← Book details Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 155

Sashe 80

Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

      A ɓangaren Farah kam kamar yanda bata fito ta nema kowa ba babu wanda ya nemeta. Sai dai mai aikinta dake ɗan shiga da fita zuwa ɗakinta lokaci-lokaci tana kai mata abunda ta buƙata, itama batasan AK yabar gidanba sai a bakin mai aikin nata daya barma saƙon cewa ta sanar mata yabar abu a ɗakinsa. Sosai hakan yayma Farah ciwo, badan tana tsoron hukuncin Mahma ba da wlhy saita bar masa gidansa. Bata kira Mammah ba sai aunty Zakiyya. Mammah kuma saita tura mata text message akan tafiyar AK ɗin. Ta kuma tabbatar mata wani ƙullin AK ya tafi yowa a Nigeria danya binne abinda ya shuka akan yaron. Itama kanta Mammah ranta yay matuƙar ɓaci da tafiyarsa bai sanar mataba. Hakan yasa ta shiga gayama Mahma rai a ɓace.
    Murmushi kawai Mahma tayi, a nutse tace, “Duk ke kikaso hakan Hindatu, na daɗe da nuna miki tsaurinki akan Abdul-Mutallab bashike nufin zaki iya rabasa da mahaifinsa ba. Adilah mace ce zaki iya tanƙwarata ko bataso tamiki biyayya. Amma Abdul-Mutallab namiji ne, su kuma maza da kike gani kullum tunaninsu dabanne da namu, suna da saurin hango kuskure idan sun so hakan, sai dai su ɗauki mataki kosu bari wannan zaɓinsu ne, dan hakan a jininsu yake. Ni banga dalilin da zaisa kicigaba da damuwa da alaƙar da ALLAH ya haɗaba, tun ran ginifa tun ran zane, kuma da uba ake ado kema kin sani. Inba hakaba miyasa sanda Mama ta koma Morocco kika dawo london kika zauna da Daddy? Ai da saiki bita can kota hanaki zama anan ɗin wajen Daddyn. Yakamata ki dawo da hankalinki jikinki, dan amatsalarki da Kabeer daban ki daina ƙoƙarin saka yaranku a ciki, hakan bazai haifar miki da ɗa mai ido ba. Da yawan labarai a tarihi maza ke nuna ƙarfa-ƙarfa wajen amshe ƴaƴa a hannun uwa idan ƙaddarar rabuwa ta ratsa, sai dai abinda mutane basu saniba ko suke gaza tunawa idan mu mata muka sami damar nasarar karɓe yara a hannun ubansu bisa irin wannan ƙaddarar munfi mazan atsabibancin cusama yaran aƙidar ƙin uban koda ace mune da kaifi a wajen haifar da rabuwar auren. Ya kamata ki dawo cikin hankalinki, ki daina azabartar da Abdul-Mutallab da laifin Kabeer. Dan na fahimci haushin Kabeer kike saukewa akan Abdul-Mutallab akowane lokaci, wannan itace kawai gaskiyar dazan iya gaya miki dan karkiyi biyu babu. Daga lokacin da zuciyar Abdul-Mutallab ta fara raya masa tsaurinki yayi masa yawa to tabbas zaki rasashi ki kuma rasa Adilah itama dan zatabi ɗan uwanta kodan so da shaƙuwar dake a tsakaninsu mai ƙarfi”.
       Mahma ta miƙe tabar mata wajen tana gama faɗa. Da kallo kawai Mammah ta bita batare data iya cewa komaiba. Tabbas gaskiya Yayar tata ta sanar mata. Sai dai bataji a ranta zata ɗauka dan itafa bazatabarma Kabeer da uwarsa ƴaƴanta ba. Dan ita tasha wahala akansu bawani shege ba. Zata riƙe ƴaƴanta shima ya riƙe nashi daya tara da shegen aure-aurensa da idan ta tuna sukafi baƙanta ranta fiye da komai. Taɗau alwashin zatayi yaƙi mai girma akan tabbatar da cigaban wanzuwar ƴaƴanta tare da ita duk wuya duk rintsi.

*_NIGERIA_*

       Koda AK ya iso Nigeria Baffah yayi mami matuƙa, amma da yake shima a yunwace yake da son ganinsa sai hakan yay masa daɗi. Ko gaisuwar kirki basuyi zaman yiba AK ya sanarma Baffah abinda ya kawosa. hundred percent Baffah ya gamsu da hakan, shiyyasa ya shiga saka masa albarka. a take kuma ya kira Mmn Sadiq. Bayan sun gaisa itama kamar yanda suka saba cike da girmama juna, ya sanar mata hukuncin da suka yanke.
      Sosai mamakin hakan ya kama mmn sadiq. Cikin sanyin jiki tace, “Ya ilahi, Yaya mufa bamun faɗa muku labarin nan bane domin zargin Adnan akan kamanninsa da Little”.
     Murmushi Baffa yayi mai faɗi, ya gyara zamansa yana faɗin, “Nasani Hauwa'u, muma kuma ba hakan bane a ranmu wlhy, sai dai ki sani tun randa kukazo da yaron nan gidannan babu wanda zuciyarsa ta huta akan kamaninsa da Adnan a gidan nan. Jin gaskiyar samuwarsa tasa muke kwaɗayin yin gwajin ko hakan zai sama mana kwanciyar hankali, dan nayi alƙawarin saina ƙwatoma Zinneerah haƙƙinta awajen koma wanene. Yanzuma bayan anyi gwajin insha ALLAH gobe idan ALLAH ya kaimu zamuje can asalin ƙauyen nasune. Dan haka banason zuciyarki ta ƙara miki wani hasashe daban bayan ƙyaƙyƙyawa”.
      Sosai raunin mmn sadiq ya bayyana, tace, “Shikenan yaya, ALLAH ya saka da alkairi yabar zuminci. Bara nama Yaya magana to dan yana gida sai mu kawosa kawai”.
     “Hakan shine dai-dai, mu haɗu a shira hospital daku”. Daga haka Baffah ya yanke wayar.

      Wanka kawai AK ya samu yayi bayan Safiyya sunje sun gyara masa ɗakinsa da falon ɓangaren hajiya iya, abincima bai iya ciba sai tea yasa Ni'ima ta haɗa masa. daga haka ya fito ya sami Baffah dake zaman jiransa yana waya rai ɓace.
    Shiru yay yana nazarin wayar ta Baffah, inda kai tsaye ya gane da Mammah suke waya, runtse idanunsa yayi da ƙarfi jin yanda Baffah ke dasama Mammah baƙaƙen maganganu, wanda ya tabbatar itace ta fara masa, shiko yake maida mata murtani.
    Juyawa yay a hankali zai fita ya jiyo kalaman Baffah da suka sakashi dakatawa a kausashe.
      “Komi zakice kice Hindatu, wlhy da banma kawo hakan a rainaba game da Adnan. Amma wlhy kinji na rantse a wannan gaɓar zan tabbatar miki da cewa ni Kabeer Abdul-Mutallab Shira nine mahaifin Adnan, ba kuma tsoronkine yasa na barmiki shiba daga shi har ƴar uwarsa. Dan haka muzuba mu gani ni dake ɗan hakal ka fasa”.
   Daga haka Baffah ya yanke wayar yama kasheta gaba ɗaya dan baya buƙatar ta sake kiransa..............✍

*_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_*

Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻.

*_★ AL-ƘIBLA_*💘
_Na Safiyya Huguma_

*_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖
_Hafsat Rano_

*_★ DALAAL_*💝
_Na Miss xoxo_

*_★ UBAYD MALEEK_*💓
_Na Mamu gee_

*_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔
_Na Bilyn Abdull_

Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻.

Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  0903 234 5899

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

*_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_*

 *_TYPING📲_*

*_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_*

_________________________

*Page 39*

..........Da sauri AK ya ƙarasa ficewa ransa na masa ƙuna da wannan halayya na Mammah, bashi da burin daya wuce ganin iyayensa sun sasanta kansu sun koma rayuwar aurensu, sai dai ya gwada ƙoƙarin yin haka yafi sau a ƙirga abin ya gagara. Kuma Mammah ce ke bada matsala a koda yaushe. Tunma Baffah na nuna masa zai amince shi, har takai yanzu idan yay masa maganar Mammah saiya ja masa warning.
         A mota ɗaya suka tafi ran kowa babu daɗi, dan haka motar ta ɗauki shiru sai driver daketa aikin tuƙi har suka isa Shira Hospital.
    Tuni AK ya tanadi likitocin da zasu aikin harsu uku domin samun gamsuwa akan abinda zai fito, dan haka suna isowa suma su Mmn Sadiq suka iso ɗauke da Little.
      Yanako ganin AK ya maƙale masa, duk da ɓacin ran da AK ke ciki sai da yay murmushi yana mai rungume little a jikinsa. Ganin yaronma da yayi sai yakeji a ransa ALLAH ma yasa ya kasance nashi ɗin, dan har cikin ransa wata irin ƙauna yake masa mai ƙarfi da saka zuciya nutsuwa.
     Cikin mutunta juna suka gaisa, inda mamaki ya cika Dr Mahmud saboda ganin Abba. Shima Abba daya ganesa sai wani tunani yazo masa. Cikin kasa jure abinda ke ransa yake tambayarsa ko ina bawan ALLAHn nan daya sakama little sunansa?.
    Kai tsaye Dr Mahmud dake dariya ya nuna AK, “Baba ai gashima zaune, ina takwaran nasa kuwa? Nasan ya girma yanzun ko?”.
       Da sauri Abba ya kalli AK da Little ke a jikinsa zuciyarsa na bugawa. Cikin ɗan rawar murya yace ai ga yaron nan a hannunsa”.
      Ba Dr Mahmud ba, hatta AK sai da zuciyarsa ta harba. Yay saurin duban Abba da faɗin, “Uncle kana nufin kaine wanda ya bani damar zaɓama yaro suna shekara uku data shuɗe?”.
     “Tabbas nine kuwa. Kuma wannan shine yaron”.
     Sosai maganar Abba ta sakasu jin shock su duka. Baffah dake saurarensu ya nemi jin ƙarin bayani. Dr Mahmud ne yay masa bayanin komai har yanzu firgici da al'ajabin kamannin little da AK na bayyane a fuskarsa.
      Murmushi baffa yayi yana jinjina kansa. Sai dai komai baiceba yabarma zuciyarsa. Dan yama gama yarda AK na ɓoye masa wani abune game da yaron kenan, inba hakaba yaya akai hakan ta faru? Tunda a wannan zuwan basusan yazoba sai a shanun ƴan talla yaji. To lallai kam zaiyima tufƙar hanci, dan yama gama yanke hukunci saura zartarwa.

       Baffah ne ya dakatar da wannan hasashen su Dr Mahmud suka shiga aikinsu. Duk wani gwaje-gwajen daya dace akan ƙwayoyin haluttar little da AK akai musu. Abinka da masu abu, ba'a wani zauna wasaba suka shiga ganin sun tantance komai dan Baffah yace bazasubar asibitinba sai da result.......

_________________________★

       *DANYA*
Chapter 80 · 0% Book details