← Book details Rayuwar Mace Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 66

Sashe 38

Rayuwar Mace Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tashi yayi, yayi hanyar fita Nadeeya da Mama suka bishi da sauri, kafin su karasa har ya shiga mota ya kwanta a bayan motar, zuciyar sa zafi take masa kamar zata ballo ta fito, ga wani matsanancin ciwon kai da ya addabe shi, har baya iya bud'e idon sa sosai.
Abdallah na tsaye jikin mota shi da MD da yake waya suka fito akan idon sa suka tafi, wayar sa ya zaro ya aika mata da text message

"I love you."

Sai ya kashe wayar ya zura ta a aljihu ya daga kansa sama, yana kirga yawan taurarin da suke sararin samaniya. Umar ne ya dawo yace su shigo ciki, dan dama tafiyar su Adam din suke jira, da hannu MD yayi masa alamar yaje zai zo, yayi gaba yana jin iska na kada shi, Asma'u dake daki umma tace ta fito, ta tashi tana nannade sallayar da take kai, ta bud'e dakin ta fito, hannun ta umma ta kama zuwa dakin ta, ta dauko wani turare me kamshin gaske ta fesa mata sannan tace taje tana da bako , bata ce komai ba ta fita, a ranta tana ayyana waye?. A daf da kofar da zata shigo ya tsaya, ya kura wa kofar ido kamar ba zata fito ba, sanyayyan kamshin turaren ta ya iso masa tun kafin ta karasa shigowa, tana bud'e labulen ta ganshi a tsaye, ya bud'e hannun sa baki daya, yana mata wani irin mayatataccen kallo, bata yi aune ba sai ji tayi ya rungume ta tsam a jikin sa.

Page 31

RM

Hafsat Rano

***Kokarin kwace kanta tayi, ya sake matse ta sosai kamar za'a kwace masa ita, jikinta ne ya hau rawa kamar mazari, ta saka karfi sosai ta ture shi,dan ita bata san duk abinda yake faruwa ba.

"Bana so."

Tace masa tana ware masa idonta sosai, bakin ta ya tsuke kalar tsiwa dan babu abinda ta tsana a rayuwar ta kamar irin wannan rayuwar yanzu da samari da yanmta sukeyi. Murmushi ne ya kufce masa ya saka hannun sa ya sake jawota da karfi ya matse ta gagam yadda ba zata iya kwacewa ba, ya zagaye ta da hannayensa masu taushi yana shakar kamshin jikin ta, kuka ta fashe masa dashi dan ganin abun nasa ya wuce gona da iri, ta dinga kokarin kwacewa amma sam ya hanata, be san me ya hau kansa ba, ji yake kamar idan ya cikata zata barshi, ga wani irin bugawa da zuciyar sa take kamar zata fito waje. Sautin kukan ta a hankali na shiga cikin kunnen sa, duk da haka be sake ta ba, sai da bugun zuciyar sa ta daidaita, sannan ya cikata yana matsawa baya, ta juya da sauri zata bar dakin, ya riko ta da hanzari

"Karka kara tabani dan ni ba yar iska bace."

"I'm so sorry ba zan kara ba."

Ya kama kunnen sa ya rik'e yana so ya saka kwayar idon sa a cikin tata, rasa abinda zatayi tayi, kawai tayi shiru tana duban kasa, dan ta fad'a masa ita bazawara ce shine zai rungume ta kenan, mutane da yawa irin kallon da suke ma wadanda sukayi aure suka fito kenan, shiyasa ko mazan sun zo wajen su sai su bisu da maganar banza, bata zaci haka daga gareshi ba, amma kuma idan ta tuna duk mazan halin su daya, ba ka iya gane musu sai kawai ta sallama. Knocking akayi, kafin ya turo ya shigo hade da sallama.

"Amaryar mu."

"Uhumm." Tace tana sake yin kicin kicin da fuska dan ta lura ma bakin su daya

"Kinga yadda abu ya kasance ko? Al'amarin Allah kenan, babu yadda bata kasancewa. "

" Allah ya bada zaman lafiya da zuria dayyiba, I can't wait na ga na zama daddy wallahi, woo wa yaga Daddy Mudan. "

Harara Abdallah ya watsa masa yana rik'e kansa, surutun MD yayi yawa wallahi, a duhu ya sakata Dan bata fuskanci komai a maganar tasa ba,tunani ta shiga yi, ta tuna dazu wajen magriba Abba ya shigo ya sameta, ya tambaye ta idan har ta amince da Abdallan, tace masa eh, daga nan ya fice da sauri bayan yace wa Umma yana zuwa da bayani. Bata kaao komai ba, ganin basu dade da tafiya ba, daga nan kuma ta shiga sabgar gabanta dan bata ma fito ba saboda Adam yana nan. Muryar MD ta katse mata tunanin ta, ta kuma kara tabbatar mata da abinda take tunani ya faru

"Zamu shirya duk events din a satin sama in sha Allah, komai ake bukata ni za'a tambaya, please."

"Yayi toh, can you please excuse us?"

"Why not? Idan ma cewa kayi na tafi gaba daya anan zaka kwana kaga lafiya lou, idan kuma kayan ka ma zan kwaso maka ayi duk shirye shiryen kana nan shima daidai ne."

Kunya maganar ta bashi, yayi masa banza yana masa kallon zaka sani, shi dai MD dariya kawai yake yi , ita kuma Asma'u tsabar shiga ruduni ta gaza cewa komai, idan har maganganun MD din gaske ne, kenan aure aka daura mata da Abdallan, ji tayi kafafun ta sun mata nauyi, taji tana bukatar ta zauna dan har yar rawa jikin ta ya dinga yi, a wajen ta durkushe MD na fita, yayi saurin zuwa ya durkusa akan guiwoyin sa yana rik'e hannun ta

"Me yake damun ki!? Baki da lafiya? Wani abun ne?"

Girgiza masa kai tayi, ya sauke ajiyar zuciya yana sakin hannun ta da ya tuna tace masa bata so, kasa kallon sa tayi, ta dinga jujjuya maganganun a ranta, ba zata ja da hukuncin Allah ba, ba kuma zata bijire masa a duka abinda ya zaba mata ba, zata karbi duk wani zabi da hannu bibiyu, hzd ehakan ta tabbata yana cikin kaddarar ta, babu wanda ya sake magana a cikin su, tana durkushe a wajen shi kuma yana tsaye kyam a kanta yana nazartar yanayin ta, be san a wanne matsayi ta ajiye shi ba, dan yana ji da ganin kamar ba'a kyauta mata ba, kamar an mata garaje da ba'a barta ta tantance shi sosai ba, duk da yasan hakan ba zai zama matsala ba,kuma hakan zabin Allah ne.

Mikewa tayi bayan ta dau lokaci a durkushe sannan tace

"Kayi hakuri."

Be san hakurin me take bashi ba, amma sai ya samu kansa da jin dadi, ya daga mata gira yana sakar masa tsadadden murmushin sa, maida masa tayi tana sunne kanta k'asa kunyar shi na ratsa ta,

"Zo ki zauna."

Yace mata yana nuna mata gefen sa bayan ya zauna, ba musu ta karasa a nutse ta zauna da dan tazara kad'an a tsakanin su, matsowa yayi ya jone da jikinta har kafadarta tana gogar tasa, hannun ta ya lalubo ya rik'e cikin nasa yana dan murza su a hankali, yanayin bugawar zuciyar ta ya sauya nan take, ta dinga jin wani irin yanayi da bata taba fuskantar sa ba. Ta zata wata magana xasuyi amma sai taji shiru har ta dago da niyyar ganin abinda yake amma sai taga kawai ita yake kallo kuri, duk sai taji kunya amma shi ko a kwalar rigar sa., Sai ma sake tsattsareta da yayi yana kokarin lallai sai ya saka idon shi cikin nata, sun jima a haka kafin yayi ta maza ya daure ya cikata yana mikewa

"Bana so na tafi, but i have to, kar Abba yaga rashin hakuri na."

Shafa kansa yayi ya mikar da hannun sa zuwa gareta, ya mikar da ita tsaye suna fuskantar juna

"My wife."

Ya kawo fuskarsa daidai tata ta hanyar rage tsawon sa, dan tsaf zai sakata a cikin rigar sa ya boye ta, dago idon ta, tayi da niyyar kallon sa, sai yaga kamar tayi masa fari, wani yarrr yaji tun daga kansa zuwa tafin kafarsa, bakin sa ya kai kuncin ta s kasalance ya manna mata kiss, ta duka da sauri tana damke idon ta

"Ki kula min da kanki kinji?"

Bata iya amsawa ba sai daga kai da tayi alamar toh, cikin sakannin da basu gaza goma ba ya fice fit daga falon dan abinda yake ji zai iya sashi aikata abun kunya. Yana fita ya tarar da driver yana jiran sa, MD ya tafi shine ya kirashi yazo ya dauke shi, babu bata lokaci ya fad'a bayan motar ya ja suka bar layin.

Tamkar wadda aka dasa a wajen haka ta kasa ko da daga kafarta ne, wani feeling me matukar dadi ya dinga mata yawo, soyayyar sa me sanyi da tsayawa a rai, bata taba experiencing hakan ba, baa taba nuna mata so irin haka ba, shiyasa take jin ta kamar wata bakuwa, kamar wadda aka chanja ta da wata ta daban. Da k'yar ta ja kafafunta zuwa cikin gidan nasu, kunyar Umma da Abba na sake dabaibaye ta. Idon Umma fes akanta ta shigo, sai taga kamar umman ta kara mata haske akan hasken ta da ta Santa dashi, bata sani ba ko tsantsar farin cikin da ta hanga a cikin idon ta ne ya sakata ganin farin nata ba, zuwa tayi ta zauna a gefen Umman tana jan mayafin jikinta ta sauke shi k'asa.

"Umma ina Abba?"

"Ya fita sallah, inaga ko ya tsaya wajensu liman."

Sai kawai ta fad'a jikin Umma, ta dora kanta a kafar umman ta runtse idon ta, tana tariyo abinda ya faru yanzu.

"Nasan ba dan dare ba, babu abinda zai hana yan uwanki zuwa, amma nasan gobe da wuri zaki gansu, dan duk munyi waya kowa murna wallahi."

"Umma wai ya akayi haka ta kasance?"

"Al'amarin Allah fa, ke dai ki bar sha'anin aure wallahi."
Chapter 38 · 0% Book details