Sashe 134
Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shaiɗan ɗin daya fahimci yana kai kawo a zukatan matan nasa ya sakashi saka karatun alkur'ani a motar, a ransa yana nema musu sassauci ga ALLAH dan shima yasan zafin kishi tunda yana dashi. Lokaci-lokaci yakan kalli Farah ya duba Zinneerah kuma ta mirror. Ganin yanda duk suka maida fuskoki gefe sai suka bashi dariya amma ya gimtse baiyi a fili ba sai a ransa. Harko suka iso gidan nasu daga Farah har Zinneerah babu wanda yayi ko tari. Bayan ya gaisa da maigadi ya ida shiga cikin gidan ransa fal mamakin ganin motoci da yawa a harabar gidan kamar har yanzu bikin sukeyi basu gamaba danma babbace. Babu wacce ta motsa a cikinsu, dan haka shima sai bai tanka musuba ya buɗe motar ya fita. Ganin haka yasa suma duk suka fito kusan lokaci guda. Kallon juna sukai, sai kuma kowacce ta ɗauke kanta. Farah tazo ta gitta Zinneerah ɗin tanabin bayan AK da yay gaba abinsa ya barsu a wajen, dan harga ALLAH idan ya cigaba da zama yana kallonsu dariya zata iya kufce masa. Dan tsaf ya fahimci itama Zinneerah ɗin A ce a fannin kishi kenan. Koba komai kishin nata a karo na biyu ya tabbatar masa da shima ya samu karɓuwa a gareta, miskilancine kawai ya hana ta bayyana kamar yanda ya buƙata. Sashen Hajiya iya suka nufa kai tsaye, inda sukaci karo da tarin takalma kala-kala ajiye, da alama baƙin da suka tara waɗan nan motocin duk sune anan ɗin. Cikin nutsuwarsa da sallama ɗauke a bakinsa ya shiga, Farah na biye dashi Zinneerah a bayanta. Da sauri Farah ta nema komawa da baya saboda cin karo da fuskar mahaifinta da tai hakimce cikin kujera. AK yay saurin riƙo hannunta yana magana ƙasa-ƙasa. “Malama ki nutsu mana” Ya faɗa yana duban Zinneerah datai musu kallo ɗaya ta ɗauke idonta. Kai Farah ta ɗaga masa idanunta cike da ƙwalla. Ya nuna musu hanya alamar su wuce. Babu musu suka nufi ƙarasawa cikin falon ran Farah fal mamakin zuwan Abban nata babu dogari ko ɗaya, sai ƙannensa biyu Matawalle da waziri, da babban amininsa da kowa ya sansu tare wanda ƙanine a wajensa shima amma kusan tare sukai rayuwarsu, sai dai ba mahaifinsu ɗaya ba. Sai da suka zo kusan tsakkiyar falon Zinneerah ma taci karo da Babanta da Abbah, harma da Maman Sadiq. Ita kanta tsoro ne ya kamata, dan babu shiri ta fara satar kallon mutanen dake a falon, sai ga idonta akan Hajji lanti, da Hajiyar da aka kaita gidanta wadda ta kaita gidan aunty Zakiyya. Ai batama san lokacin da ƙafafunta dake rawa suka goceba ta durƙushe a wajen. Hajiya iya ce tai murmushi da faɗin. “Haba Inno ya da zubewa haka ƙasa. Tashi kizo nan kinji, kema Farah taho”. Miƙewa Zinneerah tai da ƙyar tabi bayan Farah da itama gaba ɗaya ganin Abbasu ya sata tsurewa, dan tsoronsa suke matuƙa saboda bai musu da sauƙi duk da yana tsananin sonsu kuwa. Shi dai AK tuni yakai zaune gaban Uncle Ahmad yana gaida iyayen nasa da surukansa cike da girmamawa. Ganin haka yasa Zinneerah da Farah suma suka shiga miƙa gaisuwa garesu duk da basusan iyayen juna ba, garama ita Zinneerah tasan su Mammah. Bayan an gama gaishe-gaishe duk da su sun gaisa dama a tsakaninsu harma da gabatar da juna tunkan isowar su AK ɗin. Harma mai-martaba mahaifin su Farah ya shigar da ƙorafinsa na rashin sanar masa da auren AK ɗin na biyu. haƙuri Baffah ya bashi tare da masa bayanin a yanda abun ya kasance bada shiriba. Yasha mamaki matuƙa, amma cewar hajiya iya zaman nasu nada nasaba da auren yasa mai-martaban yin shiru bai nema ƙarin bayani akan zancen little ba da yana a falon jikin Abbah, dan tunda ya gansu shi da mmn Sadiq kuma ya maƙale musu cike da murna dan duk duniya su yafi sani fiye da kowa, tunda ko uwarsa batai wahalar da sukai a kansaba bayan ta haifesa. Waziri ne ya gabatar musu da addu'a. Kafin hajiya iya ta fara magana. “Zan fara da sunan ALLAH mai rahama mai jinƙai, dan shine yay sanadi da silar taramu anan ta dalilin wani saka mai sarƙaƙiya da duk ta sarƙe zukatanmu kafin shi wannan zaman. Anan mu dukanmu iyayene kuma kakannine, dan haka ina fatan zamu bada haɗin kai wajen nutsuwa mu fahimci abinda ya taramu, sannan duk wanda al'amarin ya shafa dan ALLAH ina mai roƙonsa dayaji tsoron ALLAH mai zartar ga hukunci a sanda yaso ga wanda yaso ya faɗi gaskiyar abinda ya sani. Mun cire hukuma ne a wannan zancen saboda wasu dalilai. Ba kuma hakan na nufin bazamu iya maida komai garesu bane duk da mun kasance a ƙarƙashin inuwar zumunta ta dalilin aure da sauransu. Wannan yarinya da kuke gani.....” Ta nuna Zinneerah da kanta ke a durƙe tamkar Farah. “Sunanta Zinneerah. Malam Sulaiman gashi nan zaune shine mahaifinta. Wannan kuma Hauwa'u ɗiyar ƙanwata itace mahaifiyarta. Waɗan nan iyaye sun rabu sanadin ƙaddara data saka Zinneerah zama a hannun matar uba bayan barin Hauwa'u gidansu. Inda ita wannan matar uba nata ta raineta cikin gallazawa da son zuciya, a ƙarshe kuma ta miƙata aikatau bada sanin mahaifintaba. Sanadin wannan aikatau ta dawo musu da ciki da suka rasa daga ina ta samosa. Aka turketa da tambayar duniya da barazana tace ita bata aikata komaiba kuma batasan mai ciki ba. An turza iya turzawa tace bata saniba. To a yanzu dai wannan yaro dake jikin Alhaji Abubakar shine ɗan data haifa. Nasan kuma duk wanda ya kallesa zaiyi mamaki da ruɗani akan kamanninsa da Moddibo. Kuma komi za'a faɗa bazai yardaba zai dangantashi da shi a matsayin mahaifinsa kamar yanda muma mukaitayi. Bazan kaiku da nisaba, ga dai wadda ta kai Zinneerah aikatau birni, zamu fara ji daga gareta yaya aka haihu a ragaya. Hajiya Lanti bismillah”. Hajiya iya ta ƙare zancenta da kallon Hajji lanti dake zaune ita da hajiya Haule da kallo ɗaya zakai mata ka tabbatar a gigice take tun zuwansu gidan. Zama hajji lanti ta gyara. Kanta tsaye ta fara magana da iya gaskiyarta. “Ni Lantana nayi alƙawarin faɗar gaskiya kamar yadda Hajiya mama ta buƙata, zanyi hakanne kuma domin na fita har a wajen UBANGIJI na. Wannan sunanta hajiya Haule. a garin katsina take zaune. Na santane dalilin wata ƙawata ƴar kankia da muke zuwa sarin kayan koli kano, itace ta haɗani da ita akan na dinga kai mata yara masu aikatau. Zuminci ya ƙullu a tsakaninmu mai ƙarfi saboda kai mata yara da nakeyi akai-akai. Har ALLAH yasa Zinneerah ta shiga sahunsu a dalilin matar mahaifinta Asabe. Labarin kuɗin da ake samu a dalilin aikatau yasa Asabe ɗaukar Zinni ta bani saboda ta mallake babanta ga shinan bai iya ce mata bai iya musata. Na ɗauka Zinni na kaita garin katsina aikatau tare da wasu yara, washe gari na juyo da nufin komawa gida ƴan doka suka kamani a tsaranci dalilin wata yarinya. Kusan shekarata biyu a gidan kaso, na fito shine naci karo da mummunan labarin Zinni ta dawo da ciki. Wlhy, wlhy, wlhy, wannan shine kawai abinda na sani, amma bansan komai game da cikin Zinni ba”. Kowa ya gamsu da zancenta, dan haka suka maida dubansu ga Hajiya Haule dake sharar zufa. “Nima nayi alƙawarin zan faɗi gaskiyata ni Hajiya Haule, dan faɗan da yafi ƙarfinka masu iya magana sunce ka maidashi wasa. Kamar yanda Hajiya lantana ta faɗa duk anyi haka. Ta kawomin yara ciki harda wannan yarinya Zinneerah saboda dama muna irin wannan huɗɗar. Inda ni kuma na danƙata hannun Hajiya Zakiyya. Amma kafin ita Zinneerah dama akwai wata yarinya da na taɓa bama ita Hajiya Zakiyya ɗin. Wadda ta sanarmin zasuyi mata aikine kuma zata bani maƙudan kuɗaɗe harda iyayen yarinyar. Babu wani ja'inja na yarda duk da kuwa bata fito ta sanarmin da ainahin aikinba, amma jin kuɗi ya sani ruɗewa na amince mata. A tashin farko ta diremin dubu ɗari biyar, hakan yasa a haukace na kai mata wata yarinya da aka kawomin dan sama mata aiki. Sai dai kuma bansan yaya akaiba bayan kusan sati ɗaya ta dawomin da yarinyar akan na sama musu wata ita bazata iya aikin da suke buƙataba. Nasha mamaki saboda yarinyar dana basu babba ce, nasan kowane irin aiki aka sakata zata iya. Dan haka na kasa daurewa na tambayeta duk da inajin tsoro saboda girmanta da kasancewar wadda ta fito daga masarauta. A lokacin bata kulani ba. ta daice naje idan an samu tana jira. Haka na baro gidanta cike da wasiwasi amma bani da mai bani sani sai ALLAH. Anyi haka da kusan wata ɗaya sai ga Hajji Lanti da yara. Da farko dai ƙyawun ita wannan yarinya yasani jin sha'awar kai mata ita, dan nasan masu kuɗinnan dason ƴar aiki mai tsafta da ɗan fasali haka. Cikin amincewar UBANGIJI kuma tana ganinta sai tace tayi, ta kuma ɗauka cikon kuɗina har naira miliyan ɗaya ta bani, duk da dubu ɗari biyar ya kamata ta cikamin. dan munyi da itane akan miliyon ɗayan, nawa dubu ɗari biyu na iyayen yarinya dubu ɗari uku, na yarinya ɗari biyar, amma ban saniba ko jin daɗin samo yarinyar yasata bani ƙarin dubu ɗari biyar, bakuma tamin bayanin ta karanba sai da naje gida na kirata dan duk zatona ko bata kulaba ta bani. Amma sai tace min tana sane. Samun yarinyar dai-dai da ra'ayinsu yasata ƙara mana waɗanan kuɗi mu da iyayen yarinyar. Ta kuma ɗora da faɗamin zasuma yarinyar dashe ne na ciki, idan yakai wata biyu zasu ɗauketa zuwa ƙasar waje har saita haihu musu su sallamota da tagomashin arziƙi, amma wannan sirrine tsakaninmu, ko iyayen yarinyar bataso su sani kawai nace dasu ta tafi turai ne da yarinyar inda take zama da mijinta. Iya abinda ta sanar min kenan ta yanke wayarta. Harga ALLAH na girgiza da zancen sai dai inda aka fi ƙarfi nane bani da damar cewa komai. Kamar yanda ta buƙaci karna bar Nigeria sai aikinsu ya kankama na amince, dan dama kuɗin data bani so nake na koma ƙasar saudia inda dama can nake zaune a da. An yayonine an maidoni rashin kuɗi yasa ban komaba. Gaba ɗaya na mallake kuɗi har na iyayen yarinya dana yarinya da tace, ko Hajji Lanti data kawomin yarinya