai kusan shida ya tashi bakin sa dauke da salati, be san ya akayi yayi baccin ba, duba da lokacin ba lokaci bane na bacci, babu kyau ma bacci tsakanin la'asar da magriba, sai gashi yayi ba tare da ya shirya ba. Hannun sa ya mikar zuwa wuyanta, ya zagayo su a jikin wuyan nata ya jawo kanta daf da fuskar sa.

"Shine baki tashi ni ba?"

"Nasan kana bukatar baccin, jiya fa bakayi bacci sosai ba."

"Ba zai yiwu bane, yanzu kuma kinga nayi bacci a lokacin da be dace ba."

"Dauke ka yayi ai, kafin na dawo fa har kayi bacci."

"Toh ba kece kika ki dawowa ba, sai kawai nayi bacci."

"Sauri fa nayi, bansan zakayi bacci ba da na kira Amira ta dauki abincin, gani nayi gwara naje nayi masa sannu da dawowa."

"Haka ne, taimaka min toh na tashi na watsa ruwa kafin a kira magriba."

Hannu ta bashi ya kama ya tashi zaune, ta shiga toilet din ta hada masa ruwan wankan daidai yadda zai masa, ta dawo tace ya shiga ruwan is ready, sake narke mata yayi yana noke kafada

" Kiyi min wankan, ba zan iya ba."

" wankan?"

"Eh, please..."
Chapter 61 · 0% Book details