← Book details Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 155

Sashe 17

Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

..........Ko tsayawa fahimtar a ina taji ciwon direban baiyiba. Kasancewarsa mutum tamkar ruɗaɗɗe, abu kaɗan ke gigitashi. A yanzu hakanma jikinsa sai rawa yakeyi.
     “Dan ALLAH ku taimaka a sata a mota muje asibiti karta rasa ranta”. Ya faɗa a gigice da rawar jiki saboda jinin dake zuba a jikinta da basusan ko daga ina bane.
      Suma kansu yanda ya rikice ɗin sai hankalinsu ya ƙara tashi, ga yarinyar tunda tai ƙarar farko bata sake ko motsiba alamar numfashinta ya rabu da gangar jikinsa. Ga jinin dake fita a jikin natama tashin hankaline mai zaman kansa.
     Wani abokinsa driver ne daya tsaya  a wajen kamar yanda yaga motoci nata tsayawane ya nufesu a rikice. “Ya ilahi, Naziru Accident kukayi haka?”. Cike da tashin hankali ya bashi amsa. “Wlhy bugeta nayi Malam Abubakar, sam banga yarinyarnan ba sai da mukazo gab da ita. Nayi ƙoƙarin kauce mata kuma hakan ya gagara”.
        “Hasbinallahu wani'imal wakil. Inaga to kusata a mota, wasu ƴan motar taka saisu dawo nan wajena tunda ba mutane sosai”.
     Kowa yayi na'am da wannan shawaran, dan haka a take sukayi hakan kuwa. Cikin kano suka ƙarasa shiga, inda kai tsaye suka nufi wani asibin kuɗi kamar yanda wani a motar ya bada shawran, dan sunsan yanzu idan sunje na gwamnati wani sabon turancine zai tashi na maganar ƴan sanda da sauransu. Cikin amincin ALLAH suna zuwa kuwa aka amshesu kasancewar ansan shi wanda ya bada shawaran. Ashema yana taɓa aiki a asibitin. Da taimakon wannan bawan ALLAH aka shiga bama Zinneerah da batasan ina kanta yakeba taimakon gaggawa.

           Alhmdllh kusan awa ɗaya da rabi saurayin nan da likitan da suka taimaketa suka fito, fuskar saurayin da murmushi yace, “Alhmdllhi kowa ya kwantar da hankalinsa komai yazo da sauƙi, cikin ikon ALLAH ma bataji wasu ciwuka masu tsauriba, sai dai cikin jikinta da ƙyar aka samu ya tsaya, saboda shi ne ma zamu riƙeta dan tana buƙatar kasancewa a ƙarƙashin kulawar likita na kamar sati biyu zuwa uku haka”.
         Ajiyar zuciya drivern ya sauke. Hakama sauran fasinjojin da sukai karar biyosu duk suka shiga ambaton Alhmdllhi. Sai dai kuma hankalin drivern a wani fanin a tashe yake. Da damuwa yace, “Amma zamanta sati uku a asibitin nan zan iya shiga wani hali ɗan uwa. Kuɗin gado kansu aikine babba a gareni”.
        Murmushi saurayin yayi yana dafa kafaɗarsa, yace, “Karka damu za'asan yanda za'ai insha ALLAH. Idan kuma yarinyar ta farka ai dolene musan daga ina take? A nema iyayenta da mijinta ko”.
        Ajiyar zuciya ya sauke yana gyaɗa kansa. Daga haka suka fita zuwa massallacin da basu tayar da sallaba su har yanzun.

          Bayan an idar da salla daga can sauran fasinjojin kowa ya kama gabansa. Da ga shi Naziru direba sai abokinsa Abubakar da saurayin nan da ya faɗa musu sunansa Khalipha suka dawo asibitin. Sun sami damar shiga dubata yanzu kam. Tana kwance an saka mata ruwa. Sai hanunta dake ɗaure da bandage alamar taji ciwo a wajen, sai gefen kanta shima da sauran gurare jefi-jefi. Kasancewar an cire mata kayan dauɗar jikinta an saka mata na asibitin kalar green sai taɗan canja kamanni kaɗan. Duk da idanunta a rufe suke sun fahimci dai ta farfaɗo barci takeyi yanzun, dan haka sukaji daɗi har cikin ransu, a fili kuwa suna ambaton Alhmdllh tare da mata fatan samun lafiya. daga haka suka fita domin biyan kuɗi suma suɗanje gida kuma.

*BAYAN KWANA UKU*

         Kwana uku Zinneerah na samun kulawa a asibitin da taimakon Khalipha dake tsaye akan komai. Dan koda direba Naziru ya bada iya kuɗin da ALLAH ya hore masa Khalipha ɗinne ya ƙara wasu aka biya kuɗin gado harna kwana goma, yace idan da buƙatar tafi waɗanan kwanakin sai asan abinyi. Alhmdllh jikin nata da sauƙi, dan ƙananun ciwukan harsun fara nuna alamar warkewa saboda bata da ƙan jiki, sai dai hannun natane take kuka da shi dan ta samu tsagewar ƙashi ne. Amma shima Alhmdllh yau ta tashi da sauƙi.
       Abu ɗaya ke tadama su Khalipha hankali, shine da zaran dare yayi babu zaman lafiya. Tata zabura kenan akan saita fita a asibitin. A daren farko sun ɗaukama tanada taɓin hankaline, hakan yasa suka danna mata allurar barci mai ƙarfi sosai, wadda ta jata har washe gari da rana tana barci. Sai da likita yay bincike kamar yanda Khalipha ya buƙata sannan suka fahimci lafiyar ƙwaƙwalwarta ƙalau sai dai kuma wani abu daban da basu saniba.
      A dare na biyu kam tana farawa wani tunani yazoma Khalipha. Kafin azo ai mata allura ya shiga tofa mata addu'oi, tun tana ɗan fisge-fisgen kaɗan da faɗin ita a barta ta tafi har ta fara lafawa, sai kuma gashi kafinma ayi allurar barci mai nauyi yay gaba da ita. A ranar haka Khalipha ya kwana da abin nan a rai, dan ji yake a ransa tamkar ya santa ko yanada alaƙa da ita. Dare na uku ma tana farawa ya fara mata addu'oin nanma sai gashi ta lafa. To a yau Alhmdllh bayan an cire mata ruwan da aka saka mata Khalipha ya saka wata Nurse ta taimaka mata aka goge mata jiki da duk abinda zai taimaka mata.
     Kusan ƙarfe bakwai sai ga Naziru direba da abincin karyawa kamar yanda ya jura kawowa kullum, da rana kuma almajiri yake kawo mata. Idan kuma ya dawo aiki yakan zo asibiti yay kamar awa guda sanann ya wuce gida. Hakan da yake yi nama Khalipha daɗi, shiyyasa baijin ƙyashin taimaka masa akan jinyar yarinyar dako sunanta har yanzun basu sani ba.
        Sai da aka gama kimtsata sannan suka shigo ɗakin. Fuskar Naziru washe da fara'ar jin daɗin ganin jikin nata yaketa ambaton, “Alhmdllhi, Alhmdllhi. Kai naji daɗin ganinta haka Malam Khalipha, ALLAH ya saka maka da alkairi, nagode-nagode”.
      Murmushi Khalipha yayi idanunsa akan Zinneerah shima yace, “Ai ƙoƙarin ka ne da adalcinka ya kaimu ga wannan nasarar Malam Naziru. Da ace guduwa kayi bayan kawota nan muma bazamu sami ƙwarin gwiwar taimakonta ba, dan direbobi da yawa idan irin haka ta faru guduwa suke subar majinyaci a asibiti koda kuwa ya zama gawa. Yanzu inaga jikin nata Alhmdllh gaskiya, ya kamata musan sunanta da inda ta fito dan mu nema iyayenta da mijinta kodan abinda ke a cikinta”.
     Cikin washe haƙora Naziru yace, “Wannan gaskiya ne Malam Khalipha”.
       Duk wannan magana dake fita tsakanin Khalipha da Naziru Zinneerah na zaune ne a gadon kanta a ƙasa tana saurarensu. amma ko sau ɗaya bata ɗago ta kallesu ba tanata faman wasa da yatsun hannunta ne kawai kamar bata a wajen ma.
       Nurse ɗin dake a gefenta ta ƙarasa gyara mata abinda ya rage ta fice ta barsu. Sai a lokacin su Khalipha suka ƙarasa inda take suna mata sannu. Yanzunma bata ɗago ta kallesu ba. Sai dai cikin rawar murya tace, “Ina yini”. Daga haka tai tsit.
     Wannan shine karon farko da sukaji muryarta tana cikin hayyacinta, dan haka sukaji daɗi har cikin ransu. Khalipha yace, “Masha ALLAH, yau dai naji muryar ƙanwata”.
       Batace komaiba, kamar yanda bata ɗagoba. Bai damuba, dan ya fahimci akwai damuwa tattare da ita. Zama yay a bakin gadon daga can ƙarshe, dan haka tai saurin janye ƙafafunta data miƙe ta naɗesu. Baice komaiba, sai ma Naziru ne yaja kujerar roba shima ya zauna a kusa da shi. Su dukansu idanunsu a kanta suna kallonta cike da tausayi, dan shekarunta sunyi ƙanƙanta da fuskantar lalurar ciki irin haka a ganinsu.
      “Ƙanwata!”.
Khalipha ya kirata cike da kulawa..
      A karon farko ta ɗago taɗan kallesu, sai kuma tai azamar maida kanta ta duƙar batare data amsa masaba. Ya ɗan murmusa da sake faɗin, “Ki saki jikinki munan duk yayunkine kinji, munason miki wasu tambayoyine, ko zaki taimakemu da amsa?”.
      Kanta a ƙasa har yanzu ta gyaɗa masa kanta. Shima kan nasa ya gyaɗa cike dajin daɗin tana fahimtarsu. Ya cigaba da faɗin, “Minene sunanki?”. Shiru bata amsaba. Fahimtar bazata faɗaba ya sashi sake cewa, “A wane anguwa kike anan kano?”. Yanzu kam kanta ta girgiza masa.
      Cikin rashin fahimta yace, “baki san anguwarba ko ba'a nan kikeba?”.
    Kanta ta ɗaga masa.
Naziru ya amshe da sake faɗin, “Ba'a nan kike ba?”.
      Kanta yanzu ma ta kaɗa musu.
Kallon junansu sukai da mamaki, kafin Khalipha yace, “A wane gari kike to?”.
       “Nima ban saniba, na manta komai”.
    Ta basu amsa a fisge tana ƙara ƙasa da kanta alamar gajiyawa. Nanma kallon juna sukai cike da mamaki da fargaba. Naziru zai sake magana Khalipha ya girgiza masa kai alamar su barta kawai.
      Badan Naziru yasoba yay shiru, Khalipha ya miƙe yana faɗin, “Yauwa to bara na turo sister Salima ta baki abincin kici, dan nasan kina bukatarsa”. Daga haka ya kama hannun Naziru suka fice batare da ya jira amsawarta ba.
         Bayansu tabi da kallo har suka fice, ta sauke nannauyan ajiyar zuciya tana lumshe ido. haka kawai take shiga takura da shiga wani yanayin da batasan dalilinsa ba a duk sanda Khalipha ya kasance a ɗakin.
Chapter 17 · 0% Book details