← Book details Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 155

Sashe 96

Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

shige batare damin maganaba. Da wannan damar nai zaman kuka na kusan awa ɗaya kafin wata tazo cikin wanda muka fara tararwa a falon farko ta kama hannuna muka fice. In taƙaita miki Granny tun daga ranar zazzaɓina ya ƙaru, inaga ganin yanda nake galabaita yasa Hajiyarnan ɗaukata a washe gari takaini wani asibiti mai ƙyau da alama na kuɗine. Anan aka bani gado. Sosai likitan yaytamin tambayoyi harnaji nama ƙosa dashi, amma na daure dan lafiyata nake nema ai. Kwanana shidda a asibitin nan na warke sarai aka sallamoni, sai dai kuma hajiya ta kaini wani gida ba nata da aka fara kainiba, naji tsoro sosai, dan can babu kowa sai wata dattijiwar mata mai suna Harirah. Ɗaki guda aka bani a gidan, wanda yaji duka kayan more rayuwa, ni harma abin ya ban mamaki amma sai ban tambayaba tunda dai ance aiki nazoyi. Komai na nema ina samu a gidan, amma sai dai a tsorace nake, dan haka kawai na kasa yarda da sakin jiki da baba harirah, sai dai kullum sai ta shigo ɗakina ita ta sakani shan magungunana na asibiti da aka bani. Hajiyar kuma ban sake ganintaba sai bayan kwanaki sai gata. Cataimin na shirya muje asibiti likita ya sake dubani, ban kawo komai a raiba na shirya na bita zuciyata fal fargaba. Munje likita ya sakemin gwaje-gwaje, sai yace wai akwai wani ciwo dake damuna zasu ban magani. Daga wannan maganar aka kaini wani ɗaki, tunda akaimin wata allura ban sake sanin inda nakeba sai a gida. Ni kuma tunda na farka sai tsoro ya kamani ganin ko baba harirah ɗinma yanzu babu, sai wani gardi abin tsoro dake a waje. Hankalina ya tashi, da ƙyar na samu nai wanka nayi salla. ina idarwa na saka kayan danazo dasu daga gidan hajiyar farko da aka kaini, ALLAH ya taimakeni na silalo na fito daga gidan, ɗari biyar ɗin da hajiyar ta bani da zata tafi lokacin data kaini can gidan itace ta taimaka mani na koma Danya. Koda na koma kuma saina kasa bama kowa labarin abinda ya faru har Babana, duk da inason na faɗa masa kodan kalmar iskanci da Inna ke dangantani da shi sai dai inajin tsorone”. Shiru hajiya iya kawai tai tana kallon Zinneerah kamar mai karanto komai akan fuskarta, sai dai wani irin tausayin yarinyar da ƙaunarta na sake shigarta. Dan yanda take bata labarin a nutse sai take ƙara godema ALLAH da samunta matsayin matar jikanta mafi soyuwa a ranta. Ta ɗan murmusa cike da basarwa tana faɗin, “Uhmm lallai dole ki kasa mantawa da birnin katsina. To amma ita hajiyar data kaiki gidan baki koma gidantaba bayan kin baro can?”. “Wai Granny sokike na koma ta sake maidani, nifa wlhy haka kawai naji banason hajiyarnan data kaini asibiti, ta cika tsare gida da mulkin tsiya kamar sarki”. A karon farko Hajiya iya tai dariya da juyawa tana kallon AK datun fara maganarta da Zinneerah ya shigo ɗakin, sai dai jin labarin da Zinneerah ta fara badawa ya sakashi dakatawa batare daya shigoba. Yanda ya kafe Zinneerah da idanu yana ma labarin nata fashin baƙi da nazartarsa yasa hajiya iya faɗin, “Amma baki taɓa gamo da maikama da wancan mutumin a katsina ɗinba?”. Sai a lokacin Zinneerah ta farga da AK, duk da ta jima tanajin ƙamshinsa a hancinta bata kawo shi baneba. Kallo ɗaya tai masa tai saurin maida kanta ƙasa saboda yanda kwarjininsa ke cika mata idanu da zuciya. Cikin girgiza kai tace, “A'a Granny, anan na fara ganinsa nikam”. “Inno bafa wasa nakeba”. Da iya gaskiyarta tace, “Wlhy kuwa Granny”. Hajiya iya zata sake magana AK ya katseta da faɗin, “Kin shirya ne na kaiki gidan Gwaggon?”. (mmn sadiq). Tsaf hajiya iya ta fahimci dalilinsa na katseta, dan haka tai guntun murmushi da cewa, “Eh bara na kimtsa, ai hada Inno ma zamuje saimu barta acan dan da safe idan ALLAH ya kaimu zata dawo akwai inda zan turata”. Baice komaiba sai duban Zinneerah ɗin datai ƙasa da kanta yaɗanyi, ya ɗauke idanunsa ya juya ya fice. Binsa da kallo Zinneerah tayi, tana ganin ya fice ta sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya da har sai da hajiya iya tai murmushi.............✍
Chapter 96 · 0% Book details