Sashe 15
Rayuwar Mace Complete Hausa Novel · about 7 min read
Murmushin umman tayi, sak Asma'un itace, baki daya halayen ta irin na Umman ne shiyasa take tausaya mata, bata da zafi ko kad'an hakan ya saka tun da ma kowa taka ta yake, ballantana kuma ta hadu da miji irin Adam. Har suka isa asibitin ran Umman be saki ba, ta daure dai kawai suka shiga ciki. Adaidai lokacin Asma'un ta farka, zafin ciwon ne ya farkar da ita, babu wanda be tausaya mata ba, dan ma tana da masifar dauriya, gefe umma ta koma ta dinga share hawaye, zata sake lallaba Abba ita dai ya barta tayi jinyar yar ta, ko ta koma gidan ba zata taba samun nutsuwa ba, ba wai kuma dan tana ganin ba za'a yi Asma'un abinda ya dace ba, sai dan kawai dai wani abun dole sai uwa mahaifi.
Ganin su umman ya sakata sake jin ciwon na dawo mata sabo, tun bayan auren bata ga umma ba, dama jiyan take so ta tambaye shi taje ta wuni dan tayi kewar gida sosai, sai ga tsautsayin da ta gamu dashi.
Allura akayi mata da zata rage mata zafin ciwon, hakan ya saka ta dan samun nutsuwa. Kin motsawa nan da chan Hajiya Mama tayi dan tana tsoron ta bar su Asma'un ta fad'a musu abinda ya faru duk Adam din ya rantse mata be mata komai ba amma bata yarda ba, tana kyautata zaton yana da alaka me karfi da abinda ya farun.
Har yamma likis su umma na asibitin duk su Hidaya sun zo da yan uwan umman, Adam ma ya dawo amma be sake shigowa dakin ba tsakanin sa dai wajen zuwa wajen Drs sai idan abu ya taso haka suje da Abbati. Su kansu su Ya Hadiza sai da sukayi mamakin sa, sun ga sauyawar sa sosai har suka yi tunanin ko dama ya chanja bayan auren dan aure na chanja mutane da dama.
Bayan sun yi sallar magriba sun dawo da yaga an ragu sosai a dakin sai ya shigo, da sauri Asma'u ta rufe idon ta Hajiya mama ma ankare da ita, a dan baya ya tsaya ya gaida umman da rabon su dashi tun bikin, ta tambaye shi me jiki ya amsa kansa a k'asa tamkar ma kirki.
"Ya jikin?" Yace yana kallon gadon da take kwance, bata amsa ba ta sake rufe idon ta sosai, umma dake zaune daga gefe ta dan leko ta
"Inaga ta samu bacci."
Juyawa yayi ya fice duk suka bishi da kallo hatta Maman na cike da mamakin Adam din, kamar wanda aka chanjo mata shi da wani daban, shiyasa ta sake tabbatar da sanin sa, fatan ta daya Allah yasa ba turo yar mutane yayi daga benen ba ma, dan babu wanda ya san ainihin me ya faru ya dai ce zamewa tayi ta fadi.
Tana jin ya fita ta saki kuka me cin rai, bata son sa bata kaunar sa ko kad'an, bashi da tausayi bare imani ko na digo, kanta sukayi dukka kowa na tambayar ta menene, bata ce komai ba, ta dinga kukan ta a hankali wanda kusan duk sun dauki hasken dalilin kukan nata, yana da nasaba da shigowar Adam did, kunya duk ta kama Hajiya Mama, ta dinga borin kunya tana so ta dauke hankalin su daga kan Asma'un amma kuma sun riga sun gane komai.
Sanda su umma suka zo tafiya tayi bacci, dan haka bata san sun tafi ba sai chan wajejen sha biyu na dare da ta farka ta ganshi zaune akan kujera yana danna waya, kansa a kasa yana ta murmushi, wurga idon ta tayi zuwa sauran sassan dakin, babu kowa sai shi kadai ya bada dukkan attention dinsa akan wayar.
"Zan sha ruwa." Ta furta tana kallon gefe, dagowa yayi ya kalle ta, ya dauke kansa ya cigaba da danna wayar sa, ta sake maimaitawa a karo na biyu nan ma yayi biris.
Jujjuya hannun ta, ta dinga yi mara ciwon cikin jin ishirwa sosai, ta yi kokarin daukar na ajiye akan bedside drawer din asibitin amma ta kasa, yayi kamar be san me yake faruwa ba, sai da ya gama abinda yake tas, sannan ya tashi ya dauki ruwan ya mika mata. Kautar da kanta tayi alamun bata so, ya dire mata a wajen ya fice gami da jawo mata dakin!
_ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_
_ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
_BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_
_KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._
_WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU IN SHA ALLAH
_KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_
_SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_🥰
_BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍
_MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_🥰
_HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️
_NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍
***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_*
_BIYAR : DUBU DAYA (1k)_
_HUDU: 700_
_UKU: 500_
_BIYU: 400_
_DAYA: 300_
_AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE MU TA: _
*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*
Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank
Number shaidar biya👇🏼
*_09032345899_*
*KATIN MTN*👇👇
09166221261
______________________
ZAFAFA BIYAR
VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA)
VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA.
TWO PAGES DAILY
INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE.
*_TEAM ZAFAFABIYAR_*
RM
12
***Tun da ya fita be sake dawowa dakin ba, har drip din da yake hannun ta ya kare, jini ya soma biyo hannun. Tsoro taji, ta shiga kiran nurses din amma babu wanda ya shigo,akwai yar tazara tsakanin nurses lounge din dakin da aka kwantar da ita, gashi ba zata iys kashewa ba saboda dayan hannun ko motsa shi bata isa tayi ba, cigaba da kallon robar da drip din ke sauka tayi, wani guntun hawaye ya ziraro zuwa saman kuncin ta, ta gaji sosai da zubar da hawayen ta, zuciyar ta zafi kawai take mata, bata san dalilin da ya saka aka barta daga shi sai ita ba, ya kamata ace mace ta zauna ko da kuwa Yaya Hadiza ce idan Umma tana jin nauyin Hajiya Mama, ji tayi duk ta soma jin haushin su, tunda ita bata san abinda ya faru ba, Hajiya Mama ce ya kamata ta zauna amma sai ya nuna mata shi zai zauna, ya dinga mata magiya ganin cewa ai mijin ta ne ya saka kawai ta kyale shi, tana fatan dalilin hakan su gyaro matsalar su kafin wayewar garin.
Wucewa wata nurse tazo yi zuwa wani dakin sai ta duba ta ganta, tayi saurin karasowa dakin ta kashe drip din cike da mamakin ganin babu kowa a dakin sai ita kadai
"Babu wanda zai kiramu? Ke kadai kika zaune?"
Girgiza mata kai tayi
"Fita yayi."
"Ok, idan ya dawo kice ya daina nisa gaskiya ko a samo wata babba ta zauna dake aikin na mace ne ba namiji ba, ko ba a garin nan kuke ba? "
Tayi mata tambayar cike da mamakin idan har yar gari ce ai be kamata a barta da namiji ba, bata amsa ba sai kawai tayi shiru tana motsa yan yatsun hannun da suka gaji sosai, juyawa nurse din tayi ta fita tana mamakin dalilin da zai saka a barta ita kadai bayan dazu cike wajen yake da yan uwanta gal
Baki daya ma baya cikin asibitin dan sai da akayi asubah sannan ya dawo, bata runtsa ba saboda azabar ciwo haka ta dinga kuka me cin rai ita kadai kwal a daki kamar bata da galihu, Fido ce ta matsa masa da kira gashi ya rasa dalilin da ya saka baya iya kana kansa zuwa wajenta idan har ta kira din, sai yaje ya dawo yake jin haushin kansa, ya sha tama yi mata wulakanci amma sam ya kasa, ita kadai take juya shi son ranta duk kuwa da ita din ma wataran yana mata bore idan yan abun suna kusa dashi.
Ganin dawowar sa ya saka nurse din nan dawowa dakin, ta tarar dashi yana kokarin kwanciya akan couch din dake dakin, dakatawa yayi ganin ta shigo a tunanin sa ko magani zata bawa Asma'un
"Be kamata ka dinga nisa ba gaskiya, dan dazu Allah ya kiyaye nazo da wuri, baa so a bar mara lafiya shi kadai ko Yaya ne, idan akwai uzuri babba sai a nemo mace dattijuwa ta zauna da ita."
Wani kallo yayi mata irin na wacece ke, kafin yace a kufule
"Ina ruwan ki? Bana son gulma da munafurci malama."