← Book details Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 155

Sashe 109

Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

...........Kamar jira ƴan kawo amarya na wucewa Farah ta farka, sai dai a yanayin data farka ɗin yay matuƙar tada hankalin su Mammah, AK daya tuna cewar tana tare da ciki ya cema Dr Mahmud suje asibiti kawai kar a rasa abinda ke cikinta. Mammah ce tai azamar son dakatarwa Mahma ta tsaidata itama ta hanyar faɗin, “Maganar Abdul-Mutallab nakan hanya, hakan shine yafi dacewa kar azo ana dana sani kuma daga baya”.
        Cikin tashin hankali aunty Zakiyya tace, “Mahma kubarta-fa komai zai dai-daita, inaga ya ƙara mata allurar barcin sai mu wuce can gidan da ita dan Abban Ameera ya kirani cewar wanda zai kawo mana key ɗin ya iso yana can yana jiranmu”.
      “Addah abi shawarar Zakiyya ɗin na tabbatar shock ne zata dawo dai-dai idan ta ɗanyi nesa da nan ɗin kamar”.
      Ak dake binsu da kallon mamaki ya dafe kansa dake neman fara masa ciwo, dan shikam dai abubuwan na neman masa yawa gsky. Mahma da wani tunani yazo mata a zuciya tace, “To babu damuwa kai mata allurar kawai sai mu wuce”.
      Kallon AK Dr Mahmud yayi, “Amma ranka ya daɗe karfa allurar tai mata illa, ni bansan ma tana tare da ciki ba da ban mata ita ba, tanada ƙarfi, nayi mamakin ma data farka a yanzu dan allurar mai ƙarfice”.
       Karan farko AK ya saki ɗan murmushi, dan shikam dai zuciyarsa ta fara raya masa wani abu game da yanayin Mammah da Aunty Zakiyya, ya ɗan lumshe idanunsa ya buɗe da gyara tsaiwarsa. Cikin rashin sakewarsa yace, “Kaga yimata ɗin kamar yanda sukace, dan a ganina zamanta a farken yafi allurar zama matsala ga lafiyar tata”.
       Kai kawai Dr Mahmud ya gyaɗa masa, dan shikam dai baimaga wani alamun ciki a jikin Farah ɗin ba. Yana ƙoƙarin haɗa allurar yace, “Amma cikin nata yakai wata nawane?”.
      Shiru Mammah da aunty Zakiyya sukayi, sai Mahma ce tace, “Kamar dai biyar ko”.
     “Biyar fa?”.
Dr Mahmud ya ambata mamaki ƙarara a fuskarsa. Ɗan duban Farah ɗin dake riƙe jikin Mammah tana kuka da wani ɗan fisge-fisge yayi ya ɗauke kansa. Batare da yace komaiba yay mata allurar kawai ransa fal wasiwasi.
     Yana gama mata allurar ko mintuna biyar ba'a ƙullaba barci ya ƙara ɗaukarsa. Kallon AK Mahma tayi da cewa, “Taimaka ka kai mana ita mota Abdul-Mutallab, ku kuma kumuje shima ya samu ya huta”.
       Babu shiri Mammah tace, “Addah ai shine zai kaimu, taya matarsa na wannan halin yaga wani ta hutu?”.
     Murmushi Mahma tayi na takaici, muryarta aɗan hasale tace, “Duk mu da muke tare da ita bai wadatarba sai shi ya kasance a wajen?. Ai ya kamata a tausaya masa ya huta ga kuma yarinya an kawo zai barta ita kaɗai kenan komi?”.
      A take Mammah ta sake tamke fuska matuƙa. Ta kalli AK da yay tamkar bayama jinsu yanata latsa waya. Sai kuma ta maida kan Mahma, “Addah to in hakane muyi kwanciyarmu anan ɗin kawai basai yayi wahalar da kike gudar masanba..”
     “Bazai yuwuba, tunda dai ga gida can da zamu zauna mu kaɗai bamu takura kowa ba, ba'a takuramu ba, can zamuje. Abdul-Mutallab ɗauketa”.
     Yanda Mahma tayi maganar babu wasa a ciki ya sakashi zura wayarsa aljihu ya tako a hankali inda Mammah ke rungume da Farah. Ɗaukarta yay cak ya fita da ita duk da nauyin datai masa saboda yanda jikinta ya saki sosai. Duk yanda Mammah keta kumbure-kumbure Mahma batabi takantaba ta tasasu gaba suka fice suma. Dan ita aunty Zakiyya ma ta ƙagu subar nanɗin dama suje inda takeson amayar da abinda ke a bakinta.
      Aunty Zakiyya ce ta jasu. Suna ficewa daga gidan AK yaɗan lumshe idanunsa da murza goshinsa yana furzar da huci. Sai kuma yay murmushi da girgiza kansa saboda harar da Mammah keta faman antaya masa da gargaɗi da idanu. 
       Juyawa yay zuwa cikin gidan dan shima wani ma zazzaɓi-zazzaɓi ke neman rufesa, sashen Farah ya koma ya kashe komai da maida ƙofar ya rufe, koda ya fito sashensa ya nufa dan yafi buƙatar watsa ruwa a yanzu. 

      ★★★
Chapter 109 · 0% Book details