← Book details Rayuwar Mace Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 66

Sashe 43

Rayuwar Mace Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tashi yayi ganin yadda curtains din dakin ke dagawa ya daga yana kallon yadda hadarin ya hado sosai, hannun sa daya na rik'e da wayar dayan kuma ya zura shi wajen yayyafi kad'an kad'an na sauka akan hannun nasa, yana son yanayin damuna a rayuwar sa musamman ruwan dare, yana yawan kwatanta kansa da mai iyali a irin wannan weather din, sai da yaji ruwan ya soma karfi sosai sannan ya zare hannun sa, ya rufe glass din yana cigaba da wayar, har kusan sha biyu da rabi sannan yayi mata sallama shima ba dan yaso ba, sai dan ganin dare yayi. Alwala taje tayi, tazo tayi raka'a biyu kamar yadda ya umarce ta da zasu ajiye wayar, tana idarwa ta haye gado nan da nan bacci me dadin gaske, irin wanda ta dade bata yi irin sa ba ya dauke ta, bata tashi ba sai da Umma tazo ta tashe ta sallar asubah. Ita kanta umma ta lura da chanji a tattare da ita, da taje tashin ta, da yanayin da taga ta tashi. Kiran sa ne ya shigo wayar tana kokarin shiga toilet, ta dawo ta daga cike da zakuwa

"Kin tashi?"

"Eh."

" Na zata na sakaki makara, bari muyi sallah, bye."

Jallabiyar sa ya zura ya fito, ya kwankwasa ma MD kofa ya wuce yana jin motsin sa alamar ya tashi.

***Fido na zaune ita da Faiza Adam ya dawo, ya shigo ba tare da ya kalli in da suke ba, ya shige dakin sa ya rufo kofar, tashi tayi ta bishi, taje ta murda kofar amma sai taji ta a rufe, tsaki tayi ta hau bubbugawa tana kiran sunan shi

"Man ba zaka bud'e ba, wannan wane irin wulakanci ne?"

Yana jinta yayi banza kamar baya dakin, ta dinga bugu kamar zata zare amma ko gezau be ba, bare ya tashi daga ruf da cikin da yayi a saman hargitsattsen gadon sa da ya kwana biyu baa gyara shi ba. Kwafa tayi ta dawo wajen Faiza, ta saka mata ido tana kwashewa da dariya

"Saboda soyayya ta rufe miki ido, har kike ganin a kyale shi zai sakko ya kulali, ai wallahi in dai ba maganin sa kikayi ba a yadda yake hayakin nan tsaf zai dangara miki saki. "

"Yanzu ai na dawo hayyaci na, kije kawai ki same shi duk abinda ya kamata kiyi, ki biya ko nawa ne, sai ya gane ni ya wulakanta wallahi, aure kuma babu saki ko yaji zai gane kurensa. "

" Yanzu kike magana, da kin tsaya iyayi ai kallon ki kawai nake. "

" Shiga ki dauko wani abu sai na wuce yanzu ma, kinsan da zafi zafi ake dukan karfe. "

Tashi tayi ta shiga dakin ta, ta dauko mata kudi ta bata, ta tafi ita kuma ta koma kofar dakin nasa tana cigaba da bugu, bata ji takun tafiyar sa ba, sai kawai ji tayi ya banko kofar ya fizgo ta, ya zare belt ya shiga tafkar ta babu kakkautawa, sai da yayi mata shegen duka sannan ya watsar da ita a wajen ya haure ta ya fice daga gidan, be san in da zashi ba, kawai mota ya shiga ya dinga zagaye, sai chan dare sannan ya dawo gidan ya shige dakin sa, ido biyu sukayi tana zaune tana jiransa a dakin, yana shigowa tayi kukan kura da chakume shi, yadda tayi masa bazata ne ya bata sa'a a kansa, ta dinga kai masa duka da yakushi ko ta ina, kamar mahaukata haka suka koma a gidan, suka lalata abubuwa da yawa a dakin kafin ya rufo ta a ciki da key ya dawo falo ya kwanta. Kusan kwana tayi a tsaye tana dura masa zagi, yayi kamar be ji ba, tunda ya samu ya garkameta shikenan, ba zai iya da hayaniyar ta ba dan babu alamun zata gaji, shi kuwa yanzu ba ta ita yake ba, baya ma son ko ganin me kama da ita kuma yana jira ne da zarar ya samu kan Asma'u zai kada keyar ta, su dawo su ci zaman su da Asma'un cike da so da kaunar juna, duk abinda yake ita kawai yake gani ba zai kuma taba samun nutsuwa ba har sai ta dawo gareshi.
Da duku duku ya tashi ya fice daga gidan duk da ya daina jin motsin ta wanda yake kyautata zaton tayi baccin wahala dan ya jigata ta sosai bayan uban cizo da yakushin da ta yi masa, baya saka ran dawowa gidan nan kusa dan ba zai juri ganin ta tana zuwa in da yake ba, sai yayi gaba kawai ya je ya samu daki a hotel ya biya kudin sati dan idan ya zauna a gidan su ma surutun Mama da mutane ya isheshi

***Duk yadda Hajiya Mama zatayi wajen boye masa maganar auren Asma'un tayi, ta kuma hana kowa gaya masa idan yayi mata maganar sai tace suna magana da Abban ne komai ya kusa daidai ta, hakan ya sakashi rage damuwar da yake ciki har yake tsayawa yayi wanka ya gyara jikinsa, tsakanin sa da Fido tun ranar da suka saida hali, tasan guduwa yayi, sai ta rabu dashi tana tama shi dan saura kiris ya shigo hannun ta,daga nan ne zai gane shi din karamin dan bariki ne dan sai ta zame masa tamkar rakumi da akala.

_ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_

_ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

_BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_

_KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._

_WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU  IN SHA ALLAH

_KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_

_SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_🥰

_BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍

_MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_🥰

_HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️

_NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍

***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_*

_BIYAR : DUBU DAYA (1k)_
_HUDU: 700_
_UKU: 500_
_BIYU: 400_
_DAYA: 300_

_AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE  MU TA: _

*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*

*KATIN MTN*👇👇

09166221261

______________________

ZAFAFA BIYAR

VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA)

VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA.

TWO PAGES DAILY
INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE.

*_TEAM ZAFAFABIYAR_*

*RM*
     33

****
Rauda ce ta fara zuwa tana kwance tana bacci bayan tayi sallar asubah ta koma sai ji tayi an danno kanta, ta bud'e idon ta tana ayyana Rauda din ce, da sauri ta tashi tana dubata

"Amma Allah Rauda baki da kai sam, wai bakya jin nauyin jikinki ne?"

Turo baki tayi tana dariya

"Farin ciki ne wallahi, babu fa abinda nayi na fito zai tafi office yace nazo ya ajiye ni, yasan ba zan iya zama ba shima."

"Shi yake biye miki ma Allah."

"Ina umma?"

"Wai bata san kinzo ba ma?"

"Ai direct nan nayo, nasan tana dakin Abba luf zan sai ya fito ya tafi kar yayi min fad'a."

"Aikuwa sai na fallasa ki."

Tace tana sakkowa daga gadon tayi hanyar toilet

" Ki rufan asiri dan Allah, kinsan Abba fad'a zai yace na fito na bar shi."

" Aifa sai na fad'a."

Ta shiga ta kuskure bakin ta sannan ta dawo ta zauna a gadon tana fuskantar Raudan

"Yaushe zai zo?"

"Wa?"

"Yaya Abdallan."

"Ban sani ba, kin karya?"

"Banci komai ba fa, me akayi ne yunwa ma nake ji."

"Nima yau umma bata tashe ni ba, bari na dubo mana kitchen din muga."

Mike kafa tayi ta saka pillow a bayan ta bayan Asma'un ta fita, ta dauki wayarta ta shiga call log taga wayar da sukayi da shi, murmushi ta saki tayi saurin ajiye wayar ganin sako ya shigo alamar text kuma shi ya turo, dadi take ji sosai Asma'un ta samu me.sonta da gaske, halin ta na kirki yafi dacewa da miji na kirki na gari, jin ta dawo ya saka tayi saurin kife wayar tana kallonta dauke da flask da cups ta ajiye sannan ta koma ta dauko sauran kayan, kunu da kosai ne Umman tayi hade da taimakon sabuwar me aikinta da tayi bayan bikin Asma'un, sakkowa tayi da k'yar suka yi breakfast din suna hira, sannan Asma'u ta sake kwashe kayan ta maida kitchen, ta wuce dakin Abba dan ta gaishe shi, ta same shi ya shirya yana cin dumamen tuwo da Lipton da ya zamar masa al'ada, fuskar sa ce ta fad'ad'a da fara'a cike da farin ciki ya amsa gaisuwar ta yana dorawa da tambayar babu matsala ko? Be ga wani abu tattare da ita da zai nuna masa rashin amincewar ta ba, hakan ya kara masa karfin guiwa ya bita da addu'ar fatan nasara a dukkan al'amuran ta na rayuwa, sannan ya jawo drawer sa ta falo ya ciro sadakin ta ya mika masa

"Ga sadakin ki nan Allah ya baku zaman lafiya."

Kin karba tayi, ta tashi zata bar dakin yace dole ta dawo ta dauka saboda hakkin ta ne, ganin ya dage sosai ya sakata dukawa a kunyace ta dauka sannan ta sake mika masa

"Abba gashi toh ko za'a yi wani abun dashi, ni babu abinda zanyi dashi."

Girgiza kai yayi yana kin karba

"Hakkin kine, abun da za'a yi miki kuwa hakki na ne, kamar yadda nayi wa kowa a cikin yayana, dan haka ki je ki ajiye anjima Abbati zai karba sai ya saka miki a account zai miki amfani ko gaba."
Chapter 43 · 0% Book details