← Book details Rayuwar Mace Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 66

Sashe 64

Rayuwar Mace Complete Hausa Novel · about 7 min read

" Baka ji ba kenan. " Ya tashi ya yi kansa, ya kama jibgar sa, da sauri suka shigo dan dama suna kallon komai suna daukar duk maganganun nasu, da k'yar suka raba su, daga nan suka shiga dukan G-boy  babu ji babu gani, da gefen bindiga wani ya saka ya farfasa masa baki, suka watsar a wajen, suka fitar da Adam suka sauya masa waje suka karasa shigar da report din kafin zuwa Capt Mausul.
  Zuwan Capt Mausul ya saka Adam din sanin abinda ake ciki akan sa, an same shi da laifin attempt murder duk da Allah ya kiyaye babu abinda ya faru, amma dole zasu mika shi kotu in da zata yanke masa hukunci daidai da laifin da ya aikata, domin hakan ya zama izini ga yan baya, masu shirin biyewa dokin zuciya.
   Abdallah Capt Mausul ya sake kira yace suzo shi da MD, yana office ma a lokacin ya kira MD din yace ya shirya zai dauke shi, dan tunda abin ya faru be fita ba, he need to heal from the trauma. Barin aikin da yake yayi ya fita bayan ya saka an duba masa lafiyar motar da zai hau sosai dan ya tsorata sosai, duk da sun karo tsaro sosai a wajen amma kuma duk da haka a tsorace suke da al'amarin mutane mara sa tsoron Allah.
   Gida ya fara komawa ya dauki MD din, anan yake fada masa in da zasu,ya tanbaye shi yadda ake ciki shima be sani ba, sai sun je zasu ji. Wannan karon ba kamar zuwa farko ba, suna zuwa aka barsu suka wuce kai tsaye, suka same shi a office dinsa yana karasa cike cike akan Adam din, hannu ya basu suka gaisa sannan suka zauna.

"Dalilin kiranku akan case din nan ne, mun kama yaron da muke zargi tun tuni, shi Adam ya taka sahun barawo ne, ya sakashi aiki daban shi kuma yayi nasa daban, yaron babban dan iska ne dan shi yake rabawa duk kauyukan katsina da zamfara makamai, yana kuma da daurin gindi amma duk zamu kamo su da izinin Allah."

"Wai, yanzu kun kama shi kenan."

"Eh yana ciki ma, dan har ma ya amsa laifin sa, duk da haka Adam na da laifi babba,wanda a shari'ance ake kira da attempt to murder, dan ya saka yaron ne yayi ya lalata maka motar yadda zaka iya mummunan hatsarin da ba lallai kayi surviving ba, tunda Allah ya takaita hakan bata faru ba, dole zamu gabatar dashi a gaban kotu domin ta yanke masa hukunci daidai da laifin sa. "

" Babbar magana, yanzu ace mutum musulmi zai iya sawa a kashe dan uwansa musulmi akan duniya? "

" Gashi ka gani, muna da cases da yawa ire-iren wannan din, wani ma kamar yadda kuke da Malam Mudassir hakà take da dan uwansa amma a karshe sai kaga bincike ya nuna shi a matsayin wanda ya kashe dan uwan ko kuma ya saka aka kashe shi, mutane sun shagala da yawa."

" Allah ya sa mu dace, Allah ya kiyaye mana imanin mu. "

" Amin ya Allah. "

" Please dàn Allah sir Adam yayi learning lesson, dan Allah karku bada belin sa har sai ya fuskanci hukunci me tsanani. " MD yace ransa a bace,

" Calm down aboki na, yau za'a gama komai a mika shi kotu, daga nan sai kotu ta yanke masa hukunci, bama wasa da duk wani abu da zai shafi al'umma, dole Adam ya fuskanci hukunci "

" Thank you sir, hakan shine adalci. "

" In sha Allah zamuyi kokarin mu, zaku saka hannu anan daga nan shikenan, duk wani abu da ake bukata zamu kira ku. "

" Ok . " MD ne ya fara sakawa sannan Abuya ya saka, sannan yace

" Maganar motar fa oga? "

" Mun gama magana akanta da Oga Ogidi, kuzo on 25th sai ku karba, Allah ya kiyaye gaba ya kara tsarewa. "

" Amin ya Allah, mun gode. "

" Anytime. " Yace yana tashi daga kujerar sa, ya rako su har wajen mota, ya sake basu hannu suka yi musabiha sannan ya koma ciki.

Duhu ya soma yi a lokacin dan haka suka tsaya a masallacin kan hanya sukayi sallah, sannan suka shiga wani eatery suka sai abinci suka ci a wajen suna tattauna abinda ya faru, da suka gama yayi wa Asma'un takeaway dan yasan a gajiye zata dawo ba kuma lallai idan hidimar sunan ta barta taci wani abu ba. Duba agogo yayi yaga karfe takwas ta dan gota, ya kirata yaji idan ta gama kawai su zo, tace ta gama sai kawai suka dauke hanyar zuwa gidan Raudan .

  Kayanta ta hada waje daya wanda tazo dashi a jikinta, da handbag dinta da yace mata gashi nan, babu nisa sosai daga in da suke nan da nan suka karaso ya kirata yace yana waje, tayi sallama da su Ya Hadiza da suka rage sannan ta fito ta same su a mota ya bud'e kofar bangaren sa.

"Assalamu alaikum!" Tayi sallama ya amsa yana dage mata gira, sannan ya zura hannu ta baya ya bud'e mota kofar bayansa, ta shiga ta rufo sannan ta gaida MD

"Anty barka da dare."

"Barka dai, Ina wuni?"

"Lafiya lou, Ashe an samu karuwa, Allah ya raya."

"Amin ya Allah."

"Saura na zama papa nima, Allah ya amsa."

"Kayi auren ne?* Abuya yace kansa na kallon titi

" Anty Asmy ce zata haifo min baby girl ko boy, kaji ana daddy daddy, ranar sai na zuba ruwa a k'asa na sha dan dadi. "

" Lallai, aiki ya same ka. "

" Babba fa, fatherhood is the best experience, kaji ana pampers din junior ya kusa karewa, bashi da cereal, ni kuma ina toh an gama,. "

Dariya ya basu dukka har Abuyan, suka kyalkyale da dariya yace

" Kinji fa? He's not serious at all. "

" Haka kake cewa kullum, Allah matar Abuya ki masa magana, kullum sai yace min haka, bayan kuma dai... "

" Anji, ya isa haka, kayi zuciya kawai kayi aure. "

" Dama dai akwai yar kanwar Anty Asmy, ni tsoron mata nake yanzu. "

" Basu da kanwa, cikin wadanda ka yaudara zaka samu daya ka kawo ta, na aurar da kai. "

Dariya ya fashe da ita, ya daki dashboard yana cigaba da kyakyatawa. Murmushi kawai Abdallah yayi, ya maida hankali akan tukin sa ganin garin akwai chunkoson ababen hawa, sai da suka bar cikin hold up din sannan yace

" Wifey yaushe zaki fara koyan mota ne, tana jiranki fa. "

" Gaskiya ya kamata, kaga shikenan sai kawai taja abarta duk in da zata. "

" Uhum? Yaushe? " Ya maimaita yana hango ta, ta cikin mirror, yayi kamar be ji abinda MD din yayi chagal yace ba

" Duk sanda kace. "

" Are you ready? "

" In sha Allah. "

" Shikenan zamu yi maganar,behind close doors idan mun sauke yan saka ido. "

Shiru MD yayi masa dan ya shaka sosai da sosai, hakan ya saka Abdallan yin dariya dan dama so yake ya kular dashi, yasan MD da saurin hayewa , idan ya dame shi da zuba haka yake masa ya saka shi a silent mood, har aka zo gida be sake cewa uffan ba, motar tayi shiru babu wanda ya sake magana. Ana parking ya bud'e ya fita ya zagayo ta side din Asma'un yace mata sai da safe, tunawa da tayi da jakar takeaway din sunan tayi, tayi saurin tsaida shi ta bashi guda daya, yayi godiya ya wuce tsohon part din su shida Abdallah da ya zama nasa shi kadai yanzu.

"Yayi fushi fa."

"Barshi, kafin ya kwanta zaki ga ya neme ni."

"Amma ba dadi fa."

"Idan ba haka nayi masa ba har muzo yana sakaki dani surutu, share shi muje ciki."

    Bin shi tayi a baya, suka shiga ya kunna hasken falon ya wuce toilet, ita kuma ta kai kayan ta daki ta dawo ta dauki ledar da ya kawo ta kai kitchen ta zuba abincin a plate ta hado da ginger drink me lemon tsami da tayi kafin ta fita, ta kawo falon ta ajiye, sai gashi ya fito rik'e da system dinsa a hannun sa, ya zauna ya dora akan center table din falon, da ido ta kalle shi sannan ta kalli abincin kafin tayi magana yace

" Naki ne, naci nawa, amma zan sha drink din. "

" Owk. "

Tace ta zauna a kasan ta zuba masa lemon ginger din ta ajiye masa a gefen system din sannan ta bud'e abincin ta soma ci dan dama tana jin yunwa idan ana taro kuma sune akan abun bata iya samu taci wani abinci, tana ta tunanin idan tazo sai ta dafa wani abun sai data ga ledar taji dadi dan dama ta gaji tikis girkin ma dan kawai babu yadda zatayi ne idan tazo sai tayi ko dan shi.
Chapter 64 · 0% Book details