Sashe 60
Rayuwar Mace Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Babu komai." Yace yana matsawa gefe, ta sake biyoshi ya rik'e shi tana kashe masa ido
"Ka fada min matsalar ka, zan taimaka maka, I promise!"
Kuri yayi mata da ido, ta daga masa kai alamar eh dagaske take,
"Asma'u..."
Ya furta a rarrabe yana kallonta, wani abu ne ya dake ta, tsoro ta shige ta, lallai tayi sakaci da har ta bar masa gurbin da zai iya tunanin Asma'un bata cika gurbin da tsoron ta ba, sakin shi tayi tana matsawa baya, sai kuma ta daka masa tsawa, cikin tsananin bacin rai tace
"Kana nufin tsinanniyar tsohuwar matar ka kake tunani, a gabana har kake iya furta sunan ta, lallai nayi sake wallahi Allah, ni na kyale ka amma a yau ba sai gobe ba, zanyi maaganin abun."
"Kiyi hakuri dan Allah, karki mata komai, babu laifin ta wallahi laifi na ne, bata san komai ba ni ne kawai nake hauka na."
"Hauka?" Sai ta kwashe da dariya,
"Ai baka fara hauka ba tukunna Adam, baka fara ba da sauran ka."
"Cikani Malam!"
Ta warce hannun ta, ta barshi a wajen ta haye sama fuuu, ta dauki wayarta tace wa Faiza gata nan zuwa zasu koma kura akwai sabon aikin da za'a yi mata, mayafi kawai ta figa da mukullin motar sa, tazo ta wuce shi yana tsaye a falon abun tausayi, ya bita da sauri ta shige motar ta tayar ta fice daga gidan saura kadan ta taka masa kafa.
***MD na zaune akan wata doguwar kujerar katako, tea ne da bread suka bashi da safen amma baya iya jin zai iya ci a cikin sa, har kukan bakin ciki sai da yayi, wai shine aka kama da zargin kidnapping da supply na manyan makamai, be taba ganin live bullet da idon sa ba, sai gashi tun ana kirga daya biyu sai da aka kira guda dari biyar, kuma wai a cikin motar Abuyan sa, yasan duk plot ne saboda aga bayan sa, dan wanda yayi hakan ba shi MD din yake targeting ba, amma yana da yakinin koma waye toh shi ma baya son shi, dan duk wanda baya son Abuya toh ba zai so MD ba, su din yan uwan juna ne kuma makusantan juna,.
Capt Ogidi ne ya shigo wajen ransa a bace, yaro karami da be fi sa'an Aby ba, ya daka ma MD din tsawa,
"Ba zaka fadi gaskiya ba ko? Karya yake ku matse shi zai fadi gaskiya ma."
"Wallahi yallabai bansan komai akai ba."
Be sake kallon sa ba, ya juya baya yace
"Baku samu komai akansa ba?" Ya tambayi Capt Mausul dake bayan sa tare da kananan yaransa.
"Mun samu sir,you need to see this."
Ya matso da tab din ya kunna masa video din da suka samu, hannu ya saka ya karba ya nuna wa MD,
"Kasan wannan?"
Video din a black and white yake sai da ya kalla sosai sannan ya gane shi,
" Adam ne ai."
Yace yana kallon su
"Adam? Waye shi? Menene alakar ka dashi. "
" Tsohon mijin matar Abdallah ne."
" I see! Any details of his where about?"
" Sai dai address din gidan sa."
"Capt Mausul?"
" Yes sir!"
" Take the necessary information, and assign a team to go and arrest him ASAP, we can't take any chances, kafin ya samu hanyar fecewa."
" An gama sir!"
Fita yayi ya bar Mausul din da yaran sa, ya dauki necessary information da zasu bukata, ya tashi team guda da suke under him suka tafi.
Adam na zaune a falo yana sake tisa kiran G-boy har lokacin wayar na kashe, akayi knocking a kofar, tashi yayi ya duba dan yasan ba Fido bace, mutane uku ya gani a tsaye, sai maigadi gidan da suka tiso keyarsa
"You are under arrest Mr Adam!"
"Arrest? On what ground?"
"Idan muka je office zaka ji bayani. Arrest him serj."
Handcuffs suka saka masa, suka tisa keyar sa suka saka shi a mota suka tada kura gaba daya suka fice daga unguwar, maigadi ne ya ruga gidan Hajiya Mama ya sanar da ita, ta fito a gigice tana salati, babu alamar su a unguwar haka ya sakata rushewa da kuka, ta koma gidan da gudu ta jawo mayafinta da wayarta ta hau kiran Abba a waya.
"Karami an tafi da Adam, na shiga uku."
"Me ya faru? Me yayi su waye suka tafi dashi?"
"Ban sani ba nima, kafin mu fito sun tafi, innalillah wa inna ilaihi rajiun, wannan masifa dame tayi kama?"
"Ki kwantar da hankalin ki, yanzu kina Ina? Ina zkai je?"
"Bansani ba, wallahi bansan ina zanje ba."
"Kizo gida , sai mu san abinda ya kamata ayi, ki nutsu ki kwantar da hankalin ki."
Kuka ne yaci karfin ta, ta toshe bakin ta, ta hau kira Nadeeya dake on duty, ta fad'a mata abinda yake faruwa tace gata nan a gigice, sannan ta kira su Fadeela suma duk ta fad'a musu. A waje ta samu Abban yana jiran isowar ta, yace ta shiga ciki kar ta tara musu mutane, yana kiran waya, sai a lokacin ya samu labarin abinda ya faru da MD da Asma'u ta kira umman ta fad'a mata, har take tsoron ma ko Adam ne ya aikata, shi kansa Abban da ya samu labarin sai da tsoron hakan ya darsu a zuciyar sa, sai kuma ga kiran Maman akan an tafi da Adam.
Ciki ta shiga shi kuma ya kira Abuya dan yaji komai yadda zai fi fuskantar me yake faruwa mata suna da rudu da rikicewa, ba sa ma iya tsayawa su gama fuskantar abu saboda abu kad'an zai gigitasu. A lokacin Abdallah bashi da masaniya akan me yake faruwa a chan DSS office dan haka ko da sukayi waya da Abban, Abban be fuskanci wani abu da ya nuna akwai alakar Adam din da abinda ya faru ba. Rasa ta ina ma zai fara neman Adam din yayi, dama Abdallan yaso ya nemi alfarma saboda ba laifi sun san mutane sosai sai gashi suma suna cikin tasu matsalar ba zai iya kara masa wata ba, mijin Ya Hadiza ma kuma yana jin nauyin sa ba zai sake dauko matsala ya dora masa ba, yana tsaye a wajen be shiga ciki ba yana tunanin yadda za'a yi, dole nearest police station zasu je na chan unguwar su Hajiya mama su fara cikitawa ko za'a dace, Umar ya kira ya sameshi a wajen suka tafi ba tare da ya shiga gidan ba
RM
52-53
***MD na zaune bayan an fito dashi daga cikin cell din yana zaune a bayan kanta daga shi sai singlet da dogon wandon shaddar sa, duk ya fita kamannin sa duk kuwa da babu wani cin zarafi me muni da sukayi masa, cike cike suke karasawa sannan ya bada number wanda zai zo ya tafi dashi. Shigo da Adam akayi, suka watso shi ciki, cikin daga murya da hargowa suka hau tuhumar sa akan wayar, idanun sa ne suka fito waje cikin tsoro ya soma rantse musu akan bashi da masaniyar komai, wani daga gefe ne dan yaro karami ya taso ya hau tumurmusar sa, ya dinga ihu sai da yayi masa lilis sannan ya take kansa da kafarsa ya dago masa wayar
"Wayar waye wannan?"
Cikin tsananin azaba ya hau girgiza kai
"Wallahi tallahi ba tawa bace."
"Ta uban waye toh? Kuma a wanne dalilin ka saka abinda ka saka a motar Abdallah karefa?"
"Ni, wallahi ban saka komai ba, wallahi kaji na rantse ban saka masa komai ba."
Sake take masa kan yayi dama wani jibgegen takalmi ne a kafarsa, kara Adam din ya saka jin kamar zai tsinke masa jijiyar kan yahau magiya yana rokon yayi masa rai, dan daga kan nasa yayi kad'an ya sake maimaita masa tambaya akan wayar,
"Ba tawa bace ba." Ya furta cikin tsananin azabar da yaji.
" Oga wannan fa ba zai fadi gaskiya ba, sai yaci ubansa sosai sannan."
" Mu kuke jira? Da ba zaku bashi kashi ba?"
Oga Mausul yace yana barin rubutun da yake yi akan file din MD din. Tun kafin ya rufe baki suka farmasa da duka ta ko ina, MD na zaune kamar ya tashi ya tayasu haka yake ji, dan dai kawai yanzu burinsa ya tafi gida ne, tasowa Mausul yace yayi, yazo ya saka hannu ya rubuta number Abdallan,ya daga waya ya kirashi
"Capt Mausul daga headquarter na DSS kano division!"
Wani zillo Abdallan yayi daga zaunen da yake tare da su Baba Alhaji
"Yes sir, this is Abdallah speaking!"
"Malam Abdallah, muna tare da dan uwanka Mudassir Ibrahim Karefa a yanzu haka, kuma mun yi bincike mun tabbatar da gaskiyarsa, muna neman da kazo office dinmu ka tafi dashi."
"I ll be on my way in sha Allah, thank you so much, thank you."
"Sai kazo."
Yace yana datse kiran, kasa Abdallah ya durkusa yayi sujud shukur, Allah ne kadai yasan halin da yake ciki daga jiya zuwa yau da MD yayi a waje ba tare da yaji daga gareshi ba, babu komai a cikin sa tun safe suke garari a cikin Kano daga su fad'a nan sai suyi nan haka har kawo yanzu da suka samu kiran da suke ta jira. Sanar musu yayi da abinda ake ciki ya kuma zari car key yace zai tafi, fatan alkairi Baban yayi masa suka shiga mota suka nufi gida shi kuma ya dauki hanyar office din nasu da yake chan cikin wata unguwa da babu ma mutane a cikinta sosai. Tun daga titin farko ake tsaida shi suna rik'e da wasu manya manyan bindugu ga wajen yayi masifar shiru kamar ko tsuntsu baya iya giftawa ta wajen, sai da suka dinga amsa kira daga chan ciki sannan aka barshi ya shiga. Ya dinga mamakin wajen bayan ya shiga wanda yake tamkar kasuwa, mutane ne birjik ba zaka taba tunanin dasu a wajen ba, tsaf za'a batar da kai a cikin wajen dangin ka ba zasu sake jin labarin ka ba. Wani office wata karamar yarinya da bata fi shekara ishirin ba ta kai shi, ta tsaya daga waje tace ya shiga, ya shiga ya samu Mausul din a zaune, ya soma masa bayani dalla-dalla halin da ake ciki bayan ya bashi wajen zama ya zauna