← Book details Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 155

Sashe 42

Makauniyar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

       A kwana a tashi babu wahala wajen UBANGIJI sai gasu Zinneerah an cinye hutun zangon farko a tsadajjiyar majaranta. Kwanansu biyar dayin hutu Baffah ya haɗa mata shatara ta arziƙi Yaya Haneef ya kaita gida wajen mahaifiyarta. Da dasu Jamal zasu tafi Baffah yace su bari sai ta tashi dawowa sai suje su ɗakkota tunta dai kwanaki goma zatai kacal ai.
     Haneef ya shiga sun gaisa. Sai dai bai jimaba ya fito ya tafi, dan makaranta zaije kuma yace yanada jarabawane. Amma daɗin tarbar daya samu ga Mama yace zai dawo. Bai iske su Sadiq gidaba suna islamiyya. Little kuma yana barci abinsa.
       Kwatanta irin farin cikin da Zinneerah ta tsinci kanta a ciki ɓata lokacine. Amma tsabar kewar Mama da tayi harda rungumeta. Little kuwa data shiga ta samu yana barci yasha kisses, harda hawayenta ganin yanda ya ƙara girma a watanni uku kacal data ɗauka bata ganshiba. Wani irin son yaron da ƙaunarsa na ƙara tasiri a ranta alamun hankali ya fara game jikinta a yanzun fiye da da.
     Lokacin kuwa data shiga gaida Maman Sakina ai baki ta saki tana kallonta tamkar sokuwa. Hakama dasu Luban suka dawo gidan daga makaranta dan suna jarabawa sai da ƴaƴan cikinsu suka hautsina da ganin canjawar Zinneerah ɗin a ƙanƙanin lokaci. Duk da sunsan dama ƙyaƙyƙyawa ce a yanzu kam ƙyan nata yafi fitowa da armashin gani gamai kallonta.
     Itako sosai ta nuna murnar ganinsu cike da sakewa alamar yanzu akwai banbanci da da kenan. Dan babu wannan yawan duƙar dakan da ɗari-ɗari tattare da ita. Miskilancin nedai kam akwaishi saima abinda yay gaba.
     Sai da suka shiga ɗaki sukaita gulma da zaginta wai dan taje gidan masu kuɗi kanta ke rawa tana musu shan ƙamshi. Duk da har yanzu basusan taka maimain a inda takeba. Har uwarsu ba sani taiba duk bin ƙwaƙwƙaafinta. Koda ta tambayi Abba cayay mata dangin mahaifanta ne suka ɗauketa dama basusan ta baro gida baneba zuwa nan shiyyasa. Daga haka kota masa maganar sai yace taje ta tambayi maman sadiq ɗin mana. Daga haka yake kashe bakin son gulma da tsugudidi.
      Maman halima kuwa taji matuƙar daɗi da canjin da Zinneerah ta samu. Koba komai itama ta samu ingantacciyar rayuwa bisa ga zaluncin Asabe ai.
     Dawowar su Sadiq aka sake kafa sabuwar murna da bidiri har takai ga tashin Little. Sosai girman nasa ya sake bama Zinneerah mamaki dan bakace ɗan shekara ɗaya da rabi bane. Da alama akwaishi da garin jiki kam. Yanda yaga su Aliyu nane da ita shima sai ya nane natan yana gwarancinsa dan maganar tasa bawani ganewa sosai akeba garama maman sadiq.
     Ganin ƴan uwanta yay mata daɗi duk da bata mance dasu Jamal ba suma. Kullum ma babu fashi sai tayi waya dasu ta wayar Hajiya Iya ko cikin wayar ƴammatan gidan............✍

*_1~UBAYD MALEEK_*
_By MamuhGee_

*_2~ MAKAUNIYAR QADDARA_*
_By Billyn Abdul_

*_3~ DALAAL_*
_By Miss Xoxo_

*_4~ MABUDIN ZUCIYA_*
_By Hafsat Rano_

*_5~ ALKIBLA_*
_By Safiyya Huguma_

Zaku samu wainnan duka biyar din akan farashin 700,

Guda 5👉700
Guda 4👉500
Guda 3👉450
Guda 2👉400
Guda 1👉300

Zakiyi payment dinku cikin account dinmu dake rubuce na👇👇👇👇
*_0225878823 HAFSAT KABIR UMAR GTBANK_*

Saika tura shedar biyanka ta wannan numbern👇👇
*08085405215*

Idan kuma katin wayane zaka turo da MTN card ta  wannan numbern👇👇👇
*09032345899*

Mungode
*_TM ZAFAFABIYAR🔥_*

*_TYPING📲_*

*_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_*

*Page 19*
_________________________

*Assalamu alaikum warahmatullah, shin kinaba amfani da turaren gashi a matsayinki na mace data amsa sunanta idan amsarki aa toga dama tasamu *awwaba scent* *tazomaku* *da turaren fesawa a gashi natural 100% organic *wanda akahada rose water da essential oils tripped action gashi yy kamshi yay kyali kuma moisturiser at *the same time ba anan abun yatsayaba duk wanda yy order zaahada masa da freshener kala hudu ta daki *ta bandaki ta Mopping da turaren wanka a kan kudi 3,000 kacal indai q cikin watan September dinnna ne daganan kuma zasukoma *normal price dinsu, hakanan turarukqn wuta da humra dinmu anyi masu ragi duk me bukata se nememu a 08034236800 ta what's app kokuma ya ziyarci shafinmu a instagram* @turare_by_awwaba mungode*

______________________

*Page 19*

...........Sosai zaman hutun nan yayama Zinneerah daɗi. Dan koba komai shaƙuwa sosai ta sake shiga tsakaninta da Little, dan yanzun taɗan rage yin kawaici akansa. Hakama ƙannenta koda yaushe suna nane da ita.
      A randa ta cika kwanaki goma sai ga su Jamal babu zato wajen sha ɗaya na safe. Lokacin suna shirin fita gidan sunan ƙanwar Maman Halima. Duk da taso taje gidan sunan sai zuwan nasu ya kauda son fitar, ta shiga murnar ganinsu. Su maman Halima kam dake goye da Little suka tafi bayan sun gaisa dasu Bahijja iyayen rawar kai.
    Sukam babu ruwansu da wata baƙunta. Dan sakin jikinsu sukai tamkar a gidansu. Sai hakan yayma maman sadiq daɗi sosai, dan koba komai hakan girmamawace suka nuna mata. Maman Sakina da yaranta kam sai suka shige ɗaki suna leƙensu ta Window da gulmar a ina su mmn sadiq ɗin suka samo yaran ƴan gayu haka?. Basu da mai basu amsa, dan haka suka cigaba da habaice-habaice da sukar mmn sadiq ɗin harma dasu Meenal da basusan da zamansu a gidanba. Harda cewa kodai a gidansu Zinneerah ke zaune aikin wanke-wanke yanzun?. Sai suka yarda a haka duk da suma sun san faɗane kawai danjin daɗi. Dan Zinneerah batai kama da wadda taje aikatauba.
Su Jamal ma sun sami rabon nasu zagin sosai, dan koda sukazo suka iske Maman sakina a tsakar gida dasu Luba ko kallo basu ishesuba. Sai mmn halima data tarbesu da fara'a suka gaida cike da girmamawa. Hakanne ya sake baƙanta ran mmn sakina taja ƴaƴanta suka shige ɗaki.
      Wainar filawa Zinneerah tai musu kamar yanda sukace suna buƙata, sai da sukaci suka ƙoshi Abba ya dawo gidan bayan la'asar suka gaisa sanan driver yazo ya kwashesu harda Zinneerah da taso yin sallama da Little da sauran yaran, dan sanda maman halima ta wucene da shi yana barci, ko ganinsu su Bahijja ma bayi sukaiba. To da yakema ba sanin labarinsa sukaiba basu kawo komai a ransuba sun zatama ɗan mmn halima ɗinne duk da dai basuga fuskarsaba.

       Sosai Hajiya iya dasu Yah Moos'ab suka nuna farin cikinsu na dawowarta. Tare da faɗi mata sunyi kewarta kowa a gidan. Cikin ƴar dariyarta tace, “Nima nayi kewarku ai, wani lokacin har mafarkinku nakeyi”.
       Sunji daɗin maganarta har cikin ransu, dan itama suna mata kallone na ɗaya daga cikinsu bawai wadda tazo cin arziƙi gidansu ba. Moos'ab da bai cika yawan maganaba shi dama yaɗan ɗage gira yana gyara kishingiɗar da yay a kujera da faɗin, “Ni ba yarda nai dakeba fa yarinya”.
     A hankali Zinneerah ta ɗago manyan idanunta farare tas ta zuba a kansa, irin kallon da yake matane ya sakata saurin maida nata ƙasa tsigar jikinta na tashi, ba yaune karan farko da Yah Moos'ab ɗin ke mata irin wannan kallonba, shiyyasa a mafi yawan lokuta bata wani cika sakewa da shiba sosai. Kasa bashi amsa tayi, hakan yasa Saifudden kwashewa da dariya yana faɗin, “Wataran dai zata fashe”.
       “Minene zai fashe?”. Cewar Haneef dake a kusa dashi yana latsa waya.
     Saifudden yace, “No jaridar mai tsadace, duk maiso ya tanaji kuɗi akwai ranar da zan saida muku”.
     Abidah ce tai dariya tanama Saifudden alamar jinjina. “Ai Yah Saif nima na daɗe da harbo jirgin, kasanfa idanuna sun iya gane-gane nima, duk randa suka tashi saya ka nemoni zan ƙara da nawa rahoton”.
     Tsam Zinneerah ta miƙe zata bar wajen, dan haka kawai ta tsargu da zancen nasu, tanaji a ranta kenan suma duk suna sane da Yah Moos'ab ɗin komi?.
      “A'a, auta ina zuwa?”. Cewar Safiyya da sauri.
      “Im ihm Aunty Safiyya zanje cikine nayi wanka”.
     Da sauri Ni'ima tace, “Wankafa? Ba shigowata Granny ke faɗin kina ciki kina wankaba Auta (Mafi yawan lokaci haka suke kiranta auta).
      Kasa magana tai, hakan yasa Saifudden kwashewa da dariya yana raira waƙa. Duka Moos'ab ya kai masa. Yay saurin wuntsilowa a kujerar yana cigaba da dariyarsa. Da sauri Zinneerah tabar wajen ranta fal tsoro. Ɗakin da har yanzu ta kasa sakin jiki da zamansa ta shige tare da faɗawa saman gadon a karo na farko. Tai ɗan murmushi dajan filo ta cusa kanta a ciki. A ranta kuwa rayawa take itakam karsu Yah Saifudden su jawo mata rigima. Ina ita ina soyayya da waninsu bayanma duk kallon yayu take musu itakam. Wannan zance ai da girma yake idan har yazo a yanda zuciyarta ke hankaltar da ita game da take-taken Yah Moos'ab ɗin.
      Haka ta kasance cikin dogon tunanin da har barci mai nauyi yay awon gaba da ita batare data saniba. Harsuka gama hiratsu kowa ya miƙe zuwa makwancinsa basu sake ganintaba. Hajiya Iya kam dama ta kwanta tuni saboda maganin mura da tasha, kuma dama ita ba'a doguwar hira da ita, tanada saurin barci. Wani lokacinma sai jikokin nata suzo su ƙaraci shirmensu a sashen bata saniba. Dan kullum nanne wajen hiratsu sai dai idan yayansu na gari kam babu sakewa, duk da suna zuwa a hakan.

        Sosai Zinneerah taji daɗi barci akan wannan gado da yau ya zame mata na farko, dan ko fitsari bata farka yiba yau saboda daɗin barci. Sai kiran sallar farko na asuba ta buɗe idanunta da ƙyar tana karanto ɗaya daga cikin addu'ar tashi daga barci.
Chapter 42 · 0% Book details