Sashe 141
Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
sakeki inason na gwada yanda yake sonkine kawai ba wani abuba, kuma koda ya gama tsarani bawai ban fahimci tsaranin yayba. Sarai na san bazai iya sakinkiba wlhy, nima kuma bama zan yarda yay wannan taɓargazarba. Ki yafemin na ƙara roƙonki......” Da sauri Zinneerah ta shiga girgiza mata kai, “Mammah dan ALLAH ki daina roƙona. Wlhy ni bakimin komaiba sai tarin alkairi kodan zama mahaifiya ga Yayanmu da kikayi. Kuma ni kallon uwa nake miki daman, har abada kuma zan cigaba da kallonki da wannan kimar da darajar. Dan haka ki ɗauka bakimin komaiba. Idanma kinmin na yafe miki wlhy”. Tasowa Mammah tayi ta rungume zinneerah tana saka mata albarka. Kamar yanda zancen nata ya saka kowa dake falon murmushi, duk da ƙarancin shekarunta ALLAH ya bata baiwar shirya lafuza masu taushi ga nagaba da ita duk da kuwa ko ba'a faɗa da gaske an tauye mata haƙinta. Farah da Zakiyya dai babu wanda ya roƙa gafarar Zinneerah, babu kuma wanda yace dasu ƙala akan hakan, kai kowama basu roƙaba sai kuka da sukeyi kawai. Dan haka mai martaba ya umarci AK da mijin Aunty Zakiyya da shima yana a wajen akan su basu saki. Babu wanda yace komai a falon, sai AK ne ya miƙa hannu ya amshi takarda da biro daga hanun Baba Wambai. Haka shima mijin aunty Zakiyya. Gani kawai sukai Zinneerah ta tashi da sauri taje gaban AK ta durƙusa. Biron daya dasa akan takardar ta riƙe da fashe masa da kuka tana girgiza kai. Jajayen idanunsa ya ɗago yana kallonta. “Yayanmu dan ALLAH karka aikata, na roƙeka karka saketa. Kuma koba hakaba ka tausaya mata ba laifinta bane itama tursata akayi”. Tai saurin juyawa ga mai martaba dake mata kallon mamaki hakama sauran jama'ar falon. “Abbah dan girmana ALLAH kayi haƙuri ka janye wannan hukuncin naka koda kuwa sauran zasu tabbata. Gara komi za'a musu ai musu da igiyar aurensu kar'a rabasu da iyalansu na roƙeka Abbah. Dan ALLAH kodan maraicinsu ai musu afuwa, wlhy na tsani naga an saki mace inajin ciwo. Granny, Baffah, Mahma, Babana dan ALLAH kusa baki, Abba dan ALLAH ku bama Abbah haƙuri dasu Yayanmu karsu aikata”. Yanda take kuka kamar ranta zai fita sai duk hankulansu suka tashi. Dan har suƙewa takeyi, ƙoƙarin son fisge pen ɗin AK yayi yana harararta ta sake damƙesa da fashe masa da kuka. “Yayanmu dan ALLAH, kodan ƙyautar little da ALLAH ya azurtaka da shi ka taimaka karkayi, idan ka saketa ALLAH nima bazan zauna da kai ba, zan ɗauke little na tafi inda bazaka sake ganinmuba wlhy”. Kansa dake sara masa ya dafe, da wannan damar ta samu amshe takardar da biron, ta koma gaban Mai martaba ta gurfana tana cigaba da roƙonsa shi da su baba wambai da su waziri. Sosai ta basu tausayi ta kuma sake birge kowa. dan haka hajiya iya tai ɗan murmushi da duban mai martaba ɗin da shi kansa yakejin wani irin ƙaunar Zinneerah na shigarsa. Dan koda ƴaƴansa suka kasance masu laifi bazaiso mutuwar aurensuba ai. Sai dai kuma dolene ya yanke musu hukunci domin yin gargaɗi. “Inaga a amsa kukan Zinneerah dan ALLAH, za'a iyama su Farah hukunci bawai sai an katsa igiyoyin aurensu ba, dan koda abinda duk ya faru aka barsu ya ishesu tunawa da ishara har ƙarshen rayuwa. Ayi haƙuri dan ALLAH”. Ƙasa kawai mai martaba yayi da kansa dan yana ganin girman tsohuwar ainun, yanda yayi ɗin ne ya saka sauran ƴan falonma fara roƙonsa harma dasu AK kansu. Ganin sun masa taron dangi ya sashi jan numfashi da dafa kan Zinneerah ya shiga jera mata addu'oi masu daraja da ake jifan mutum mai daraja dasu. Sai da ya gama ana amsawa da amin sannan yace, “Shikenan zan janye maganar saki, amma kuma dolene sai sunje masarauta sunyi wancan zaman wlhy, sauran hukuncin kuma tsakanina da sune. ALLAH yay miki albarka ke kuma, daga yau kema kin zama cikin jerin ƴaƴana”. Kabbara aka ɗauka a take. Kowa na nuna jin daɗinsa da farin ciki. Daga haka Hajiya iya tai musu nasiha. Hakama baba wambai yayi musu sannan shima maimartaba ya ɗaura tashi, daga ƙarshe aka rufe taro da addu'a saboda lokacin sallar zuhur yayi.