← Book details Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 155

Sashe 27

Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

      Kamar yanda ya bada wakilci ga Dr Mahmud hakance ta faru, dan har ɗakin da aka kwantar da Zinneerah Dr Mahmud yaje yayma yaro huɗuba. Ya kuma ajiye kuɗi dubu hamsin shima yace asai rago a yankama takwaran abokinsa, kuma ogansa ranar suna.
      Shima sun masa godiya sosai, kowa na jinjinawa a ransa yaro yazo da farin jini. yayinda Maman Sakina keta taɓe baki a kaikaice, a ranta kuwa tana ganin tsabar iya asirine na ƴan ƙauye kuma Katsinawa da kullum take ambata ga maman Sadiq.
          Tare Alhaji suka fita da Dr Mahmud. Sai bayan kusan mintuna talatin ya dawo ɗauke da madaidaicin kwali da aka zubo masa magungunan da Doctor yace su sayo da drips, sai jini leda ɗaya. Kwalin Maman Sadiq ta amsa takai ɗakin dan sun fito waje. Tana fitowane yake faɗin, “Wani iko sai ALLAH, kunga jininma da naje nema a lab ɗin nasu saina samu bawan ALLAHn nan ya bada nasa a ajiye idan masu bukata sunzo nema. Cikin ikon ALLAH sai gashi ni na fara zuwa kuma. Gashi sun bada ƙyauta babu ko sule”.
      Cikin riƙe haɓa Maman Sakina da hassada kecin ranta tace, “Oh har jini yake zuwa ya badar a asibitin kuma? Dan tsabar jin daɗi irin na masu arziƙi”.
     Alhaji ya bata amsa da cewar, “Wlhy kin gani dai, dama likitan daya kira mani shi a waya yace jinin yazo badawa kawai shiyyasa bai jimaba ya tafi”.
        Sudai su Maman Sadiq godiya suka sakeyi da jera masa addu'oin gamawa da rayuwa lafiya.

★★★

         Sai yamma Zinneerah ta farka sosai cikin hayyacinta, bayan an cire mata jinin da aka gama ƙara mata. Bayan likita ya shigo ya fita suma su Maman Sadiq suka shiga. Zaune suka isketa jingine da filo ta zubama yaron dake gefenta yana barci ido. A zahiri shi take kallo, amma idan ka nutsu kaima a kallonta zaka fahimci sam batama tare da duniyar mutane gaba ɗaya. Dan yaron kuka yake iya iyawarsa amma da alama ba jinsa takeba.
     Matar Naziru ce tasa hannu ta ɗauki yaron tana faɗin, “Haba Zinneerah, yaro na kuka ke kuma kin tsaya kallonsa kawai”.
     Nan ɗinma ba jinta tai ba. Sai da Maman Halima ta taɓata sannan ta kawo numfashi. “Oh ni Binta, mi kike tunani haka Zinneerah?”.
    Maman Halima ta faɗa tana tsatstsareta da idanu. Ƙasa kawai Zinneerah tai da kanta tana ƙoƙarin haɗiye kukan daya tokare mata ƙirji tun ɗazun. Matar Naziru dake jijjiga yaron dai yay shiru tace, “Haba Zinneerah ai yanzu ba lokacin kuka bane, lokacibe da zamu taru mugodema ALLAH ne. Jiya iyanzu muna nan cikin tsananin tashin hankali da fargabar rasaki, amma cikin amincin UBANGIJI yau gaki zaune da ƙyauta mai girma da wasu kecan suna bulayin nema da kuɗi amma ALLAH bai ƙaddara samuwarta garesuba. Kiyi haƙuri kibar kukan nan, mu yanzu babban fatanmu kuma ALLAH ya baki lafiya mu koma gida”.
       “Maganarki kam gaskiyace Maman Abu. Zinneerah yanzu lokacine na godiya ga ALLAH kinji. ALLAH ya ƙara miki lafiya. Kinga yaron nanma ya kamata a bashi abincinsa dan wannan kukan bana komai bane sai na yunwa, tunda likita yace zaki iya ɗan gwada bashi yanzu sai a gwada ɗin ai ko”.
       Sake fashewa da kuka Zinneerah tayi, dan ita kaɗai tasan yanda takeji a ranta akan wannan al'amari mai rikitarwa da matuƙar ruɗani. Tunda take bata taɓajin labari irin nataba. Tayaya zaka haifi ɗa na mutum batare da kasan yanda ka samu cikinsa ba. Anya kuwa yaron nan baɗan wani aljanin baneba?......
      Shigowar Alhaji da Maman Sadiq da gayyar yaran gidan gaba ɗaya har da ƴaƴan Maman Sakina ya katse mata tunani. A take kuma ɗakin ya kaure da hayaniyar yaran. Dan bayan sun mata yaya jiki gaba ɗaya hankalinsu suka maida ga ɗan jinjirin suna yaba ƙyawun da ALLAH yay masa. Sai da Maman Halima taga kukansa na ƙara ƙarfine ta amsheshi cikin tilastawa suka saka Zinneerah bashi abincinsa tanata kuka.
      Alhaji da Maman Sadiq ne kawai suka iya fahimtar kukan Zinneerah saboda sune sukasan labarin tushen samuwar yaron. Dan ita kanta maman Sadiq konawarsu gida tasha kuka, a yanzu hakanma kukan zuci takeyi. Su Maman Halima kuwa da basusan dawan garinba sai tunaninsu ke basu Zinneerah tana kukane saboda tunawa da mahaifin yaron da akace rasuwa yayi.
     Da ƙyar aka samu ta bari yaɗan kama na wasu mintuna. Dan kuka take sosai tana yarfa hannu wai zafi. Maman Halima ta ɗaukesa tana mata faɗa akan karta sakama ranta fargabar tsotso dan yaron nan daga gani ba wasa zaiyi da cikinsaba. Ita dai Zinneerah zamewa ma tai ta kwanta a hankali tana matse baki dan inda aka yankata na mata ciwo sosai har yanzun.
      Sun daɗe a asibitin yaran na cigaba da jagwalgwala yaron da aka samu yay shiru, yayinda Zinneerah ke kwance shiru bata sake kula kowa ba. Idonta a lumshe suke tana zirar da hawaye ta gefensu, yayinda hancinta ke shaƙar daddaɗan ƙamshin turaren dake manne da jikin showal ɗin yaron da batan a ina ya kwasoshi ba.
       Ƴar hayaniyar yarance ta saka Doctor shigowa ɗakin yace suyi haƙuri a barta ta huta hakanan, ya kuma bada damar a bata abu mara nauyi tasha, kamar shayi ko kunu haka. Godiya sukai masa ya fice. Alhaji kuma ya tattara iyalansa shima sukai musu sai da safe suka tafi. Aka barta daga ita sai Maman Halina dake haɗa mata kunun da akace zata iya sha ɗin.

_____________★

        Haka Zinneerah ta cigaba da jiyya a asibiti. yayinda abokan arziƙin Maman Sadiq na anguwa da dangi ɗai-ɗai dake anan suke ɗan shigowa dubata. Kulawa da take samu na abinci ya saka komai yake tafiya kan tsari Alhmdllh. Dan jikinta yayi ƙyau sosai a kwanki shidan data ɗauka a asibitin. Idanma ba'a faɗa makaba bazaka taɓa ɗauka cs akai mataba. Sai dai sam babu mai ganin walwalarta, sannan ko kallo yaron bai ishetaba sai Maman Halima ta mata jan ido.
     Matsalar da suke fuskanta da yaron kawai shine idan yasha nono cikinsa sai ya kumbura yayta kuka. Da farko basu fahimci hakanba sai suke ɗauka cibiyarsa ne ke ciwon. Sai daga baya Doctor ya gane inda matsalar take. Dan haka ya dakatar da Zinneerah daga bama yaron nonon gudun kar a cutar da yaron kuma. Sai dai sun ɗorata akan magani zuwa wani lokaci sai ta cigaba da shayar da shi. shi kuma yaron suka bada shawarar a ringa bashi madara.
      Hakan yama Zinneerah daɗi, dan a shirementa ayyanawa take a ranta ta huta da ciyar da ɗan aljanu, dan har cikin ranta ta yarda aljanune sukai mata ajiyar yaron kawai a cikinta.
     Babu wanda yasan da wannan shirmen nata, sai dai ranar tsabar jin daɗi har ɗan sakin jikinta tai sukai hira da Maman halima da ada take danganta rashin walwalar Zinneerah ɗin da rashin ƙarfin jiki.

       Washe gari Alhaji ya sayi raguna biyu aka raɗama yaro suna Abdul-Mutallaf a masallaci, wato dai takwaran AK Shira kenan kamar yanda akai masa huɗuba. Ba ayi wani shagaliba kasancewar mai jego na asibiti, sai dai maman Sadiq tayi abinci ta bada sadaka ko zata samu sassauci a ranta da nutsuwar rugumar wannan ƙaddara a garesu.
        Da yamma da sukazo dubasu a asibiti Alhaji yake sanarma Maman Halima cewar yaro yaci suna Abdul-Mutallaf.
     Cike da murnarta da farinciki taita jera addu'a ga jariri tana tsokanarsa. Zinneerah kam ko motsi bataiba balle ta nuna taji sunan da yaron yaci. Sai dai tausayinsu da takeyi akan sunatama ɗan aljanu hidima batare da sun saniba. Ta tabbata wataran sai aljanin daya ajiye mata ɗan yazo ya ɗauke ɗansa batarema dasun saniba zasu gane wahalar banza sukayi. Babu wanda ya damu da rashin tankawar tata. Garama maman halima taɗan mata faɗa kamar yanda ta saba idan taga tana share yaron. Shiru dai tai batace komaiba kamar kullum, sai hawayen data share a ɓoye duk da ita Maman Sadiq na lure da ita.

         Ganin komai normal ta samu lafiya Alhmdllh washe gari aka basu sallama. tare da basu ranakun da zasu dawo domin duba lafiyarta. Daɗi sosai Zinneerah taji da wannan sallama. dama ba ƙaramin gundura tayi da zaman asibitinba.
        Koda suka dawo gida sun sami ƙyaƙyƙyawar tarba daga yaran gidan, dan harda ƴaƴan Maman Halima na ma'auri duk sunzo gidan tarbarsu, dama duk sai da sukaje asibiti anan nema Zinneerah ta fara saninsu. Amma yanda suka karɓeta saika ɗauka a cikinsu ta tashi itama.
     Yau ɗinma tararwa sukai sun haɗa wata ƴar ƙwarya-ƙwaryar liyafa iya su kawai ƴan cikin gidan, sai ƴaƴan Naziru da matarsa da maƙwafta na kusa da ake gaiswar mutunci. Kowa yayi mamaki dan babu wanda yasan da wannan shirin nasu. Maman Sadiq zata hana Alhaji ya hanata akan kartace komai, dan sudai basusan komaiba akan wannan haihuwa ba. Sannan kosu ɗin da suka sani ai Zinneerah batasan sun saniba. Su daure su ƙarfafa farincikinta har lokacin da za'aje gaɓar da tuhumarta zatai musu amfani, kuma dalilin hanyar samuwar ɗan bazaisa su toshe hanyoyin karɓar ƙaddarar da yazo a cikintaba, da har zasu ƙi farinciki ko nuna godiyarsu ga ALLAH.
      Badan tasoba ta haƙura ta zuba idanu itama.
     Ita dai Zinneerah bata nuna wani alamun damuwa da hakanba, dan tunda suka shigo gidan Maman Halima tai mata gashi na musamman a jikinta sai ta samu nutsuwa sosai, aka kawo mata abinci kuma taci ta ƙoshi tasha magani sai barci. Sai gashi har suka gama walinarsu ita bama tasan wace waina suke toyawaba, sai bayan ta tashine su Aunty Halima suka shigo sukai mata sallama zasy wuce gida dan lokacin anyi sallar isha'i.
       Yanda suke nuna mata so da ƙauna su da mahaifiyarsu yasa itama take sakin jiki dasu sosai, kuma tanajinsu tamkar yayunta, dansun maye mata gurbin su Yaya Gajejen ta.............✍

*_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_*

Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻.

*_★ AL-ƘIBLA_*💘
_Na Safiyya Huguma_

*_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖
_Hafsat Rano_

*_★ DALAAL_*💝
_Na Miss xoxo_

*_★ UBAYD MALEEK_*💓
_Na Mamu gee_

*_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔
_Na Bilyn Abdull_

Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻.

Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
Chapter 27 · 0% Book details