Sashe 22
Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
............Tunda suka iso gidan Zinneerah keta kalle-kalle. Basai an faɗaba a ganin gidanma kasan mahaifiyar tata yanzu kam tai gaba, kuma tana cikin jin daɗi da kwanciyar hankali. Bawai ƙaton gida baneba irin na masu kuɗi, babbane dai kam amma gini irin na mai rufin asirin ALLAH. Dan da Alhaji Bashir Ɗanmusa kam yayi kuɗi sosai, sai dai daga baya ya fuskanci ƙalubalen karayar arziƙi, tun daga nan ne dai har yanzu bai koma yanda yake daba, amma ko a hakan Alhmdllh dan yana iya ɗaukar nauyin komai na gidansa harma ya taimakawa ƴan uwa da maƙwafta. Hatta da motar da Nasiru keja a yanzu haka shine ya siya masa ita. Sannan duka ƴaƴansa suna karatu gwargwadon ƙarfinsa danshi mutumne maison ganin zuri'arsa ta samu ilimin addini dana zamani.
Zinneerah ta samu tarba maiba mamaki a gidan na kawunta, kuma mijin mamanta. Hakama yaran gidan duk da ba saninsu tayiba suma basu santaba sunzo sun zagayeta sunata kallo. Bata wani sake da kowa ba dan har yanzun damuwar tafiyar Khalipha bata saketa ba. Tanajin raɗaɗi da zafi a ranta wanda ita kanta batasan dalili ba.
Duk da a yanayin da take na rashin sakin jiki hakan bai hana Mama Sadiq nuna zumuɗin ganintaba, danma tana ɗan kawaicine wa Maman Halima kasancewar Zinneerah ƴar fari ce, sannan kuma yanda Maman Haliman ke nuna kara ma ta cancanci a ɗaga mata ƙafa ai. A yanzu hakama duk da tare suka dawo a ɗakinta ta sauketa. Sai dai an kawo kayan Zinneerah ɗakin Maman Sadiq ɗin alamar anan zata zauna.
Da ƙyar Maman Halima ta lallaɓa Zinneerah taci abincin da Maman Sadiq ɗin ta tarbesu da shi, bayan ta ɗan tsatstsakura aka kaita tai wanka, tare da bata kaya sabbi fil da Maman Sadiq ɗin ta ɗiɗɗinka mata a ƴan kwanakin nan gudun kar'a sallamosu tazo babu sitirar da zata saka, dan a yanzu haka gidan nasu ƴammatan dake sa'annin Zinneerah duk ƴaƴan Saude ne, Saude kam ba bari zatai su bama Zinneerah kayaba, ballema yaran suma sun rigada sun haddace karatun uwarsu suma kishi suke da su, danma sunajin tsoron ubanne, suma kansu su Maman Sadiq ɗin kuma basu basu fuskar rainiba suna ɗan shakkarsu.
A zahiri Maman Sadiq cike take da murnar kusantowar ɗiyar tata kusa da ita duk da batasan dalilin barowarta gidaba har yanzun. sai dai ƙasan ranta cike yake da fargabar yanda Zinneerah taƙi sakin jikinta ita. Haka dai ta daure ta danne damuwarta a ƙasan zuciyarta bayan sallar isha'i da Zinneerah ta dawo ɗakin nata bisa rakkiyar Maman Halima. Alhaji yayi tafiya, hakama Saude bata gidan, tana can gidansu bikin ƙanwarta akeyi, yaran natama suna dawowa Islamiyya da yamma yau suka bita can. Dan haka gidan ya kasance daga ita Maman Sadiq sai Maman Halima. Sai yaran Maman Sadiq uku duk maza ƙannen Zinneerah data haifa anan. Abubakar Sadiq, Abdul-Salam, sai Aliyu auta. Itako Maman Halima yaranta duk matane, huɗu sunyi aure ma, sai biyu yanzu a gabanta ƴan biyune sa'annin Sadiq. Sai itama Saude nada biyar, yanzu haka akwai ƴammata biyu da suka isa aure, sai ɗaya zasuyi kusan sa'a da Zinneerah, da ƙannensu biyu ƙanana suma kusan sa'annin su Sadiq ɗin dai.
Sosai Saude take kishi da Maman Sadiq saboda tazo gidan ta haifi ƴaƴa maza su basu haifaba, taso su haɗe kai da Uwargidan da suke kira maman Halima amma taƙi, dan dama itama ɗin can ba zaman lafiyarne a tsakaninsuba, to mizaisa ta yarda su haɗe su cuci wani bayan ALLAH shine mai badawa. Kuma koda Maman Sadiq tazo gidan batazo musu da raini ba, su duka girmamasu takeyi dan mace ce mai sanyin hali, sai dai idan ka ƙureta kam zaku kwasa da ita. Shiyyasa duk haukan da Saude zatai a gidan ko kallonta batayi, sai idan ta kaita maƙurane ta yaɓa mata maganar da zatai kwana da kwanaki tana damunta a rai.....
Numfashi Maman Sadiq taɗan sauke da duban Zinneerah dake a takure gefe tana magana dasu Sadiq dake zagaye da ita a hankali. Tanajin misu Sadiq ɗin ke faɗa, amma batajin na ita Zinneerah ɗin. Gashi kuma ta duƙar da kai bata ko kallon sashen da take.
“Abdul!”. Ta kira sunan yaron nata na tsakkiya da yafi kowa ƙiriniya a yaran, dan a yanzu haka kusan rabin jikinsa na manne da na Zinneerah ne, gashi dama suna kamanni sosai da ita.
Kansa ya ɗago ya dubeta, “Na'am Mama”.
“Ku tashi aje ai shirin barci hakanan, duk kabi ka katantaneta bakaga halin da take ciki bane”.
Baki yaron yaɗan tura gaba da faɗin, “Ayya mama ki barmu muyi barci tare da ita, muna sonta sosai”.
A karon farko Maman Sadiq taga Zinneerah ta saki murmushi tana shafa kan yaron, sai dai bataji mita faɗaba sai da yaran suka haɗa baki wajen cewa, “Muma ai muna sonki sosai” ne ta gane cewa tai tana sonsu itama.
Murmushi tayi tana maijin daɗi da farin ciki a ranta, ta sake faɗin, “Karku damu ai tana nan tare da ku babu inda zata, kuje ku kwanta akwai islamiyya gobe idan ALLAH ya kaimu”.
Badan sunso ba sukaima Zinneerah sallama suka nufi ɗakin barcinsu. Shiru falon yayi na tsahon mintuna. Ita dai Maman Sadiq kallon Zinneerah ɗin takeyi cike da nazari, itako kanta a ƙasa tana wasa da zanen carpet ɗin dake shimfiɗe a falon.
“Zinneerah.”
Ta kira sunanta cike da rauni.
Karon farko Zinneerah ta ɗago ta dubeta, sai kuma taɗan risinar da idonta. Murmushi mai ciwo Mama tayi, ta sake faɗin, “Taso ki dawo nan”.
Babu Musu Zinneerah ta miƙe zuwa gareta. Sai dai kamar bazata zauna inda ta nuna mata ɗinba, sai kuma mita tuna oho ta zauna a hankali gab da Maman nata. Mama dake cigaba da kallonta ta riƙo hannunta cikin nata tana gyara zama da fuskantarta sosai. Hakanne ya saka Zinneerah maida kanta ƙasa idanunta na cika da ƙwalla.
Itama Mama idanun nata cike suke da ƙwallan, cikin rawar murya tace, “Kiyi haƙuri Zinneerah, kiyi haƙuri kiyi haƙuri. Na fara da baki haƙuri ne saboda dalilai masu yawa. Nasan har ranki kina kallona ne matsayin uwa gareki mara adalci. wadda ta wofantar da ke ta manta da rayuwarki. Wlhy Zinneerah ba hakan baneba. Ni mahaifiyarki ban taɓa mantawa dakeba koda na daƙiƙa guda. A kowane sakanni kina maƙale a raina da zuciyata. Hawayena basu taɓa jinkirin fitowa ba a duk sanda na tunaki. Duk wanda ke tare dani yasan hakan Zinneerah. Nisantarki da nai itace babbar jarawar da har yanzu na kasa cimmawa wajen cinyeta, sai dai Alhmdllh, tunda yau gani gaki a yanda ban taɓa tsammataba ko tunani. Inason ki daure ki cire komai a ranki ki saki jiki dani ko hakan zai ragemin raɗaɗin ciwon gyanbon dake maƙale a zuciyata kinji”.
Hannu Zinneerah tasa ta share hawayen dake sakko mata daga idanu zuwa kumatu, cikin rawar harshe tace, “Amma miyasa baki taɓa zuwa gareniba mama”.
Murmushi Mama tayi itama tana sharar nata hawayen. “Zinneerah bana cikin hayyacinane, koda na baro ƙauyen Danya a yanayin ciwon hauka na barosa, sai dai Alhmdllh ALLAH ya taƙaitamin wahala maimakon na nufi wani waje saina nufi gida. Bayan isowata gida ƴan uwana sunje har Danya danjin miya faru dani amma mahaifinki yaƙi saurarensu, yama nuna bai sansuba baisan daga ina suka fitoba. Asabe kuma taci musu zarafi da musu korar kare. Duk da sunji zafin abinda akai musu sun buƙaci tahowa dake dan a gida na barki ni. amma mahaifinki ya hanasu, yama ɗora musu da cin zarafin dayafi na farko. Wannan shine dalilin yin fishinsu, amma basu haƙura akan wataran zasu amsoki ba. Ansha fama wajen nemamin magani sosai, har takai mai gidannan dake a matsayin yayana yaje Ɗanmusa yaga halin da nake a ciki, shine ya fahimci sihiri ne tattare dani. Shine yasa aka kawoni nan kano wajen wani mutumi mai bada magungunan musulinci. Ya kashe kuɗi bana wasaba wajen ganin hankalina ya dawo tare dani, bayan wani tsahon lokaci aka dace na samu lafiya. Daga nanne ya nema aurena. Duk da banso hakanba aka tirsasani harna amince. Sosai kina maƙale a raina tunda na dawo hayyacina Zinneerah, sai dai bansan miyasaba ko sha'awar nufar hanyar Danya banayi, kai hasalima duk sanda nai yunƙurin son naje sai ciwona ya motsa min. Ƴan uwana kam bansan daliliba kowa ya bar zancen amsoki ko zuwama inda kike. Hakan na damuna a cikin rai, amma inajin kunyar yima wani magana ace na zaƙe da yawa, amma kiyi haƙuri Zinneerah ki yahe mani kinji”.
Kuka sosai Zinneerah keyi fiye da farko. tausayi da ƙaunar mahaifiyarta na sake shigarta cikin jiki da ɓargo. sun daɗe a haka kafin Mama ta koma lallashinta da tambayarta abubuwa game da rayuwarta da Inna Asabe.
Wani takan bata amsa, wani kuma takanyi murmushi ne kawai, hakan yasa Mama sake fahimtar ɗiyar tata tasha wahalar rayuwa kamar yanda tasani Asabe zama tayi fiye da haka. Dan ko ita ba daɗin zama taji da itaba a tsahon shekarun da sukayi tare na zaman kishi.
Yanda Mama bataima Zinneerah zancen ciki ba itama Zinneerah batace komai game da cikinba. Ganin dare yayi Maman tace ta taso taje ta kwanta haka nan.
Yau kam Mama da Zinneerah sunyi barci ne a gado ɗaya, hakan ba ƙaramin farin ciki da jin daɗi ya saka Zinneerah ba, har takaita da shagala dogon tunani akan abinda ke a cikinta itama. Mace ne ko namiji bata saniba. Wanene mahaifinsa yaya aka samar dashi bata saniba, wace amsa zata bashi taba mutane da mahaifiyarta game dashi bata saniba. Ta shafa cikin tana sakin wani murmushi mai ciwo da saka ƙunar zuciya, daga haka barci yay awon gaba da ita mai cike da mafarkin Khalipha.
*WASHE GARI*