← Book details Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 155

Sashe 38

Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

        “Sister Zinneerah lallai keɗin mai sa'a ce”. Meenal ta faɗa tana tura ƙofar ɗakin da suka iso a ɗan lungun corridor ɗin dake facing jikin ɗakin Hajiya Iya. Kafin Zinneerah ta iya cewa wani abu Jamal ya karɓe da cewa “Mai sa'a kuwa ta gasken gaske. Dan kece ta farko a tarihin gidannan kaf da zaki rayu a wannan ɗakin na Yayanmu bayan shi kaɗai dake rayuwa a cikin kayansa idan yazo ƙasar”.
      Haka kawai gaban Zinneerah ya faɗi batare da tasan daliliba. Har suka shige ɗakin ita tama kasa motsawa balle ɗaga ƙafarta. Ganin hakan yasa Jamal dawowa da baya yaja hannunta suka shige ciki, duk da taso ƙoƙarin ƙwace hannun nata amma yaƙi bata dama sai da suka shigo tsakkiyar ƙaton ɗakin da batamasan yanda zata fasaltashi ba a fahimceta.
           Sakin hannunta da Jamal yayi ya bata damar ɗago idanu tanabin ɗakin da kallo. Yayinda hancinta ke shaƙar mata wani irin mayataccen ƙamshi mai sanya zuciya salama. Wani irin saki gaɓɓanta sukai a lokaci ɗaya, ta zubama su Bahijja daketa yaye fararan ƙyallayen da aka lulluɓe komai na cikin ɗakin dasu saboda gudun ƙura ta hausu.
         Sai da suka gama yaye komai ya bayyana Meenal ke faɗin, “Bara na ɗakko kayan shara mu tayaki ɗan ƙara gyarawan baƙunta. Kuma mufa kibar mana wannan ɗari-ɗarin Madam”.
     Cikin tsokana Jamal yace, “Barta sotake mu kirata baƙauya maybe. Gwarama ki sake damu kafin su Yah Haneef su dawo gidannan gobe idan ALLAH ya kaimu, dan zasu cinyeki da bakine”.
       “Kaji munafiki, saina faɗa musu yasin”. Bahijja dake hararsa ta faɗa.
    Yanda Jamal yay da fuskane ya saka dariya kufcema Zinneerah batare data shiryaba. Hakan yay dai-dai da dawowar Meenal ɗauke da kayan shara ɗakin. “Oh ALLAH, kokefa ƴar uwa. Ni kuwa an taɓa faɗa miki keɗin ƙyaƙyƙyawa ce musamman idan kina dariya?”.
          Kasa bata amsa Zinneerah tayi, sai dariyar tatace ta koma murmushi kawai. Hakan datai ya saka su Jamal kwashewa da dariya a tare. Bahijja tace, “Kinga kinsatama ta haɗiye abinta da wannan bakin naki da bai gani ya ƙyale”.......
       “Wai nikan sharar zakuyi ko damuna da shegen surutu?”. Suka jiyo muryar Hajiya Iya dake tunkaro ɗakin.
       A take kowa ya nutsu suka fara ƙoƙarin sharar. Shigowa tai har yanzu fuskarta a dagule da ɓacin ran ɗazun. Tabi ɗakin da kallo da ƙyau kamar mai nazari. A ƙarshe ta sauke idonta akan Zinneerah dake ƙoƙarin tayasu itama. Haka kawai kuma sai taji ɓacin ran nata ya sassauta. Ta sauke ajiyar zuciya da juyawa ta fice a ɗakin.

      Tsaf suka gyara komai dan an horar dasu aiki tuni. Cikin kanƙanin lokaci ƙyawu da tsaruwar ɗakin ya ƙara bayyana a idon mai kallo. Musamman da suka cire labulayen ɗakin duk suka sake canja wasu fararen tas dan dama fararen suka cire. Kaso mafi yawa dake a ɗakin kalar blue and white ne. Sai wasu colors ɗin ɗai-ɗai da ba'a rasaba. Da yawansu kuma an ɓaɓɓoyesu ma.
      Idanu ta lumshe a hankali tana maijin wani abu mai nauyi dake a ƙirjinta yana narkewa sannu-sannu zuwa cikinta. Nannauyar ajiyar zuciyar da bata shirya fitartaba ta kufce mata a karon farko. Kusan a tare Meenal, Bahijja, Jamal suka dubeta. Sai dai babu wanda ya iya cewa komai a cikinsu, dan sun fahimci Zinneerah bata da sakewa da mutane, gata kuma da alama akwai miskilanci tattare da ita.

★★

       Ƙarfe bakwai da wasu mintuna Alhaji Kabir ya iso katafaren family House ɗin nasu. Bayan samun wajen fakin da direba yayi ya tsaya aka buɗe masa ya fito riƙe da leda a hannunsa wadda kowa yasan mai ita. Dan babu fashi kullum sai ya shigo da irin wannan ledar domin mahaifiyarsa koda iyalansa basu samu hakanba. Sanin baya bama kowa dakon ɗaukarta, shi yasa babu wanda ya tunkaresa domin karɓa. Sai dai sauran kayansa da ɗallami driver ya kwasa zuwa sashensa shi da iyalansa. Shi kuma ya nufi sashen Hajiya Iya kansa tsaye.
        Ɗauke da cikkakkiyar sallama a bakinsa ya shigo falon duk da yasan a irin wannan lokacin Hajiya iya na ƙuryar ɗakinta. dan idan tai sallar magriba bata fitowa sai isha'i. Amma yanada tabbacin baza'a rasa wasu daga cikin ƴaƴansaba da basa rabo da sashen a koda yaushe.
    Ilai kuwa yana shiga da fuskar Zinneerah da Meenal ya fara tozali dan sune ke facing ƙofa. A take falon yay tsit kowa ya ƙara nutsuwa. Sai Meenal ce datai saurin miƙewa ta nufesa domin amsar ledar hannun nasa. “Baffah sannu da zuwa?”.
      “Yauwa uwata kune anan?”.
“Eh Baffah, munzo tarbar Sister Zinneerah ne tun ɗazun”.
     Murmushi Alhaji Kabir yayi yana maida kallonsa ga Zinneerah data risinar da kanta ƙasa tun bayan amsa sallamarsa. Ya ƙaraso cikin falon sosai su Bahijja ma na masa barka da dawowa. A hankali Zinneerah ta zamo ƙasa tana faɗin, “Sannu da zuwa Baffah. Ina wuni”.
     Murmushinsa ya sake faɗaɗawa da faɗin, “Yauwa ɗiyata. Welcome to Shira's family”.
       “Thanks you Baffah”. Ta faɗa a hankali cike dajin kunya.
       Ya cigaba da faɗin, “Yaya kika barmin ƙanwata da ƙannanki da Abbanki?”.
      “Lafiya lau Baffah, sunce suna gaisheka”.
     “Ina amsawa. Alkairin ALLAH yakai garesu. Tashi ki zauna”.
    Babu musu Zinneerah ta miƙe ta koma kusa da Meenal data kaima Hajiya Iya leda ta dawo ta zauna. Shikuma ya wuce bedroom ɗin Hajiya iyan domin gaisheta.

       Tunda yay sallama a yanda ta amsa masa ya saka gabansa faɗuwa. Cikin ƴar ruɗewa ya ƙaraso ƙaton ɗakin nata itama da sassarfa. Gabanta ya zube jikinsa na rawa. “Innata mike faruwa naji muryarki tamkar baƙyajin daɗi?”.
       Ɗago kyawawan idanunta da mafi yawan ƴaƴa da jikokin gidan suka gada a wajenta tai tana kallonsa. A take hawayen da taketa maƙalewa tun ɗazun suka silalo mata tare da murmushi a lokaci guda. Sake ruɗewa Alhaji Kabir yayi idanunsa shima na kawo ruwan hawaye.
     Kanta ta girgiza masa a hankali tana share nata. “Hawayena basu zuba domin kai ba Kabir. Dan kai ɗa ne tamkar da dubu ga kowaɗanne irin iyaye. Nagodema ALLAH domin yayimin ni'imomi masu yawa a rayuwa da har wanda ke a nesa dani bazai ɗauka inada wata damuwa ko jarabawa nima tattare dani ba, kuma har da samunka matsayin ɗa a cikin ni'imomin. Kabir tabbas ɗan uwanka shine jarabawata. Dan ALLAH ka tayani addu'a ALLAH ya bani ikon cinyewa. A lissafin danai yau shekarar Ahmad ɗaya da watanni biyu kenan rabonsa da ƙasarnan. Yanzu ace Kabir har Inno ta rasu Ahmad ya gagara ɗakko iyalansa suzo sumin ta'aziyya. Idanma ita data nisantani dashi bazatazo ba shi bazai iya zuwaba koda shi da Modibbo ne?. Moddibo fa kansa shekararsa uku kenan rabonsa da ƙasarnan. Tunda nai maganar yay auren nan bai sake zuwaba, uwarsa kuma ta hana wannan ƙoɗaɗɗiyar yarinyar zuwa nan ɗin koda ta haihunma. To kosai na mutune zata barsu suzo su raɓi gawata......”
      Ta kasa ƙarasa maganarta saboda kuka daya kufce mata.
      “Innata dan girman ALLAH ki daina kuka. Kiyi haƙuri dan ALLAH, addu'arki da tamu Ahmad yafi buƙata. Kuma insha ALLAH namiki alƙawarin a wannan karon zanbi duk hanyar data dace domin maido ɗan uwana gida. Har ita ɗin da shaiɗancinta dole ta biyosa. inko taƙi wlhy sai dai ta kama gabanta inda ta fito. Amma dan ALLAH kibar kuka Inna”.
      “Kayya Kabir. A baya fa kayi irin wannan namijin ƙoƙarin amma kaga ta sake sabon shiri, harshi Moddibo ɗinma da ada bayabin ra'ayinta yanzu ta sake janyesa. A zatonmu kusancin da Khalipha ya samu dasu zai kawo wani canjin sai gashi ba hakaba”.
       “Insha ALLAH Inna komai zai wuce. Ai duk abinda ya saka kuka wataran zai saka dariya. Duk kuma abinda ya saka dariya wataran sai ya saka kuka. Itama ai gasunan ta haifa indai ƴaƴane ko. kuma Alhmdllh sai ya bata mafi rinjayensu maza. Itama kukan da zatayi akansu sai ya ninka naki sau dubu. Amma dan ALLAH ki daina masa kuka Inna dan shima ba laifinsa bane, anfi ƙarfinsa ne kawai”.
      “Humm ko anfi ƙarfinsa kam da halima. Dan shima kaidin macen yana iske haline. Kai miyasa matan naka basu rabani da kai ba”.
     Kasa cemata komai yayi sai ban haƙuri dai. Sai da yaga hankalinta ya kwanta sanann ya miƙe ya fice domin zuwa gabatar da sallar isha'i tunda ya cinye lokacin zuwa yay wankan anan.
     Bai iske su Zinneerah a falonba yanzu. Da alama sun shige gabatar da sallar suma.

______________★
Chapter 38 · 0% Book details